Ticker

6/recent/ticker-posts

Itikafi 01 - Hukunci Da Falalar Ittakafi

Ma’anar li’itikafi shi ne lazimtar Masallaci da zama a cikinsa da niyyar neman kusanci da ALLAH TA'ALAH.

HUKUNCINSA

Shi li’itikafi sunna ce mai ƙarfi, kuma a goman ƙarshe na watan Ramadan ake yin sa, Amma yinsa a wani watan mustahabbi ne.

Manzon ALLAH {s.a.w} ya kasance yana yin li’itikafi a kowane watan Ramadan kwana goma, amma da shekarar da zaiyi wafati tazo, sai yayi kwana ashirin.

[Bukhari ne ya rawaito]

FALALARSA

Shi li’itikafi ibada ne mai girma wanda yake tsarkake zuciya ga barin shagala da duniya kuma yana sa mutum ya dukufa wajen neman lada da kyakkyawar makoma.

SHIGARSA

Ana son shiga li’itikafi kafin faɗuwar ranar da za'a fara.

AYYUKANSA

Ana son mai li’itikafi ya shagala da yin ibada kamar nafilfili, karatun Alƙurani, tasbihi da hailala, zikiri, istigfari, salatin Annabi {s.a.w} da sauran ayyukan bin ALLAH.

 Amma banda karatun jarida, ko karatun wani littafi wanda ba Alƙur'ani ba, domin malamai sunce ko littafin hadisi bazaka karanta ba, a gurin sai dai idan wani malami ne yake darasi kama cikin masallacin.

 Sannan dole a nisanci amfani da wayar hannu inba dole ba, kuma ba'a fita ko ima sai iya harabar masallaci.

ALLAH shi ne mafi sani.

ALLAH ka bamu ikon aiki da abinda muka karanta.

ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.

Duk mai neman ƙarin bayani ya tuntuɓemu ta private.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

1 Comments

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.