𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum malam. Na yi sallar Isha'i sai na yi
shafa'i ban yi wutiri ba ina son in farka zuwa Ƙarfe 2:am
in yi nafila sannan in rufe da wutiri sai bacci ya dauke ni ban farka ba sai da
Asuba, shi ne aka ce min sai na yi wutiri sannan in yi Asuba, kuma lokacin an
tsayar da sallah. Shin malam haka ne?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus salam, malamai sun yi ittifaƙi cewa lokacin sallar Wuturi yana farawa 'bayan sallar
Isha'i zuwa ɓullowar Alfijir' ne, saboda dalilai da dama da suka
tabbata daga Manzon Allah ﷺ da suka haɗa da hadisin da Abu Nadhrata ya ruwaito daga Abu Sa'eed
cewa: Manzon Allah ﷺ ya ce: "Ku yi Wuturi kafin ku yi Asubahi".
Muslim (754).
Amma malaman sun yi saɓani game da
halascin yin sallar Wuturi bayan ɓullowar Alfijir kafin a yi sallar Asubahi, daga cikinsu
akwai waɗanda suka hana yin
hakan, daga cikinsu kuma da waɗanda suke ganin halascin yin Wuturi bayan ɓullowar Alfijir
matuƙar ba a yi Asubahi ba.
Daga cikin waɗanda suka hana akwai Abu Yusuf da Muhammad bn Hassan
abokan Abu Haneefa, da Sufyan ATthauriy. Waɗanda suke ganin ya
halasta a yi Wuturu bayan ketowar Alfijir kafin tsayar da sallar Asubahi kuwa
su ne Imam Asshafi'iy, da Imam Malik, da Imam Ahmad.
Abin da ya sa suka yi saɓani game da hakan
shi ne, saboda an sami wasu dalilai daga ayyukan Sahabbai cewa sun yi sallar
Wuturi bayan Alfijir ya keto kafin a tsayar da sallar Asubahi, sai dai duk da
haka, ayyukan na Sahabbai ya nuna ba ya halasta a yi sallar Wutiri bayan sallar
Asubahi kamar yadda wancan hadisi na Abu Nadhrata da wasu hadisan suka
tabbatar. Amma kuma yin Wuturi ɗin bayan ɓullowar Alfijir kafin a yi Asubahi yana matsayin ƙala'i ne ba a matsayin ada'i ba.
Duba littafin Ibnu Rushdi, BIDAAYATUL MUJTAHID WA
NIHAAYATUL MUƘTASWID (1/212),
don neman ƙarin bayani.
Saboda haka ƴar uwa idan kin lura za ki ga cewa
lokacin sallar Wuturi yana farawa ne bayan Isha'i zuwa ketowar Alfijir, idan
mutum bai sami damar yi ba a wannan lokaci zai iya yin ta a bayan ɓullowar Alfijir ɗin kafin a yi
Asubahi a bisa ɗaya daga fahimtar malamai.
Ke nan wannan ya nuna matuƙar an fara
sallar Asubahi to babu maganar yin sallar Wuturi, sai a haƙura a tara
a gaba, tun da ke ma kin ce har an tsayar da sallah, don haka maganar da aka faɗa maki cewa sai
kin yi wuturi kafin ki yi Asubahi wannan zai yiwu ne idan har ba a riga an
shiga sallar Asubahi ba, idan ko an fara Asubahi, to babu wannan magana, saboda
akwai ma hadisin da ya ce, idan aka tsayar da sallah, to babu wata sallah sai
ta farillah, kamar yadda Muslim ya ruwaito a hadisi mai lamba: 710.
Allah S.W.T ne mafi sani.
Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/Du5LNx31U9hDi6RƘbbrzgW
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.