Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Ana Fitar Da Zakkar Fid-Da-Kai Da Gero?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Malam game da zakkar fidda Kai da ake yi ana iya fitarwa da gero alhali mutum na da shinkafa, dalilin da ya sa za su fitar da gero saboda su ma shinkafa wata rana tana buwayarsu. amma lokutan ba ya suna fiddawa ne da shinkafa, amma shinkafar su ma ba su cika sonta ba. Kuma an ce ba a ba Allah abun da ba ka so, shin suna iya fitarwa da gero?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salámu, 'yar uwa bayani yalwatacce ya gabata a Amsoshin Tambayoyinku a kan hukunce-hukunce masu alaƙa da Zakkar Fid-da-kai, kina iya komawa can domin samun ƙarin bayanai. A hadisan da suka yi magana game da zakkar fidda-kai sun tabbatar cewa Annabi ya farlanta a fitar da zakkar fidda-kai da wasu nau'o'i na abinci, sai malamai suka fassara hakan da cewa:

Mutum zai fitar da zakkar fidda-kai ne da nau'in abincin da aka fi ci a garinsu, wato ba dole ne sai nau'in abinci guda ɗaya tal ba, mutum zai lura da nau'in abincin da aka fi ci ne a garinsu, kuma ya zama nau'i ne da yake da halin fitar da zakkar da shi. Don haka babu laifi idan kun fitar da zakkar fidda-kai da gero, saboda shi ma yana daga cikin abincin da ake yawaita ci a ƙasar Hausa.

Allah S.W.T ne mafi sanin daidai.

Jamilu Ibrahim, Zaria.

Ga masu buƙatar shiga Wannan Group zasu iya bi ta links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/CƘ9TMXMrWDx1y7sYye2znU

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments