𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum malam, Allah ya kara maka basira, malam
dan Allah tambayata a nan ita ce, ni ce na yi sallar Isha, na kuma yi Shafa'i
da Wuturi, to kuma sai Allah ya ba ni ikon tashi cikin dare, shin Wuturi zan
sake ko dukka zan sake?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salám, amin na gode bisa addu'o'iku na
alheri. Babu laifi ga wanda ya yi wutiri
a farkon dare ko a tsakiyar dare idan ya sake yin wata sallar nafila a daren a
bayan wutirin nan nasa, sai dai abin da aka fi so shi ne mutum ya sanya
sallarsa ta ƙarshen dare ta zama wutiri ne, saboda Abdullahi ɗan umar ya ruwaito
cewa Annabi ﷺ ya ce: "Ku sanya sallarku ta ƙarshen dare
ta zama wutiri".
Albukhariy (998), Muslim (751).
Amma wanda ya riga ya yi sallar wutiri, to idan ya sake
yin wasu raka'o'in a bayanta ba zai sake maimaita wani wutiri daga baya ba.
Saboda hadisi ya tabbata daga Dalƙ ɗan Aliyu ya ce: Na ji Manzon Allah ﷺ yana cewa:
"Ba a wutiri biyu a dare ɗaya". Attirmizhiy (470), Annasá'iy (1679), Abu Dawud
(1439).
Wato dai a taƙaice idan mutum ya riga ya yi sallar
wutiri sai kuma daga baya ya so ya yi sallar nafila a daren, to hakan ya
halasta ba tare da wani karhanci ba, saboda umurnin da Annabi ﷺ ya bayar cewa a
sanya sallah ta ƙarshe a dare ta zama wutiri, ba umurni
ne na wajabci ba, umurni ne na mustahabbanci, sai dai kamar yadda bayani ya
gabata, duk wanda ya yi sallar wutiri, kuma ya ƙara yin
sallah a bayanta, to ba zai maimaita
wani wutiri na biyu ba, kamar yadda hadisin can ya bayyana.
Dubi Almuhallá (2/91, 92), da Almajmú'u (4/16).
Allah S.W.T ne mafi sanin daidai.
Jamilu Ibrahim, Zaria.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/Cnf26Ƙ8MPƙz9yUYU1nxƙRƙ
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.