Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Wanda Ya Yi Mafarki Da Rana Alhali Yana Azumi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Na kasance mai azumi sai na yi barci a masallaci, dana tashi sai na samu cewa na yi mafarki, Shin mafarkin yana da tasiri ga azumina? Tare da cewa banyi wanka ba sai kawai na yi sallah ba tare da na yi wankan ba.

Wata rana kuma dutse ya rotse min kai sai jini ya kwarara, Shin azumina ya lalace saboda fitan jini?

Dangane da amai kuma shin yana bata azumi ko a'a? Ina fatan a amfanar da ni?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Lallai mafarki baya lalata azumi, kuma baya yi masa tasiri; saboda kasancewarsa yana fita ne ba a cikin zabin mutum ba, Sai dai kuma wajibi ne akansa ya yi wankan janaba idan har maniyyi ya fita daga gare shi, saboda Annabi (صلى الله عليه وسلم) yayin da aka tambaye shi kan haka, sai ya amsa da cewa mai mafarki zai yi wanka ne; idan har ya ga ruwa (maniyyi).

Sallar da ka aikata ta kuma ba tare da ka yi wanka ba wannan jahilci ne daga gare ka, abun kyama, kuma dole ne akanka ka sake sallah bayan ka yi wanka, kana mai tuba zuwa ga Allah (سبحانه وتعالى).

Shi kuma dutsen da ya rotse kanka har ya kwararar da jinni babu komai a kan haka.

Shi kuma amai da ya fita maka ba tare da zabinka ba, to ba zai ɓata maka azuminka ba; saboda faɗin Annabi (صلى الله عليه وسلم):

«مَنْ ذَرَعَهُ الْقَيْءُ فَلَا قَضَاءَ عَلَيْهِ، وَمَنِ اسْتَقَاءَ فَعَلَيْهِ الْقَضَاءُ».

Ma'ana: "Wanda amai ya rinjaye shi to babu ramukon azumi akansa, duk kuma wanda ya janyo amai to wajibi ne akansa ya yi ramuko", Ahmad da ma'abota littafan "sunan" suka rawaito shi da isnadi ingantacce.

WALLAHU A'ALAM

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURƘƘ

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments