𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Mene ne hukuncin i'itikafi ga namiji da mace? Sannan da
wadanne abubuwa ake son mutum mai i'itikafi ya shagalta da su? Yaushe ne kuma
zai shiga wurin i'itikafinsa? Yaushe ne kuma zai fita daga cikinsa?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
I'itikafi sunnah ne ga maza da mata, saboda abun da ya
tabbata daga Annabi (صلى الله عليه وسلم) na cewa ya yi i'itikafi a watan Ramadan, kuma daga ƙarshe sai lamarinsa ya tabbata a kan i'itikafin kwanaki goman ƙarshen
Ramadan, kuma sashin matansa sun kasance suna yin i'itikafi tare da shi (صلى الله عليه وسلم), haka kuma
matansa sun cigaba da yin i'itikafi a bayansa.
Kuma mahallin da ake yin i'itikafi shi ne: masallacin da
ake yin sallar jam'i, kuma idan a kwanakin i'itikafinsa juma'a za ta gitta to
an so ya aiwatar da i'itikafinsa a masallacin juma'a.
Kuma a mafi ingancin magana daga zantukan maluma;
i'itikafi bashi da wata iyaka da aka iyakance masa, kuma ba a shardanta yin
azumi tare da i'itikafi, saidai kuma yinsa tare da azumin shi ne ya fi.
Kuma sunnah ga i'itikafi shi ne mai yinsa ya shiga wurin
i'itikafinsa a lokacin da ya niyyaci haka, ya kuma fita daga wurin bayan ƙarewar lokacin da ya diba wa kansa; (ko ya niyyata), amma ya samu damar ya yanke i'itikafinsa (ya
fita daga masallaci) idan akwai buƙatar hakan, saboda kasancewar i'itikafi
sunnah ne, da baya wajaba a kan mutum
don shiga cikinsa ko fara shi, matuƙar dai ba
na bakance ba ne.
Kuma mustahabbi ne a yi i'itikafin kwanaki goman ƙarshen watan Ramadan, a matsayin koyi da Annabi (صلى الله عليه وسلم), kuma duk wanda
zai yi i'itikafinsa to mustahabbi ne ya shiga wurin i'itikafin bayan sallar
asubah, a yinin ashirin da ɗaya (21), yana mai koyi da Annabi (صلى الله عليه وسلم), sai kuma ya
fita idan kwanaki goman suka ƙare, idan kuma ya yanke shi gabanin
cikar kwanaki goman to babu laifi akansa, matuƙar dai ba
bakance ya yi ba, kamar yadda ya gabata. Kuma abun da ya fi shi ne ya kama wuri
aiyananne a masallaci –in hakan ya sauƙaƙa masa-, kuma an shar'anta wa mai
i'itikafi cewa ya yawaita ambaton Allah, da karatun alƙur'ani da
neman gafara, da addu'oi, da kuma salloli matuƙar dai ba a
lokutan hani ba ne. Kuma babu laifi wassu daga cikin abokansa su ziyarce shi,
haka kuma babu laifi ya yi tadi da su, kamar yadda Annabi (صلى الله عليه وسلم) wassu daga cikin
matansa su ke ziyartarsa, su ke kuma yin tadi da shi, har ma a wata rana matarsa Uwar muminai Safiyyah ta ziyarce shi alhali
yana i'itikafi a cikin watan azumi, a yayin da ta tashi za ta koma sai ya tashi
tare da ita ya raka ta bakin kofar masallaci, Sai hakan ya nuna cewa babu laifi
kan aikata irin wannan.
Kuma wannan aikin nasa ya ƙara fito da
cikar ƙanƙan-da-kan Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم) da tawali'unsa,
da kuma kyakkyawar mu'amalarsa tare da matansa, Allah ya yi daɗin yabo da salati
a gare shi.
Wannan mas'alah an yaɗa ta a cikin littafinsa
TUHFAUL IKHWAAN, tana nan kuma a cikin MAJMU'U FATAWA WA MAƘAALAAT MUTANAWWI'AH (15/441-443).
Wannan ya zo daga A'ishah (رضي الله عنها) a cikin Sahihul
Bukhariy (lamba: 2072), da Muslim (lamba: 1172).
Bukhariy ya rawaito shi (lamba: 2035), da Muslim (lamba:
2175).
Hukunce-Hukuncen Ittikafi
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Mene ne hukuncin i'itikafi ga
namiji da mace? Sannan da wadanne abubuwa ake son mutum mai i'itikafi ya
shagalta da su? Yaushe ne kuma zai shiga wurin i'itikafinsa? Yaushe ne kuma zai
fita daga cikinsa?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
I'itikafi sunnah ne ga maza da
mata, saboda abun da ya tabbata daga Annabi (صلى الله عليه وسلم)
na cewa ya yi i'itikafi a watan Ramadan, kuma daga qarshe sai lamarinsa ya
tabbata akan i'itikafin kwanaki goman qarshen Ramadan, kuma sashin matansa sun
kasance suna yin i'itikafi tare da shi (صلى الله عليه وسلم),
haka kuma matansa sun cigaba da yin i'itikafi a bayansa.
Kuma mahallin da ake yin
i'itikafi shi ne: masallacin da ake yin sallar jam'i, kuma idan a kwanakin
i'itikafinsa juma'a za ta gitta to an so ya aiwatar da i'itikafinsa a
masallacin juma'a.
Kuma a mafi ingancin magana daga
zantukan maluma; i'itikafi bashi da wata iyaka da aka iyakance masa, kuma ba a
shardanta yin azumi tare da i'itikafi, saidai kuma yinsa tare da azumin shi ne
ya fi.
Kuma sunnah ga i'itikafi shi ne
mai yinsa ya shiga wurin i'itikafinsa a lokacin da ya niyyaci haka, ya kuma
fita daga wurin bayan qarewar lokacin da ya ɗiba
wa kansa; (ko ya niyyata), amma ya samu damar ya yanke i'itikafinsa (ya fita
daga masallaci) idan akwai buqatar hakan, saboda kasancewar i'itikafi sunnah
ne, da baya wajaba akan mutum don shiga cikinsa ko fara shi, matuqar dai ba na
bakance ba ne.
Kuma mustahabbi ne a yi
i'itikafin kwanaki goman qarshen watan Ramadan, a matsayin koyi da Annabi (صلى الله عليه وسلم), kuma duk wanda zai
yi i'itikafinsa to mustahabbi ne ya shiga wurin i'itikafin bayan sallar asubah,
a yinin ashirin da ɗaya
(21), yana mai koyi da Annabi (صلى الله عليه وسلم),
sai kuma ya fita idan kwanaki goman suka qare, idan kuma ya yanke shi gabanin
cikar kwanaki goman to babu laifi akansa, matuqar dai ba bakance ya yi ba,
kamar yadda ya gabata. Kuma abun da ya fi shi ne ya kama wuri aiyananne a
masallaci –in hakan ya sauqaqa masa-, kuma an shar'anta wa mai i'itikafi cewa
ya yawaita ambaton Allah, da karatun alqur'ani da neman gafara, da addu'oi, da
kuma salloli matuqar dai ba a lokutan hani ba ne. Kuma babu laifi wassu daga
cikin abokansa su ziyarce shi, haka kuma babu laifi ya yi taɗi da su, kamar yadda Annabi
(صلى الله عليه وسلم) wasu daga cikin
matansa su ke ziyartarsa, su ke kuma yin taɗi
da shi, harma a wata rana matarsa Uwar muminai Safiyyah ta ziyarce shi alhali
yana i'itikafi a cikin watan azumi, a yayin da ta tashi za ta koma sai ya tashi
tare da ita ya raka ta bakin kofar masallaci, Sai hakan ya nuna cewa babu laifi
kan aikata irin wannan.
Kuma wannan aikin nasa ya qara
fito da cikar qanqan-da-kan Manzon Allah (صلى الله عليه وسلم)
da tawali'unsa, da kuma kyakkyawar mu'amalarsa tare da matansa, Allah ya yi daɗin yabo da salati a gare
shi.
Wannan mas'alah an yaɗa ta a cikin littafinsa
TUHFAUL IKHWAAN, tana nan kuma a cikin MAJMU'U FATAWA WA MAQAALAAT MUTANAWWI'AH
(15/441-443).
Wannan ya zo daga A'ishah (رضي الله عنها) a cikin Sahihul Bukhariy (lamba: 2072),
da Muslim (lamba: 1172).
Bukhariy ya rawaito shi (lamba:
2035), da Muslim (lamba: 2175).
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
WALLAHU A'ALAM
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/JoWs3feDfdyGE9yBsa1RSC
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.