Ticker

6/recent/ticker-posts

Idan Na Riski Daren Lailatul Qadri Wacce Addu'a Zan Yi?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Malam. tambaya na anan shi ne in har Allah ya sa mutum ya dace da daren lai-latul ƙadar wani irin addu'a ya kamata ya yi kuma shi addu'an so nawa ake yi? Kuma shi lai-latul ƙadar ɗin tana da wasu alamomi ne na ganinta?

 Na gode

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Dangane da amsar tambayarka ta farko, akwai hadisi wanda Imamu Muslim da Imam Ahmad da Tirmidhiy da Abu Dawud suka ruwaito daga Sayyiduna Ubayyu bn Ka'ab (rta) cewa shi ya ce : "Ina rantsuwa da Allah wanda babu abin bautawa da gaskiya sai Shi, Hakika shi wannan daren a cikin Ramadana ne. Kuma ina rantsuwa da Allah ni nasan daren da take. Ita ce daren nan wacce Manzon Allah ya umurcemu da Tsaiwarta. Ita ce daren Ashirin da bakwai.

Alamominta kuma, Rana za ta ɓullo a safiyar ranar, fara sol babu tartsatsi gareta.

2. tambayarka ta biyu kuma : Imam Abu Dawud da Tirmidhiy da Ibnu Maajah sun ruwaito daga Nana A'ishah (ra) tace : "Nace "Ya Ma'aikin Allah, shin idan nasan wacce ce daren Lailatul Ƙadari, Mai zan ce a cikinta?". Sai ya ce kice:

اللّٰهُمَّ إِنَّكَ عَفُوٌّ تُحِبُّ الْعَفْوَ فَاعْفُ عَنِّيْ

"ALLAHUMMA INNAKA 'AFUWWUN TUHIBBUL 'AFWA FA'AFU 'ANNEE"

 (Ya Allah kai Mai Afuwa ne, kuma kana son yin afuwa. To kayi afuwa gareni)

Kaima ita wannan addu'ar za ka rika yi kamar yadda Annabi ya koyar.

WALLAHU A'ALAM.

***

IDAN NA RISKI DAREN LAILATUL KADRI (ƘADIR) WACCE ADDU'A YA KAMATA NAYI?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Malam. tambaya na a nan shi ne in har Allah ya sa mutum ya dace da daren lai-latul qadar wani irin addu'a ya kamata ya yi kuma shi addu'an so nawa ake yi? Kuma shi lai-latul qadar ɗin tana da wasu alamomi ne na ganinta? Nagode

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Dangane da amsar tambayarka ta farko, akwai hadisi wanda Imamu Muslim da Imam Ahmad da Tirmidhiy da Abu Dawud suka ruwaito daga Sayyiduna Ubayyu bn Ka'ab (rta) cewa shi ya ce : "Ina rantsuwa da Allah wanda babu abin bautawa da gaskiya sai Shi, Hakika shi wannan daren acikin Ramadana ne. Kuma ina rantsuwa da Allah ni na san daren da take. Ita ce daren nan wacce Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya umurcemu da Tsaiwarta. Ita ce daren Ashirin da bakwai.

Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) Ya ce: “Ku kintaci daren Lailatul Qadri a cikin marar goman qarshe ta Ramadan” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi]. waɗanda su ne daren 21, 23, 25, 27, 29.

Wasu malamai sun yi bayanin cewa daren Lailatul Qadri yana yawo a tsakanin waɗannan darare (Wata shekarar wannan, wata shekarar wancan) saboda a yi aiki da dalilan da suka zo a kan haka baki ɗaya.

An karbo daga Jabir ɗan Abdullahi – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Haqiqa ni an nuna min daren Lailatul Qadri, sannan an mantar da ni shi, yana goman qarshe na Ramadan, dare ne babu sanyi ko zafi a cikinsa, kuma mai haske ne, ba zafi ba sanyi (mai cutarwa acikinsa)” [Ibn Khuzaima ne ya rawaito shi].

Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya kasance yana ƙara ɗamara a goman karshe, yana raya dukkan dararrakinsa, kuma yana tada iyalansa.

Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ya ce, “Wanda ya yi tsayuwa daren Lailatul Qadri yana mai imani da neman lada, an gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

Imam Abu Dawud da Tirmidhiy da Ibnu Maajah sun ruwaito daga Nana A'ishah (ra) tace : "Nace "Ya Ma'aikin Allah, shin idan na san wacce ce daren Lailatul Qadari, Mai zan ce acikinta?". Sai ya ce kice:

اللّٰهُمَّ إِنَّكَ عَفُوٌّ تُحِبُّ الْعَفْوَ فَاعْفُ عَنِّيْ

Ya Allah kai Mai Afuwa ne, kuma kana son yin afuwa. To kayi afuwa gareni.

Kaima ita wannan addu'ar zaka rika yi kamar yadda Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya koyar.

Allah ya datar damu da dukkanin alkhairin da ke cikin wannan dare mai albarka Allah ya bamu ikon lizimtar ta.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Fc3hX6HoDt65aKhhKOiDpX

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments