Ticker

6/recent/ticker-posts

Zamani Abokin Tafiya: Kira Da Makeran Karni Na (21) a Garin Talata Mafara

Muƙalar da aka gabatar a ajin ALH 400 (Seminar), a Sashen Harsuna da Al’adu, Jami’ar Tarayya, Gusau, Jahar Zamfara, Nijeriya, (Disamba 2022 - Janairu, 2023).

Zamani Abokin Tafiya: Ƙira Da Maƙeran Ƙarni Na (21) a Garin Talata Mafara

 Samir Aminu Musa

Lambar Waya: 08109474995
 Imel: samiraminumusa95@gmail.com

 Tsakure

Sana’ar ƙira sana’a ce daga cikin sauran sana’o’in gargajiya na Hausawa, da suke aiwatarwa domim samar wa kansu madogara. Wannan sana’a ta ƙira a kan ta za a waiwaya a ga wace waina zamani ya toya, ko kuma yake toyawa a cikin ta a nan cikin garin Talata Mafara, ta fuskar kayan gudanar da sana’ar da kuma kayan amfani da sana’ar take samarwa. A yayin gudanar da wannan bincike an yi amafani da wasu manya-manyan hanyoyin tattara bayanai kamar bitar ayyakan da suka gabata da kuma tattakawa zuwa wasu maƙerai da ake da su a nan cikin garin Talata Mafara.

1.0      Gabatarwa

 Tun ran gini, ran zane, al’ummar Hausawa tun can asali al’umma ce wadda ta gogara da kanta wajen samar da hanyoyin tattalin arziƙinta. Ba a san Hausawa da kasala ko ragwanci ba, tun asalatan suka tashi tsaye tsayin daka da yin sana’o’i daban-daban don wadatar da kansu daga buƙatunsu na yau da kullum. Ta haka ne har ya zama a kowane gidan Bahaushe za ka tarar yana da sana’o’in da yake aiwatarwa.

 Manufar wannan bincike ita ce, nazarin sana’ar ƙira a garin Talata Mafara, domin a ga wane irin ci gaba sana’ar ta zo da shi a wannan zamani da muke ta fuskar kayan gudanar da sana’ar da kuma kayan amfanin al’umma da sana’ar take samarwa.

 A hasashen wannnan bincike, ana sa ran zai fito da wani sauyi da aka samu a cikin sana’ar ƙira a garin Talata Mafara saboda ƙarin samun abubuwan kimiyya da fasaha da ci gaba ya zo da su, Hausawa suka sami sauƙi wajen haɓaka tattalin arzƙinsu

1.1 Dabarun Bincike

 Domin ɗaure akuyar bincike da iccen magarya aka yi amfani da hanyoyin tattara bayanai kamar haka:

i.                    Bitar ayyukan da suka gabata.

ii.                  Nazarce-nazarcen bugaggun litattafai

iii.               Rangadi zuwa masana’antun gudanar da sana’ar ƙira a nan garin Talata Mafara.

2.0      Waiwaye a akan sana’o’in gargajiya

 Masana irin su Ibrahim (2007), Ya ce: “sana’a  hanya ce ta amfani da azanci da hikima a  sarrafa albarkatu da ni’imomin da ɗan Adam ya mallaka don buƙatun yau da kullum. Don haka ke nan sana’a wata abu ce wadda mutum ya jiɓinci yi da nufin samun abin  masarufi don gudanar da harkokin rayuwa. Sana’a abu ce wadda ta danganci tono Albarkatun ƙasa da sarrafa hanyoyin kimiyya da fasaha da ni’imomin da suke tattare da ɗan Adam da sauransu. Sana’o’in su ne mafi girman Matsayi da Hausawa suke amfani da su don yin dogaro da kai, su samar da abubuwan da suke buƙata. Ta hanyar abin da Bahaushe ya samu daga sana’arsa ne yake musanyawa ya mallaki abubuwan da ba zai iya samar-wa kansa ba.”

