Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin gaskiya ne a cikin daren lailatul ƙadari ana ganin komai ya koma yanayin sujada, kamar bishiyoyi da gidaje har ma mutum ya rinka hango ka'aba daga duk inda yake ?

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Shin gaskiya ne a cikin daren lailatul ƙadari ana ganin komai ya koma yanayin sujada, kamar bishiyoyi da gidaje har ma mutum ya rinka hango ka'aba daga duk inda yake ???

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wannan bai tabbata ba daga manzon Allah ko magabata na kwarai. Ijtihadin wasu mutane ne ba tareda wani dalili na sharia ba. Amma ya tabbata wasu daga cikin sahabbai "An nuna masu a mafarki cewar daren lailatul Ƙadari yana cikin bakwai na karshe" Wannan hadisin yanuna cewar an nuna masu ranar ne amma ba wani abu suka gani ba. Amma ana ganin alamomin daren lailatul Ƙadari kamar yadda Annabi ya bada labari cewa:"Ranar daren lailatul Ƙadari takan fita ba ta yin zafi. Muslim (Sharhin khadi iyad, 1165). Kuma Manzon Allah ya ce: "A cikinku wa zai tuna daren da wata ya fito kamar rabin akushi? Ana fadin daren lailatul kadari sai Annabi yafadi haka.

WALLAHU A'ALAM

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/CƘ9TMXMrWDx1y7sYye2znU

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments