Ticker

6/recent/ticker-posts

Kashi Ya Game A Sake Rabawa: Gambizar Gargajiya, Addini Da Zamananci A Bukukuwan Hausawa A Yau (Keɓaɓen Nazari Kan Bukukuwan Suna A Garin Dutsin-Ma)

Muƙalar da aka gabatar a ajin ALH 400 (Seminar), a Sashen Harsuna da Al’adu, Jami’ar Tarayya, Gusau, Jahar Zamfara, Nijeriya, (Disamba 2022 - Janairu, 2023).

 

Muhammad Yahaya

Lambar G.S.M 08100073485
Kibɗau:mydarawa@gmail.com 

Tsakure

Wannan aiki ne, da ya kalli yadda zamananci ya yi tasiri a cikin al’adun bukukuwan suna gargajiyanci da addini a garin Dutsin-ma. Don haka dalilin gudanar da wannan binciken don gano tasirin da zamananci a cikin bukukuwan sunan Hausawa tare da fito da shi fili ƙarara. Sannan ayayin gudanar da wannan binciken an yi anfani da nagartattun hanyoyi kamar haka, hanya ta farko bitar ayyuka masu alaƙa da wannan binciken, hanya ta biyu ziyartar ɗakunan karatun jami’o’i da kwalejoji don duba bugagun littatafai masu alaƙa da wannan aikin, hanya ta uku tattaunawa da wasu mata waɗanda suke da ido a waɗannan baƙin al’adun. Hausawa kance zamani riga ne, inji masu iya magana. Don haka wannan muƙala zata duba tasirin da baƙin al’adu suka yi a cikin bukukuwan suna a garin Dutsin-ma.

1.0    Gabatarwa

 Haihuwa na ɗaya daga cikin manya-manyan ginshiƙan dalilan yin aure a cikin al’ummur Hausawa. Duk da yake lamarin haihuwa lamari ne da ya bambanta daga wannnan al’ummu zuwa waccen. Domin wasu al’ummu ba su buƙatar haihuwa kamar yadda wasu suke da ita. A ƙasar Hausa ɗa (mace ko namiji) baiwa  ce da kowa ke burin ya samu. A al’ada, yaro ko ba kai ka haife shi ba muddin ka girme shi zai yi maka ladabi(C.N.H.N.1981:16) Wannan ya nuna ‘ya’ya suna da muhimmancin a cikin al’ummar Hausawa.

A al’adance, a duk lokacin da aka sami ƙaruwa ta haihuwa a ƙasar Hausa, ana aiwatar da wasu al’adu waɗanda ke nuna murna ko farin cikin ƙaruwar da aka samu. Don haka,wannan muƙala za ta yi ƙoƙarin nazarin wasu daga cikin al’adun da zamananci ya yi tasiri a cikin su wajen bukukuwan suna a garin dutsin-ma.

Bisa wannan dalili ne muƙalar za ta yi ƙoƙarin kawo irin yadda zamananci ya yi tasiri a cikin al’adun haihuwar Bahaushe a yanzu. Ma’ana,  za ta dubi yadda nason baƙin al’adun haihuwa na Bahaushe. A ƙarshe muƙalar ta yi ƙoƙarin yadda za a tsare a kuma inganta waɗannan al’adu musamman a cikin al’ummar Hausawa domin muhimmancinsu.

1.1 Ra’in bincike

Wannan bincike an dorashi a kan ra’in adana al’adu da ci gaban al’umma (cultural sustainability theory) Wannan ra’in ne mai yin bayani kan hanyoyin adana ko inganta al’ada domin ci gaban al’umma (cultural sustainability) A cewar Abdurraman Ado a cikin littafinsa na ra’o’in bincike kan Al’adun Hausawa ya bayyana: Gasau (2015) ya kira makarantar da ta fito da irin wannan ra’i da suna ‘Mazahabar Adana al’adu. Shi kuwa Shaibu (2013:78) ya kira makarantar da ke da da’awar irin wannan ra’i na adana al’adu da sunan’’Mazahabar Muhafaza”.

 

2.0 Dabarun Gudanar Da Bincike

A ya yin gudanar da wannan binciken an yi amfani da muhimman hanyoyin gudanar da bincike kamar haka:

1.      Bitar ayyuka masu alaƙa da wannan aiki.

2.      Ziyartar ɗakunan karatun jami’o’i da kwalejoji da duba ayyuka masu alaƙa da wannan.

3.      Tattaunawa da wasu daga cikin mata waɗanda idon su ya kai ga baƙin al’adun.

2.1 Bitar ayyukan da suka gabata kan ma`anonin Al`ada

Masana da manazarta sun ba da bayanai da dama kan ma`anar al`ada kamar haka:

 Bunza (2007) Ya bayya na ma`anar al`ada da cewa: Al`ada tana nufin dukkanin rayuwar ɗanAdam ce tun daga haihuwa har zuwa ƙabari.

Ɗangambo (1984) Ya bayyana cewa: Al`ada it ace abar da aka saba yi yau da gobe.

Umar (1987) Wanda ya bayyana ma`anar al`ada da cewe: Al`ada itace, sababbiyar hanyar rayuwa wadda akasarin jama`a na cikin al`umma suka amince da ita.

2.2 Tarihin Dutsin-Ma

    Takaitacce tarihin garin dutsin-ma, sunan dutsin-ma ya samo asali ne daga sunan mafaraucin da ke rayuwa a kan babban dutsen da ke tsakiyar garin shekaru da dama da suka gabata, sunansa’’MA’’kuma dutsin yana nufin (Dutsi) a harshen Hausa, sai mutane suka fara kiran dutsin a matsayin Dutsin-ma, sai mutane suka fara zuwa suna za ma a kusa da dutsen da kewaye saboda samun ruwa. Dutsin-ma ta za ma karamar hukuma a shekarar (1976). Shugaban karamar hukuma ne a hukumance. Mazaunan karamar hukumar galibi Hausawa ne da Fulani a kabila. Babbar sana’ar su ita ce noma da kiwo da noma rani. Dutsin-ma karamar hukuma ce dake cikin jahar katsina, Nijeriya.

2.3 Ma`Anar Haihuwa

       A cewar masana da manazarta da dama sun bada ma`anar haihuwa daban-daban daga ciki su akwai:

Idi (2016) Ya bada ma`anar haihuwa da cewa yanayi ne da mata mutane ko dabbobi suke yi sakamakon saduwa daga jinsin mace da namiji wanda daga karshe kan bada samun ɗa ko ɗiya.

Haruna (2016), Haihuwa abu ce wadda ta kunshi halitta daban-daban domin haihuwa yana yi ne na samun karuwar zuri`a ta hanyar saduwa tsakanin namiji da mace sakamakon aure ko wata hanyar. