Ticker

6/recent/ticker-posts

Amsar Wasiƙar Sha'iri Maikwari - Ta Abu-Ubaida Sani

Wasalamu alaikum ɗan uwa,
Farin baƙo mai sallama.

Batun nan naka na jinjina,
Haƙiƙa ka so lalama.

Ka yi batun ko daki-daki,
Salon koyarwar maluma.

Ka yi bayani na gani,
Ga hujja nan ka gama (added).

Lallai a ɗaukar illimi,
Natsuwa na ɗore a can sama.

Da zarar babu akwai wuya,
Ƙwaƙwalwa na yin gardama.

A saka a saka ta zubar shi duk,
Cikinta karatu bai zama.

Idan da natso ko ta kama duk,
Abin da ake hada haɗɗama.

Zama fa a Sakkwato kwai wuya,
Ko ba don zafi ba ma.

Balle a yanzu da azzumi,
Ga kuwa rana na tsima.

Burinta a sau ta ta babbako,
Ta sako  zafi daga can sama.

Na ga waɗansu sukan tafi,
Kwalkwalawa su kwanta ƙorama.

Sai ku kwatanta 'yan uwa,
Zafin ga da me ne yai kama?

Ni dai mabiyi ne ɗalibi,
Komai aka ban zan kinkima.

Komai aka ce mini sai in yi,
Ko yau na ɗau harrama.

Idan in taho ne sai in zo,
Mu sha harbinta mu sha zuma.

Da ma mun san da akwai wuya,
Samun ilimi sai an himma.

Amm in ga hanya biyu,
Garanti duk ba tantama.

To wuf zan yi in laɓaɓa,
In bi mai sauƙi mara riggima.

Ku ba mu sanarwa don mu ji,
Mu san decision in an gama.

Post a Comment

0 Comments