Ticker

6/recent/ticker-posts

Wadanne nau'in abinci ne ake yin zakkar fidda-kai da su?

 𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Asssalamu alaikum malam. Waɗanne nau'in abunci ne ake yin zakkar fidda-kai da su?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Zakkar fidda-kai ana fitar da itane daka dukkan wani nau'in abuncin damutane suke ci, kamar alkama da masara da shinkafa, da gero da dangoginsu, danama da wake da makaroni, dama kantansu, hakika manzan Allah sallallahu alaihi wasallam y afarlanta ta sa'i ɗaya na abunci, sahabbai yardar Allah takara tabbata agaresu sun kasance suna fitar da ita daka abuncin dasuka saba suna ci agaruruwansu.

Imamul bukhari yaruwaito hadisi (1510) da muslim(985) Daka Abu sa'idul kudri yardar Allah takara tabbata agareahi ya ce: (Munkasance muna fitar da zakkar fidda-kai ranar idin karamar sallah azamanin Annabi sa'i ɗaya na abunci, Abu sa'idul khudri ya ce: abuncinmu ya kasance shi ne azzabib da accah, da dabino, da Al'aƙdi, Nonone ake alkintashi yakoma gyararre ana hadashi da dabino aci.

Malamai dayawa sun fassara abunci a cikin hadisin dacewa: (Alkama ake nufi) wasu sukace: Abunda ake nufi da abunci shi ne wanda mutanan gari suka saba shi ne abuncinsu, kowanne irine, alkamace ko masara ko makamantansu, Majmu'u fatawa bin baaz (14/200).

Shaikul islam ibnu taimiyyah a cikin majmu'u fatawa (68/25) ya ce: Idan mutanan gari sun kasance sun saba da cin ɗaya daka cikin jerin wadancan nau'ikan abunci yahalatta sufitar da zakkar fidda-kai a cikinsu babu kokwanto a kan wannan, shi ne maganar mafiya rinjayen malamai.

Ibnul ƙayyem a cikin littafinsa I'I LAMUL MUWAƘƘI'EEN (3/12) ya ce: Mutanan garin da su abuncinsu ba acca bane ko alkama ko dabino kamar waɗanda abuncin garinsu shi ne shinkafa dasuransu zasu fitar da sa'i ɗaya daka nau'in abuncin, kamar wanda abuncinsu shi ne nama ko kifi, ko nono, zasu fitar daka cikinsu kowanne irin nau'ine na abunci indai shi ne abuncinsu dasuka saba dashi zasu fitar daka cikinsa, wannan shi ne maganar jamhur din malamai kuma shi ne dai-dai wanda baza a fadi sabanin hakaba,.

WALLAHU A'ALAM.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta wannan Links...

NAU'IN ABINCIN DA AKE YIN ZAKKAR FIDDA-KAI DA NAU'IN MUTANEN DA ZA A BA WA

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Asssalamu alaikum Malam. Wadanne Nau'in Abuncine ake Yin Zakkar Fidda-Kai Dasu? Kuma Wadanne Nau'in Mutanen ne Daza'a Bawa zakkar fidda kai ?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam Warahmatullahi Wabarkatuhu.

Zakkar fidda-kai ana fitar da itane daka dukkan wani nau'in abuncin damutane suke ci, kamar alkama da masara da shinkafa, da gero da dangoginsu, danama da wake da makaroni, damakantansu, hakika manzan Allah sallallahu alaihi wasallam ya afarlanta ta sa'i ɗaya na abunci, sahabbai yardar Allah takara tabbata agaresu sun kasance suna fitar da ita daka abuncin dasuka saba suna ci agaruruwansu.

Imamul bukhari yaruwaito hadisi (1510) da muslim( 985) Daka Abu sa'idul kudri yardar Allah takara tabbata agareahi yace: ( Munkasance muna fitar da zakkar fidda-kai ranar idin karamar sallah azamanin Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam) sa'i ɗaya na abunci, Abu sa'idul khudri yace: abuncinmu yakasance shine azzabib da accah, da dabino, da Al'aqdi, Nonone ake alkintashi yakoma gyararre ana hadashi da dabino aci.

Malamai dayawa sun fassara abunci acikin hadisin dacewa: ( Alkama ake nufi) wasu sukace: Abunda ake nufi da abunci shine wanda mutanan gari suka saba shine abuncinsu, kowanne irine, alkamace ko masara ko makamantansu, Majmu'u fatawa bin baaz ( 14/200).

Shaikul islam ibnu taimiyyah acikin majmu'u fatawa ( 68/25) yace: Idan mutanan gari sun kasance sun saba da cin ɗaya daka cikin jerin wadancan nau'ikan abunci yahalatta sufitar da zakkar fidda-kai acikinsu babu kokwanto akan wannan, shine maganar mafiya rinjayen malamai.

Ibnul qayyem acikin littafinsa I'I LAMUL MUWAQQI'EEN ( 3/12) yace: Mutanan garin dasu abuncinsu ba acca bane ko alkama ko dabino kamar wadanda abuncin garinsu shine shinkafa dasuransu zasu fitar da sa'i ɗaya daka nau'in abuncin, kamar wanda abuncinsu shine nama ko kifi, ko nono, zasu fitar daka cikinsu kowanne irin nau'ine na abunci indai shine abuncinsu dasuka saba dashi zasu fitar daka cikinsa, wannan shine maganar jamhur ɗin malamai kuma shine dai-dai wanda baza'a faɗi saɓani hakaba.

NAU'IN MUTANEN DAZA'A BAWA ZAKKAR FIDDA KAI

Wannan mas'ala akwai saɓanin malamai akanta, shafi'iyyah suntafi akan waɗanda ake bawa zakkar fidda kai sune jinsin mutane takwas da Allah yalissafa waɗanda za'a bawa zakkar kuɗi ko dukiya.

Malikiyya suntafi akan waɗanda za'a bawa zakkar fidda-kai sune talakawa da miskinai, kuma shine ra'ayin da shaikul islam ibnu taimiyyaj da dalibinsa ibnul qayyeem suka zaɓa, cikin malaman wannan zamanin kuma shaik bin baaz ya zaɓi wannan maganar.

yazo acikin hashiyatul dasuqi ( 1/508) " Ana bayar da zakkar fidda kai ga ɗa musulmi talaka wanda ba dangin Annabi ba,  banda mai aikin zakkar ko wanda akesan ya musulunta ko wanda yake matafiya ko bako, kawai ana bawa talaka ne.

Ibnu taimiyyah yace: " wannan zancen shine yafi karfi wajan dalili, majmu'u fatawa ( 25/71).

Ibnul qayyeem acikin zadul ma'ad ( 2/23) yace: yana daka cikin shiriyar manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam keɓance talakawa da ita, bai kasance yana rabata ga jinsi takwas danki danki ba, kuma bai umarni da hakaba, babu wani cikin sahabbai daya aikata hakan, ko waɗanda suka biyo bayansu, daya daka cikin zantukan awajanmu, shine ta keɓanta ne kaɗai ga miskinai datalakawa, bai halatta rabata tsakanin jinsi takwas ba.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IƙsWWSpUkwk6b8hWJ6vXOO

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments