Ticker

6/recent/ticker-posts

Cin naman mutane (yi da mutum) yana daga abubuwan da ke bata azumin mutane?

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Shin. Cin naman mutane (yi da mutum) yana daga abubuwan da ke ɓata azumin mutane?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Yi da mutum, ba ya cikin abubuwan da su ke ɓata azumi, Shi ne kuma: ambaton mutum da abinda ya ke ƙi, saboda fadinsa Mabuwayi da daukaka:

"Kuma kada sashenku ya yi gibar sashe"

[Suratul Hujurat: 12].

Haka kuma annamimanci da zagi da karya dukkansu basa cikin abubuwan da su ke ɓata azumi, Sai dai manya manyan saɓo ne wanda ya zama wajibi a kiyaye su, mai azumi da wanda ba mai azumi; su nisance su ba, kuma lallai suna kawo gibi ga azumi, kuma su rage masa ladansa; wannan kuma saboda fadin Manzon Allah (SAW):

"Duk wanda bai bar zancen karya da aiki da shi, da wauta ba, to Allah bashi da buƙatar ya bar cin abincinsa, da abin shansa" Bukhariy ya rawaito shi a sahihinsa.

Da kuma saboda fadinsa:

"Azumi garkuwa ne, idan ranar azumin ɗayanku ya zo, to kada ya yi batsa balle jima'i, kada kuma ya yi shewa, idan wani ya zage shi, ko ya nemi fada da shi, to ya ce: Ni mai azumi ne" Bukhariy da Muslim suka ruwaito. Kuma Hadisai kan wannan mas'ala suna da yawa.

MAJMU'U FATAWA WA MAKAALAAT MUTANAWWI'AH, (15/ 320).

ALLAH NE MAFI SANI.

Yi da mutum, baya cikin abubuwan da su ke ɓata azumi, Shi ne kuma: ambaton mutum da abinda ya ke qi, saboda faɗinsa Mabuwayi da ɗaukaka:

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اجْتَنِبُوا كَثِيرًا مِّنَ الظَّنِّ إِنَّ بَعْضَ الظَّنِّ إِثْمٌ ۖ وَلَا تَجَسَّسُوا وَلَا يَغْتَب بَّعْضُكُم بَعْضًا ۚ أَيُحِبُّ أَحَدُكُمْ أَن يَأْكُلَ لَحْمَ أَخِيهِ مَيْتًا فَكَرِهْتُمُوهُ ۚ وَاتَّقُوا اللَّهَ ۚ إِنَّ اللَّهَ تَوَّابٌ رَّحِيمٌ

Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku nĩsanci abu mai yãwa na zato. Lalle sãshen zato laifi ne. Kuma kada ku yi rahõto, kuma kada sãshenku yã yi gulmar sãshe. Shin, ɗayanku nã son yã ci naman ɗan'uwansa yanã matacce? To, kun ƙĩ shi (cin nãman). Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle Allah Mai karɓar tũba ne, Mai jin ƙai. (suratul Hujurat Aya ta 12)

Haka kuma annamimanci da zagi da karya dukkansu basa cikin abubuwan da su ke ɓata azumi, Sai dai manya-manyan saɓo ne wanda ya zama wajibi a kiyaye su, mai azumi da wanda ba mai azumi; su nisance su ba, kuma lallai suna kawo gibi ga azumi, kuma su rage masa ladansa; wannan kuma saboda fadin Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam): "Duk wanda bai bar zancen karya da aiki da shi, da wauta ba, to Allah bashi da buqatar ya bar cin abincinsa, da abin shansa" Bukhariy ya rawaito shi a sahihinsa.

Da kuma saboda faɗinsa: "Azumi garkuwa ne, idan ranar azumin ɗayanku ya zo, to kada ya yi batsa balle jima'i, kada kuma ya yi shewa, idan wani ya zage shi, ko ya nemi faɗa da shi, to ya ce: Ni mai azumi ne" Bukhariy da Muslim suka ruwaito. Kuma Hadisai kan wannan mas'ala suna da yawa.

MAJMU'U FATAWA WA MAKAALAAT MUTANAWWI'AH, (15/ 320).

ALLAH NE MAFI SANI.

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments