Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Yin Sallar Tahajjud A Masallaci

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamualaikum dafatan malam yana cikin koshin lafiy Amin. malam ni tambayata ita ce yana da kyau mutum yayi sallar Tahajjud a masallaci?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Annabi ya ce “Mafificiyar sallarku (tahajjud) wacce kuka yita a gida ne sai dai sallar farilla kawai(Dubi Tirmizi Bisharhil Ahuz 2\00).

An ruwaito a cikin Bukhari mafificiyin sallar mutum a gidansane sai dai sallar Farilla kawai.

(Dubi Fathul Bary 3\0 ko Umdatul Ƙary.

A cikin Hadisin Abdullahi bn Sa’ad ya ce “Na tambayi Manzon Allah a kan sallar mutum tahajjud a gidansa da yin ta a masallaci wanne ya fi? sai Annabi ya ce “shin ba ka ganin gidana ba wanda ya fi shi kusa da masallaci, amma na yi sallah a gidana (tahajjud) ya fi na yi sallah amasallaci sai dai sallar farilla” (Dubi Ibn Majah 1\39).

An karɓo daga Zaidu bn Sabit (RA) daga Manzon Allah cewa “Sallar mutum a gidansa tafi sallarsa a masallacina. (wato masallacin Annabi). sai dai sallar farilla”(Dubi

Abu Dawud 1\9, taglikutta aliƙ 1/ 239 Nailal Audar 3\5 ko Ash shama,il 150).

Don haka yin nafilar tahajjud a gida y afi yin ta akowani masallaci falala. tunda Annabi ya fifita nafila a gidage a bisa masallacinsa.

A nan ne Hafizu bn Hajar yake cewa: Yin tahajjud a gida lallai shi ya fi falala ga al’umma gaba ɗaya, domin shi ne amsar da Annabi ya baiwa mai tambaya, fatahul bary juzu’I na 3 shafi na 25\6 Abu daud juzu’I na1 shafi na 69 Tajujjami’u juzu’I na 1 shafi na 332 Nailul Audhar juzu’Ina 3 shafi na 95 Tagliƙutta’aliƙ juzu’I na 1 shafi 239 Ashshama’il shafi na 157

Amma duk da haka rafkanannu a cikin garuruwan kasannan (Nigeria) suna karfafa mata a kan fitowa masallaci da tsakar dare domin yin sallar Tahajjud. Alhali Annabi ya ce da ummu Humaidu Allah ya yarda da ita, yayin da ta zo gurin Manzon Allah tace “ Ya Rasulullahi inaso na yi sallah tare da kai” sai ya ce “Na sani kinaso ki yi sallah tare dani,

amma ki yi sallah a’yar kurin dakinki ya fi ki yi sallah a falonki, ki yi sallah a tsakar gidanki ya fi ki yi sallah a masallacin mutanenki, kuma ki yi sallah a masallacin mutanen ki ya fi ki yi sallah a masallaci na wannan”.(Ahmad ne ya ruwaito 6\71 da Ibn Khuzaima a cikin sahihinsa 3\5 da Ibn Abdul Barri a cikin Tamhid 23\98).

Wannan yana nuna sallar mace ta farillah a cikin gidanta ya fi ta yi  a masallaci to yaya kuma Nafila. Donhaka yin tahajjud a gida ya fi yin ta a masallaci a wajen mace ko namiji.

WALLAHU A'ALAM

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa  a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BpO6i5KwGBm8IcVtlhBr0j

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

 

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments