𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu
alaikum Don Allah malam a taimaka min da bayani game da sababin da ya sa ake
yin azumi??
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikum
assalam Azumi ginshiki ne, daga cikin turakun musulunci, wadanda addinin
musulunci, ba zai cika ba sai da su, Allah da manzonsa sun yi umarni da shi,
saboda wasu muhimman manufofi, ga wasu daga ciki:
1. Samun tsoron
Allah, saboda mai azumi yana barin abin da yake so saboda Allah, hakan zai sa,
ya kara samun tsoron Allah.
2. Samun kariya
daga Shaiɗan, saboda
azumi yana takure hanyoyin Shaiɗan,
wannan ya sa zunubai suke karanci a Ramadan.
3. Tuna
talakawa da wahalar da suke ciki, saboda duk lokacin da mai kuɗi
ya ɗanɗana
yunwa zai tuna halin da talakawa suke ciki.
4. Saɓawa
rai wajen barin abin da take so, da kuma haƙuri
akan abin da take sha'awa.
5. Kankare
zunubai da kuma samun ɗaukakar daraja,
saboda azumi yana gyara zuciya, da kuma rai.
6. Samun
lafiyar jiki, saboda azumi yana kariya daga cututtuka masu yawa, kamar yadda
likitoci suka tabbatar da hakan.
7. Ta hanyar
azumi mutum zai saba da yin aikin don Allah, saboda azumi sirri ne tsakanin
Allah da bawansa.
Allah ne mafi
sani
DR. JAMILU
YUSUF ZAREWA
Ku Kasance Damu
Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa a Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/J1hm5Tw12uYBƙfaiPwf28l
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ
ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ
ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ
ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ
ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ
ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ
ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
Post your comment or ask a question.