Ticker

6/recent/ticker-posts

Mene ne hukuncin wanda ya ci ko ya sha da mantuwa, a cikin yinin ramadana?

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Mene ne hukuncin wanda ya ci ko ya sha da mantuwa, a cikin yinin ramadana?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Babu wata matsala a kansa kuma azuminsa ingantacce ne, saboda fadin Allah (SWA) a ƙarshen suratul baƙara ayata 286: 

ربنا لا تؤاخذنا إن نسينا أو أخطانا.

Ma'ana: "Ya Ubangijinmu kada ka kama mu idan muka yi mantuwa ko muka yi kuskure"

Kuma ya inganta daga Manzon Allah (SAW) cewa Allah Ta'alah ya ce: 

قد فعلت.

Ma'ana: "Lallai na amsa"

Muslim ya rawaito shi daga hadisin Abdullahi bn Abbas (ra), a lamba ta 1206).

Da kuma abin da ya tabbata daga Abu-huraira (ra) daga Annabi (SAW) lallai ya ce: "Duk wanda ya manta -alhalin yana azumi sai ya ci ko ya sha, to ya cika azuminsa; saboda Allah ne ya ciyar da shi, ya kuma shayar da shi"

Bukhari da Muslim su ka rawaito shi.

👉 Duba cikin littafin: TUHFATUL IKHWAN, (tambaya ta 16),  da

👉 MAJMU'U FATAWA WA MAKAALAAT MUTANAWWI'AH, (15/ 291-292).

ALLAH NE MAFI SANI

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa  a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/EYxwmBW9U2o1wckaƙ48MƘ4

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments