𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Mene ne Hukuncin Wanda Ya ci Ko Ya Sha Bisa Mantuwa Alhali Yana Azumin
Ramadan?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Sai ya cigaba da azuminsa yana nan bai kare ba, domin Allah ne ya ciyar da
shi ya shayar dashi. Dalili kuwa ya tabbata daga Abi Hurairata (RA) daga Manzon
Allah ﷺ yace “Idan mutum ya manta, yaci ko ya
sha, to sai ya cigaba da azuminsa, domin Allah ne ya ciyar dashi ya shayar
dashi”.
Attarghib wattarhib na munzuri lahakikin sheikh Albani Juzu’I na farko. (2)
Surah Baƙarah, aya 183 (3)
Bukhari (1933)
Amma wasu daga cikin malaman malikiyya sunce sai ya rama wannan azumin. Sai
dai lafazin hadisin ya zama raddi a garesu, saboda manzon Allah ﷺ
anan ya ambaceshi a “sai ya cika azuminsa” ya tabbatar da cewa azumine bai kare
ba.
WALLAHU A'ALAM
Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa a
Sunnah.
HUKUNCIN WANDA YA KARYA
AZUMINSA BISA GA MANTUWA
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Menene hukuncin Mutumin da yakarya Azuminsa bisa ga mantuwa
ta hanyar Ci ko Sha ko ta hanyar yin Jimā'i da Mātarsa bisa ga kuskure, Shin
akwai ramuwa ko Kaffāra akansa ko babu??
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Alal-Haƙiƙa mafi
yawa daga cikin Mālamai
(Jumhūrul-Ulamā'u) sun tafine akan cewa
Mutumin da yakarya Azuminsa da mantuwa ta hanyar Ci ko
Sha, to Azuminsa yana nan lafiya ƙalau
babu wata ramuwa akansa, kuma koda wanne irin Azumine yakeyi to duk hukuncin
dayane, Misali kamar
1. AzAzumin-Nāfila.
2. AzAzumin-Kaffāra.
3. AzAzumin-Bākance.
4. AzAzumin-Rāmuwa.
5. AzAzumin-Ramadan.
Dadai
sauran dukkan wani nau'i na Azumi, Mālamai sukace babu komai akansa, daga cikin Dalilansu
sunkafa Hujja da wannan Hadisi na Mαnzon Aʟʟαн
(Sallallahu alaihi Wasallam)
da Yake cewa:
"من نسي
وهو صائم فأكل أو شرب فليتم صومه، فإنما أطعمه الله وسقاه" (متفق عليه)
MA'ANA:
Wanda
yamanta yana Azumi sai yaci ko yasha to kawai yacika Azuminsa, domin kuwa Aʟʟαн(ﷻ)
ne Ya ciyar dashi kuma ya shāyar dadash.
Saidai
dangane da Hukuncin wanda ya karya Azuminsa da mantuwa ta hanyar yin
Jimā'i da Mātarsa, ko yasadu da'ita
bisa ga kuskure, kamar Misāli
yana zaton cewa Al-Fijir bai ketoba ashe kuma
yariga yāfito, kokuma
yana zaton cewa rāna
ta fāɗi ashe bata fāɗiba, ko ya sadu da Mātarsa
bisa ga Jāhilci, kamar Misāli tunda yake bai taɓa
sanin ko bai taɓa jin
cewa Harāmunne ayi Jimā'i da rānaba,
Mālamai sunyi Saɓāni dangane da wannan MMas'ala.
Mazhabin
Shāfi'iyya da Hanafiyya duk sun tafine akan cewa
wanda yayi Jimā'i da kuskure ko mantuwa shima babu komai akansa
domin Azuminsa bai lālaceba, danhaka babu ramuwa
akansa, sunkafa Hujjane da wannan Hadisi na Mαnzon Aʟʟαн
(Sallallahu alaihi Wasallam)
wanda Yake cewa:
"من أفطر
في رمضان ناسيا فلا قضاء عليه ولا كفارة"
MA'ANA:
Wanda
ya karya Azuminsa da mantuwa acikin watan ramadan, to babu ramuwa akansa kuma
babu KaKaffāra.
Anan
Sai Mālamai sukace ma'anar wannan
Hadisin tagame dukkan wani abu da Mutum zaiyi wanda zai iya lalata masa Azumi, indai yayine da mantuwa
shikenan babu komai akansa.
Amma
Mazhabin Mālikiyya suntafi akan cewa zai rama
wannan Azumin amma babu Kaffāra
akansa sakamakon Uzuri na mantuwa ko kuskure da yayi.
Saidai
Mazhabin Hanābila tare da wani Sāshe na Mālamai
sun tafine akan cewa wanda yayi Jimā'i da mantuwa ko kuskure, to wajibine sai yayi Kaffāra,
daga cikin Dalilansu sunkafa Hujja da Hadisin wani Mutumin-Ƙauye da yazo wajen Mαnzon Aʟʟαн
(Sallallahu alaihi Wasallam)
yana cewa ya halaka, sakamakon yasadu da Mātarsa da rana, acikin Hadisin an
ambaci cewa sai yayi Kaffāra, danhaka sukace wanda yayi Jimā'i
da ganganci da wanda yayi Jimā'i da Mantuwa ko da kuskure kokuma Jāhilci
ko wanda aka tīlastāshi
yayi, sukace duk hukuncinsu ɗayane
dole sai sunyi Kaffāra.
To
amma Saidai magana mafi inganci kamar yadda mafi yawan Mālamai suka tafi akanta
shine, babu wata Kaffāra akansu, saboda Faɗin Aʟʟαн(ﷻ):
رَبَّنَا
لَا تُؤَاخِذْنَا إِن نَّسِينَا أَوْ أأَخْطَأْنَ
MA'ANA:
Yā
Ubangijinmu (ﷻ) kada ka kāmāmu (akan
laifin da mukayi da) mantuwa ko da kuskure. (Suratul Baqara aya ta 286)
шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαм
Mυѕтαρнα Uѕмαn
08032531505
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/I3vXUPymspzLawMCwJ44H2
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.