Watau sana’a hanya ce ta tsururin arziƙi da alumma suke biya lungu da saƙo dare da rana domin haɓaka tattalin arzƙinsu. Musamman alummar Hausawa da yake sun daɗe suna yin fafutikar neman na kai domin kar a gani ga tsara. Kamar yadda aka sani Hausawa suna da ire-iren sana’o’in da suke aiwatarwa, ko da yake ba a iya ƙayyade adadin nauukan sanaoin Hausawa na gargajiya, amma daga cikinsu akwai:

(1)   Sana’ar Ƙira

(2)   Sana’ar Fawa

(3)   Sana’ar Noma

(4)   Sana’ar Farauta

(5)   Sana’ar Gini

(6)   Sana’ar Rini

(7)   Sana’ar Kiyo

(8)   Sana’ar Su

(9)   Sana’ar Dukanci

(10)Sana’ar Wanzanci. Da sauransu.

2.1      Ma’anar Sana’ar Ƙira

Malamai irin su Zarruƙ da Al- Hassan (1987), sun bayyana ma’anar ƙira cewa: sanaa ce da ake sarrafa ƙarfe ta hanyar narka shi cikin wuta sannan a fito da narkakken ƙarfen a bubbuge shi zuwa sifar da ake so ya zama.”

Haka kuma an ruwaito a cikin katafaren Ɗakin Karutun nan (rumbun ilimi), “sana’ar ƙira sanaa ce da ake sarrafa tama da ƙarafa, zinariya ko azurfa, da sauran dangogin ƙarfe a mayar da su abin amfani wanda ka iya zama makami ko maaikaci abin yin sanaa.

 Gusau da Bello (2012), sun ce: “ƙira ita ce ƙera

 abubuwa kamar kayan doki ko kayan noma,

 kayan yaƙi misali sulke da takobi da mashi da sauransu.

 Maƙera su ne masu aikin ƙira maƙeri kuwa mutum

 ɗaya ke nan, maƙera kuma ana nufin wurin da ake yin

 ita ƙirar.

 Akwai maƙeran fari waɗanda suke aiki da azurfa da

 tagulla da jan ƙarfe da zaiba da goran ruwa da dalma

 da gaci da taba. Suke ƙera ƙananan kaya irin na adon

 mata kamar zobe da munduwa da kayan dawaki da

 sauransu.

 Kuma akwai maƙeran baƙi, waɗanda suke ƙera

 kayan noma da yaƙi da na fawa da na aski da sauran

 sauran sana’o’i.

 Maƙera masu ƙarfi ne ga kuma jimirin zafin wuta,

 har ba su kulawa da ita in suna cikin aikinsu.

 Wannnan sana’a tana da sarki wanda yake shi ne

 shugaban duk wani maƙeri na wannan nahiyar ana

 kiransa sarkin maƙera, galibi hakimi ko sarkin gari ke

 naɗa shi. Don haka ne kowace ƙasa ko gari da nata

 sarkin maƙera.

 Maƙera sukan yi ƙira da ƙarafa daban-daban,

 kamar zinariya da azurfa da gaci da farin ƙarfe da

 baƙin ƙarfe da jan ƙarfe da sanholama da dalma

 da tagulla da zaiba da sauransu.

 Daga nan kuma sai kayan aikin maƙera daga

 cikinsu a akwai zuga-zugan da ake hura wuta da su

 da gawayi da masaba ta bugun ƙarfe da hama da

 muntalaga da hantsaki ko awartaki da uwar maƙera

 da sauransu.

 Lokacin ƙira maƙeri zai zauna maƙera tun da farko

 zai sa gawayi ya hura zuga-zugi, sai ya saka ƙarfe

 cikin wuta idan ya yi ja, sai ya fitar da shi ya riƙa

 bugawa da masaba bisa uwar maƙera ya sarrafa

 ƙarfen yadda yake so. Tare da taimakawar sauran

 kayan aikinsa, zai ƙera dukan abin da yake so

                         kamar garma ko fartanya da makamantansu. Idan

 maƙerar farin ƙarfe ce ana amfani da waɗannan

 kaya domin ƙera kayan ƙawar mata wato azurfa

 ko tasa ko zinariya ko tagulla ko dalma.”

Daga waɗannan ma’anoni da masana suka bayar ake iya fahimtar cewa sana’ar ƙira sanaa ce da ake cin gajiyar ta, ta hanyar amfanuwa da abubuwan da masu aiwatar da sana’ar ke samarwa na amfanin yau da gobe. Sana’a ce da take samar da kayan da ake amfani da su domin bunƙasa tattalin arziƙi kamar noma, kare kai kamar takobi da mashi da sauransu.

3.0      Tarihin Ƙasar Talata Mafara

 “Mafara Garken Haɗo Tamode Me Kamar Yau Sallah”

Akwai bayanai da yawa a game da tarihin asalin mutanen Mafara. Amma dai abu ne da babu saɓani ga malaman tarihi cewa, Mafarfari suna daga ƙabilar Zamfarawa. Su kuwa Zamfarawa suna daawar cewa su maguzawa ne, kuma mafarauta waɗanda suka samo asali daga Kano. Da suka baro Kano sun zauna a wani wuri da ake ce ma Dutse a kusa da garin Zurmi. Daga baya kuma suka gina Birnin Zamfara wanda ya faɗa hannun Gobirawa a bisa ga yaƙe-yaƙe.

 A game da kalmar Talata Mafara wadda take ita ce sunan garin an haɗa wannan ne a kan kalmomi guda biyu. Ɗayar ita ce Talata guda kuwa ita ce Mafara. Kalmar Talata sun ce tana da alaƙa da Kasuwar garin, domin kasuwar ta kasance tana ci ne, a ranar Talata kowane mako. Kuma mutane daga sassa daba-daban na cikin Najeriya da wajen ta suna kwararowa zuwa gare ta. Ɓangare na biyu na sunan, watau Mafara sun ce asalin kalmar ita ce Mafarau. Wannan suna kodai ya kasance suna ne na unguwar da suka taso daga gare ta a can Kano ko ya kasance suna ne na ƴaƴan wani sarkin nasu. Matanen Mafara kafin su zauna garin Talata Mafara sun zauna a wurare daban-daban daga cikinsu akwai Tsaraka. Wannan gari ana ganin muhallinsa na tsakanin tsohon garin Maradun da Ƙauran Namoda.

 

3.1      Sana’ar Ƙira a Garin Talata Mafara

 Talata Mafara Hausawa ne kamar sauran Hausawa su ma, ana aiwatar da wannan sana’ar ta ƙira tun gabanin zamani ya zo akwai masu gudanar da wannan sana’a kuma ita ce hanyar cin abincin su. Su yi aure, su haihu har su aurar babu mai jin asirinsu. Sana’ar ƙira a garin Talata Mafara kamar sauran garuruwan Hausawa su ma, suna da ire-iren maƙerai kashi biyu watau ƙirar fari, da ƙirar baƙi.

 To wai mice ce ƙira? Wannan tambaya an fuskantar da ita zuwa ga wani mai aiwatar da sana’ar inda ya bayyana cewa: “sana’ar ƙira wata abu ce wadda ake sarrafa ƙarfe domin ya bayar da maana, a samar da abin amfani kamar hauya, galma, kwashe, sungumi, da sauransu.” Tattaunawa da Altini Maƙerin Baƙi, (25-12-2022, 11:30am).

 Watau sana’ar ƙira sanaa ce da ake samun ƙarfe ko tama a sanya shi cikin wuta bayan ya yi ja, a fito da shi a ɗora a akan uwar maƙera a riƙa bugun sa har ya kasance abin da ake so ya kasance.

 Haka kuma wani maƙerin fari ga abin yake cewa: Ba wani abu ba ne ƙira face wasu hikimomi ne da ake amfani da su a sarrafa ƙarfe a mayar da shi wani abu na ado kamar azurfa, tagulla, ƴan kunne, sarƙa, ko kuma kayan adon doki kamar algaita, da likkafa, ƙaraurawa da sauransu. Tattaunawa da Ɗan barau maƙerin fari, (24-12-2022, 5:30pm).

 Bugu da ƙari ya bayyana cewa ita wannan sanaa ta ƙira a nan garin Talata Mafara tana da shugaba kamar sauran garuruwa, sarkinta kuwa shi ne Malam Yahaya amma ya rasu wata uku da suka shige.

Ya ƙara ba da haske cewa ƙirar fari ita ce ake kiran shugabanta da sarki amma ƙirar baƙi ana ce wa shugabanta mazuga.

 

3.2      Kira Jiya a Garin Talata Mafara

 Kamar yadda Altini maƙeri ya bayyana cewa Ƙira a jiya ana amfani ne da wasu kayan gudanar da sana’ar waɗanda a yau ko dai an daina amfani da su ko kuma an rage amfani da su. A jiya ana amfani da “tama” shi wannan wani dutsi ne da shi ake samar da kayan gudanar da ƙira kamar guduma da awartaki da mulgu, ana sanya shi cikin wuta bayan ya yi ja, sai a fiddo shi a riƙa bugun sa har a warwatse shi

 Shi kuma Jamilu maƙerin fari ya bayyana cewa: a lokacin kafin a sami dabarar yin amfani da gyare to zuga-zugi ne ake hura wuta da shi wanda kuma shi zuga-zugi ɗin nan ba kowa ba ne yake iya hura ma wuta da shi yadda ake buƙata face wanda ya gaji sanaar ko kuma wanda yake maƙwabcin maƙeri ne kuma yana zama akai-akai yana ganin yadda ake yi to, irin waɗannan suna iya hura ma wuta da shi.”

3.3      Kayan Gudanar da Ƙira

 Mafi yawan kayan da ake gudanar da ƙira a jiya duk da har yau ana samun wasu daga cikin su ana amafani da su, ba a daina ba irin waɗannan kaya sun haɗa da:

1)      Zuga-zugi: wani abu ne da ake yin shi da fatar awaki bayan an jeme fatar a sanya mata ƙota da ita ake hura wuta.

2)      Uwar maƙera: ƙarfe ne dunƙulalle ake kafewa a kan shi ake bugun karfen da ake son sarrafawa.

3)      Masaba: Abin bugun ƙarfe ce da ake yin ta da zallar ƙarfe.

4)      Awartaki ko Araftaki: Ƙarfe ne ake yin sa don ɗauko ƙarfe daga wuta.

5)      Majayi: Shi ne ake jawo gawayi da shi ana yinsa da rodi a yau.

6) Guduma: Ƙarfe ne ake yi masa ƙota. Da ita ake dukan ƙarfen da ake son ƙerawa bayan an ɗora shi a kan uwar maƙera.

7) Ƙarfe: Shi ake ƙerawa.

8) Gawayi: Shi ne makamashin wuta.

9) Tama: Sinadari ne da ake yin kayan aiki da shi.

10) Kasko: Ana zuba ruwa a ciki da wasu lokutan ake tsoma ƙarfen da ake son rage zafinsa.

11) Kurfi: Da shi ake sara ƙarfe.

12) Gizago: Ana sassaƙe ƙota da shi idan buƙatar hakan ta taso.

13) Matsoni: Da shi ake yin huda (ƙofa) a jikin ƙarfe.

14) Madashi: Da shi ake huda ƙota bayan an saka shi a wuta ya yi ja.

 

 3.4 Kayan Amfanin Al’umma da Sana’ar ke Samarwa

 A ɓangaran maƙeran baƙi suna samar da kayan amfani kamar irin su:

1)Hauya

2)Kwashe

3)Galma

4)Laushe

5)Maƙwarƙwasa

6)Takobi

7)Adda

8) Munjagara

9) Aska

10) Huƙa

 11) Gatari                                                                                                                 

 12)Magini. Da sauransu                                                                                               

 A ɓangaran maƙeran fari suna samar da kayan amfani kamar haka:

1)Sarƙa

2)Ƴan kunne

3)Ƴan hannu

4)Zobe

5)Algaita

6)Ƙaraurawa

7)Likkafa

8)Linzami. Da sauransu                                                                                                                

4.0 Tasirin Zamani A Kan Sana’ar Ƙira a Garin Talata Mafara

 Masu iya magana kan ce “ Zamani rigar doli a saka ki a huta” shi zamani riga ne idan ba a saka ba to, sai a ga mutum tsirara. A lokacin da ake tattaunawa da wani maƙeri wanda zamani ya yi tasirin a kansa da sana’ar da yake yi ta ƙira, ya bayyana cewa Yanzu ƙira ta sami sauye-sauye ta fuskar kayan gudanar da sanaar da kayan amfanin alumma da sana’ar take samarwa. Domin a halin yanzu ana ƙera tasa wadda ake niƙa ko malkaɗe da ita, da injimin niƙar shinkafa, injimin niƙar hatsi kamar gyero dawa, da injimin niƙar kara kamar karan dawa domin a ba shanu su sami abinci.” Tattaunawa da Muhammad Sani, (24-12-2022, 11:30am).

 Haka kuma Ɗan Barau ya bayyana cewa “Yanzu ci gaban da suka samu har ta kai yanzu ba sai sun yi amfani da gyare ba a wajen zuga kamar ma wani tsohon ya yi ne, saboda yanzu suna amfani da wutar lantarki da wasu kayayyaki da zamani ya zo da su sai su riƙa haɗawa domin su huta da samun mai yi musu hurin wuta yayin da suke gudanar da aikinsu.” Abubuwan da suke amfani da su sun haɗa da:

Ø  Fanka: Ita wannan fanka ta rediyo ce suna amfani da ita ta hanyar haɗa ta da wata waya sai a jona ga wuta sai ta zama a maimakon yaron da zai riƙa hura wuta idan ana aiki.

Ø  Sola: Ita sola tana zama maimakon wutar lantarki ne watau idan ba wuta suna amfani da ita ana laƙo ta ne a saman rufin ɗaki inda rana ke fuskantar ta.

Wannan dai yana nuna irin tasirin da zamani ya yi a kan sana’ar ƙira a garin Talata Mafara.

4.1 Ta Fuskar Kayan Gudanar Da Ƙira

 A ɗan binciken da aka gudanar an ga kayan gudanar da ƙira a yau sun haɗa da:

1)      Ƙarfe: Kafin a sami ƙarfe ana samar da kayan gudanar da sanaar da wani abu da ake kira tama shi wannan wani dutsi ne ake sarrafawa a samar da kayan aiki. Amma yanzu zamani ya zo da ƙarafa kamar rodi da sauransu, ma’ana yanzu kayan sun zama duk zalla ƙarfe ne.

2)      Gyare: Shi ma wani tasiri ne da zamani ya kawo shi domin kafin a san shi da zuga-zugi ake yi kamar yadda bayanin sa ya gabata tun a 3.1

3)      Wutar Lantarki: Wannan yana daga cikin tasirin da zamani ya yi kamar yadda aka bayyana a cikin 4.0

4)      Almakashi: Shi ma wannan yana daga cikin kayan da ake iya cewa zamani ya zo da shi a cikin sana’ar ƙira.

5)      Mawashi: Shi ma wani abu ne da maƙera suke amfani da shi domin wasa kayan da aka samar kamar wuƙa, takobi da sauransu.

6)      Durom-durom: Shi kuwa kamar yadda Muhammad Sani mai ƙirar zamani ya faɗa cewa suna sawo waɗannan durom-durom daga masu sayar da man juye da gas da kalanzir (kerosine), suna sarrafa su su samar da kayan amfanin al’umma kamar tasoshin niƙa da sauransu kamar yadda aka bayyana a cikin 4.0

7)      Filaya (plier): Ita ma wannan zamani ya zo da ita kafin a san filaya da awartaki ake amfani.

 

4.2 Ta Fuskar Kayan Amfanin Al’umma

 A yanzu an sami ƙari a kan kayan da ake samarwa domin a yau maƙeran zamanin nan suna da basirar ƙera wasu kayan amfanin alumma kamar irinsu:

1)      Kayan da ake sanyawa a wajen gine-gine kamar:

Gambuna da tagogi (windows), da kuma kayan aikin gini kamar baho, sheburi da sauransu.

2)      Injimoman niƙa

3)      Baruka kamar dogon baro da guntun baro

4)      Murahu

5)      Tukwanen ƙarfe

6)      Gadaje

7)      Kujeri na ƙarfe

8)      Tasoshi na suya kamar suyar ƙosai da sauransu.

9)      Tandodin ƙarfe domin gashin masa/waina.

 Bugu da ƙari a yau maƙeran fari suna ƙera zobba irin na samari da ‘yanmata masu ɗauke da sunaye, da sarƙoƙi masu kwalliya irin ta zamani.

Yanzu har ana zuwa a yi sarin irin waɗannan kaya a yi fatauncin su zuwa wasu wurare. Tattaunawa da Jamilu Maƙeri, (24-12-2022, 6:00pm).

 

5.0    Sakamakon Bincike

Sakamakon wannan bincike ga alama bai ci karo da hasashen binciken da aka bayyana a sama ba. Wannan muƙala ta ci nasarar gano wasu sauye sauye da sana’ar ƙira ta samu da suka haɗa da:

a.      Kayan gadanar da ƙira kamar filaya (plier) wadda kamar yadda aka sani ana amfani ne da awartaki.

b.      An gano cewa yanzu maƙera suna amfani da wutar lantarki ko sola ta hanyar haɗawa da wasu wayoyi da fankar rediyo a samar da iska.

c.       Bugu da ƙari an gano cewa yanzu maƙera suna yin aiki tare da masu walda ta zamani domin an ce in dambu ya yi yawa ba ya jin mai suna samar da kayan amfani kamar injimin niƙar hatsi da kujerin ƙarfe da sauransu.

d.     Haka kuma an gano yanzu ƙarfe ne zalla maƙera suke amfani da shi a maimakon tama wanda aka san cewa shi dutse ne.

5.1   Kammalawa                                                                                                        Kamar yadda aka gani sana’ar ƙira sana’a ce da take daɗaɗɗiya mai tsohon tarihi a ƙasar Hausa. Kuma hanya ce ta gwagwarmaya da faɗi-tashi da Hausawa suke nema domin samar wa kansu mafita daga wasu matsalolin rayuwa.

 

 

 

 

 Manazarta                                                                   

C.B.T.T.M. (2008). Talata Mafara Jiya Da Yau.

 Gusau, S. M., & wasu. (2012). Gusau Ta Malam Sambo.

 Century Research and Publishing Limited.

 Abuja Kano Kaduna Lagos Zariya. https://www.rumbunilimi.com.ng|

Yahaya, I. Y., (2007). Darussan Hausa, Don Manyan Makarantun Sakandare,

 Littafi Na Uku University Press Ibadan.

Zarruƙ, R. M., & wasu. (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don

 Makarantun Sakandare Littafi Na biyu.

 University Press Ibadan.

Tattaunawa da Altini Maƙerin Baƙi a Ranar 25/12/2022, a Garin Talata Mafara,

Ƙaramar Hakumar Jahar Zamfara Nageriya.

Tattaunawa da Ɗanbarau Maƙerin Fari a Ranar 24/ 12/2022, a Garin Talata Mafara, Ƙaramar Hukumar Zamfara Najeriya.

Tattaunawa da Jamilu Maƙeri a Ranar 24/12/2022, a Garin Talata Mafara,

Ƙaramar Hukumar Zamfara Najeriya.

Tattaunawa da Muhammad Sani a Ranar 24/12/2022, a Garin Talata Mafara,

Ƙaramar Hukumar Jahar Zamfara Najeriya.

Post a Comment

0 Comments