Ticker

6/recent/ticker-posts

Jinin Haila Ya Zo Min Saura Minti 3 Rana Ta Faɗi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum, Malam tambayata ita ce mata ce ta yi azumi har saura minti 3 a kira sallah magariba sai jinin hailarta ya zo. To tambayata a nan ita ce, wannan azuminta na wannan ranan yana nan ko za ta biya bayan sallah?. Allah Ya karawa Malamanmu basira.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam, in har jinin hailar ya fito a wancan lokacin da ka ambata,, to azumin ta ya karye.

Saboda azumi yana kammala ne bayan faɗuwar rana, ita kuma na ta ya warware kafin lokacin, wannan ya sa za ta rama bayan sallah.

Allah ne mafi sani.

Amsawa: Dr. Jamilu Zarewa.

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa  a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/JLojawdOWYsEOeSHZMNdjf

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments