Ticker

6/recent/ticker-posts

Mene ne hukuncin bin masallaci sallan tarawi daga cikin gida?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Ya aiki? Don Allah tambayata ita ce mace za ta iya bin masallaci sallar tarawi a gida ba tare da taje masallaci ba. Na gode

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

A'a Sai dai ta fita izuwa masallacin ko kuma ta yi  sallar Tarawih ɗinta ita kaɗai a cikin gidanta ba tare da bin liman ba, kai koda a cikin masallaci idan mutum ya ware can gefe yabi liman ba tare da ya shiga cikin sahu ba to bashi da sallah, Sabida Tirmizi da abu dawud da Imamu Ahamad sun rawaito Hadisi cewa: WANI MUTUM YAYI SALLAH A BAYAN SAHU BAYAN AN IDAR DA SALLAH SAI MNZON ALLAH YA UMARCESHI DA YA SAKE SALLAH To kinga idan har wanda yayi sallah a masallaci sabida be cike sahu ba Annabi ya ce masa yaje ya sake sallah Ina ga kuma wacce tabi masallaci sallah daga cikin gida??

WALLAHU A'ALAM

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa  a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BpO6i5KwGBm8IcVtlhBr0j

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments