Assalamu Alaikum Warahmatulah wabarkatuh.
Ya ku Yan'uwa masu Albarka Maza da Mata... Wannan Group mai albarka yana muku fatan alheri, da fatan samun rahamar Allah da dacewa baki ɗayanmu.
BAYAN HAKA:
Da wannan ne muke sanar da dukkanin members ɗin Group namu
sabon tsari da salo na Fadakarwa da muka samar, wanda canji da gyare-gyare da
ake samu daga WhatsApp da kuma software developers yake bamu wannan damar a ko
yaushe.
Alhamdulillahi, kullum muna samun cigaba tare da samun
hanyoyi masu sauƙi wajen isar da saƙon Allah da
Manzonsa, ﷺ wanda wannan yassarewa ce daga Allah Maɗaukaki Sarki gare
mu baki ɗaya.
Wannan Group na TAMBAYA DA AMSA zamu haɗe groups ɗin waje ɗaya, daga Group 1
zuwa 20 ta hanyar kwashe members ɗin sauran Groups don su haɗu a wannan
zaurukan da muka kayyade don samarwa kanmu sauƙi baki ɗaya.
WHATSAPP COMMUNITY GROUPS
Dandali ne da aka kirkire shi domin karantarwa da
tunatarwa ga abinda ya shafi Addinin Musulumci bisa karantarwar Alkur'ani da
Sunnah bisa fahimtar magabata na kwarai.
wannan wani tsari ne da WhatsApp suka fito dashi,
hikimarsa da amfaninsa wajen mu sun haɗa da:-
👉 Bawa members damar ajiye tambayar da suke son yi, domin
shi wannan community Groups ɗin zai fi bawa admins sauƙi da kuma
saurin ganin saƙonnin members, a maimakon tsarin da ake
yi a baya, wanda wata tambayar sai ta fi watanni ba'a duba ba, ko an duba an
manta.
👉 Tsarin zai bawa members damar tattaunawa kai tsaye da
kuma samun sanarwa da saƙonni masu muhimmanci akan lokaci,
Wannan Tsarin yana da amfani masu yawan gaske.
Community Group Kebantacce ne ga Members ko Participants,
Bazasu Iya Ganin Sauran Members Ko Ganin Lambobinsu ba. Admins Kaɗai ake Iya Gani Da
Adadin Mutanen Da Suke Ciki.
TSARIN POLL
Shi ma wannan wani tsari ne da WhatsApp ya kirkira kamar
dai na TELEGRAM, wanda in shaa Allah wannan Group namu akai akai zai dinga
tsara wasu yan taƙaitattun tambayoyi ga members domin mu
dinga tunatar da junanmu akai akai akan darussan da ake yi a groups ɗin, ko tambayoyi
game da tsarin mu in shaa Allah.
Muna roko da bada hakuri akan ayi hakuri a cigaba da
kasancewa da mu ko yaushe. Muna rokon Allah ya cigaba da taimakon mu, tare da
sauƙaƙe mana hanyoyinsa wajen neman ilmi da
yaɗa shi. Allah Yasa
mu Amfana da Ababen da muke Rubutawa da kuma karantawa. Allah Yasa fadakarwan
nan ta Amfani Al'ummah ga baki ɗaya.
Ga masu buƙatar su Kasance damu acikin Wannan
Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa, zasu iya bi ta links ɗin mu...
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
+2347042085123
+2348173457713
✍ SANARWA DAGA
ADMIN:
𝐌𝐚𝐥. 𝐊𝐡𝐚𝐦𝐢𝐬 𝐘𝐮𝐬𝐮𝐟
+2347042085123
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.