Ticker

6/recent/ticker-posts

Addu'ar Buɗe Sallah (Du'a'ul Istiftahi)

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum, yayana ina godiya mara adadi, dan Allah ina so a dan kara min bayani a kan addu'o'in da ake yi kafin a ta da sallah.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus salám, Sahabbai da dama sun ruwaito cewa Annabi ya kasance yana buɗe sallah da addu'o'i da dama da suka haɗa da:

1. Abu Hurairata Allah ya ƙara masa yarda ya ce: Manzon Allah ya kasance yana yin shiru a tsakanin kabbarar harama da karatu na ɗan lokaci, sai na ce ya Manzon Allah Mahifina da Mahaifiyata fansa ne a gare ka, yin shiru ɗin da kake yi a tsakanin kabbara da karatu mene kake faɗi? Sai Manzon Allah ya ce: Ina cewa ne:

"اللَّهُمَّ بَاعِدْ بَيْنِي وَبَيْنَ خَطَايَايَ ، كَمَا بَاعَدْتَ بَيْنَ المَشْرِقِ وَالمَغْرِبِ ، اللَّهُمَّ نَقِّنِي مِنَ الخَطَايَا ، كَمَا يُنَقَّى الثَّوْبُ الأَبْيَضُ مِنَ الدَّنَسِ ، اللَّهُمَّ اغْسِلْ خَطَايَايَ بِالْمَاءِ ، وَالثَّلْجِ ، وَالبَرَدِ".

Bukhariy (744), Muslim (598).

2. Nana A'isha Allah ya ƙara mata yarda ta ruwaito cewa Manzon Allah ya kasance idan zai buɗe sallah yana cewa:

"سُبْحَانَكَ اللَّهُمَّ وَبِحَمْدِكَ ، وَتَبَارَكَ اسْمُكَ وَتَعَالَى جَدُّكَ ، وَلَا إِلَهَ غَيْرَكَ".

Abu Dáwud (776), Attirmizhiy (243).

3. Daga Aliyu Allah ya ƙara masa yarda ya ce: Ya kasance Manzon Allah idan ya miƙe zai yi sallah yana cewa:

"وَجَّهْتُ وَجْهِيَ لِلَّذِي فَطَرَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ حَنِيفًا ، وَمَا أَنَا مِنَ الْمُشْرِكِينَ ، إِنَّ صَلَاتِي ، وَنُسُكِي ، وَمَحْيَايَ ، وَمَمَاتِي لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ ، لَا شَرِيكَ لَهُ ، وَبِذَلِكَ أُمِرْتُ وَأَنَا مِنَ الْمُسْلِمِينَ ، اللهُمَّ أَنْتَ الْمَلِكُ لَا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ أَنْتَ رَبِّي ، وَأَنَا عَبْدُكَ ، ظَلَمْتُ نَفْسِي ، وَاعْتَرَفْتُ بِذَنْبِي، فَاغْفِرْ لِي ذُنُوبِي جَمِيعًا ، إِنَّهُ لَا يَغْفِرُ الذُّنُوبَ إِلَّا أَنْتَ ، وَاهْدِنِي لِأَحْسَنِ الْأَخْلَاقِ لَا يَهْدِي لِأَحْسَنِهَا إِلَّا أَنْتَ ، وَاصْرِفْ عَنِّي سَيِّئَهَا لَا يَصْرِفُ عَنِّي سَيِّئَهَا إِلَّا أَنْتَ ، لَبَّيْكَ وَسَعْدَيْكَ وَالْخَيْرُ كُلُّهُ فِي يَدَيْكَ ، وَالشَّرُّ لَيْسَ إِلَيْكَ ، أَنَا بِكَ وَإِلَيْكَ ، تَبَارَكْتَ وَتَعَالَيْتَ ، أَسْتَغْفِرُكَ وَأَتُوبُ إِلَيْكَ".

Muslim (771), Annasá'iy (897).

Asshaikh Abdul'aziz bn Baaz ya ce: "Wannan addu'ar ta uku Annabi ya kasance yana karanta ta ne a sallar nafila ta dare, amma a sallar farillah, abin da ya fi shi ne karanta waccan addu'ar ta farko ko ta biyu, wannan shi ne abin da aka kiyaye daga gare shi  a sallar farillah, amma buɗe sallah da addu'a mai tsawo ya kasance yana yin ta ne a sallar tahajjud".

Duba Fataawá Nurun Alad Darb (8/182).

Baya ga waɗannan akwai wasu addu'o'in da dama da Manzon Allah yakan buɗe sallarsa da su da ba zai yiwu a kawo su duka a nan ba.

Allah S.W.T ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURƘƘ

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments