Ticker

6/recent/ticker-posts

Tun da na haihu ban yi jini ba sai jiya, kuma jinin ya zo nau'i na daban, shin zan yi azumi?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Malam ina da tambaya ni ce tun bayan dana haihu na gama jini ban kuma yin jini ba Sai jiya kuma ban gan shi kamar yanda na saba gani ba, to abin tambayar shi ne zan iya daukan azumi ko kuwa? Na gode.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Eh ya wajaba ki dauki azumi Domin kamar yadda tambayarki ta nuna ba jinin haila kika gani ba Shi kuma azumi da sallah ba'a dena su har sai idan asalin jinin hailar ne yazo sabida hukuncin dakatar da ibada yana ratayuwa ne da ganin jinin haila ba kowane jinine idan mace tagan shi yake zama na haila ba musamman Idan ba a cikin kwanakin hailar yazo ba, Sabida haka idan mace taga jini kuma ya canza daga asalin jinin hailarta to matukar dai ba a tsakiyar hailarta ko ƙarshen hailar tagan shi ba, Bazata daukeshi a matsayin haila ba.

WALLAHU A'ALAM

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments