𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamualaikum, tambaya ta, matanane ta haifu lokacin azumi, kamin azumi ya zagayo kuma ta dau Wani ciki bata Samu ta biya Wanda ta sha ba, domin kuwa tana shayarwa kuma ga ciki, ta fara ramawa a wannan halin, ranar farko tana shan Ruwa Sai asibiti dama tana da ulser amma ba Wanda zai Hana azumi ba, ganin haka nikuma Na tsorata Sai Na hanata azumin. Mallam tambaya Na shi ne ina da laifi ne na hanata azumi? za ta Rama azuminne koko shayarwa koko dukka biyu? In shayarwa ne za ta iya Bawa mutum ɗaya dukkan mudunabi a lokaci ɗaya koko Ko Wani rana za a Bawa mutum ɗaya.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaykumussalam
1. Ba kada laifi domin shari'a ta yi rangwame ga wanda ba
yada lafiya da ya aje azumi sai ya rama a wasu lokuttan na daban bayan ya samu
sauki, kamar yadda ya zo cikin fadar Allah cikin suratul bakara 184.
2. Idan har za ta iya ramawa to ta rama duk abin da ta
sha, idan kuma bazata iya ramawa ba bisa bincike na likitoci masana addini toh
za ta ciyar ne kawai babu ramako a kan ta, malamai na hujja da fadar Allah
suratul bakara 184.
3. Za ta ciyar da miskini ɗaya kowane yini,
idan kuma ta haɗa na adadin da ake binta ta baiwa miskini ɗaya duka shi ma
babu laifi, kamar yadda Sheihul islam ibn taymiyya ya bada fatawa cikin
littafin sa majmoo'ul fatawa 15/203.
WALLAHU A'ALAMlam.
✍️ Malam Nuruddeen Muhammad Mujaheed
Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare
Da Fadakarwa a Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/Bvk6LLvY9evDZHXFMZCzeU
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.