𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Wasu cikin mutane suna raya daren lailatul ƙadr (ranakun da a ke sa ran lailatul ƙadr) da salloli da ibadu, amman ba sa raya wasu
dararrakin da ba wannan ba a ramadan din. shin hakan ya dace da daidai?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
A'a bai dace ba, domin daren lailatul ƙadr na caccanzawa, ta yiwu ya kasance a daren 27, ta yiwu
kuma ya kasance a wani daren da ba wannan ba, kamar yanda hadisai da dama su
kayi nuni a kan hakan. Sannan shi tsayuwan dare ba ya halatta ga mutum ya keɓanceshi da daren
da ya ke fatan ya kasance lailatul ƙadr, dagewa da tsayuwa a duka
dararrakin ƙarshen duk yana cikin koyarwan Annabi tsira da aminci su
tabbata agareshi.
Abin da yake kamata ga Mumini mai ƙwazo shi ne
ya dage ya raya duka goman saboda kar lada ya kubuce masa.
Shaykh Muh'd Saleh Al'uthaimeen
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/DSdbBS8RZVoIKYG5exOuZE
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
Post your comment or ask a question.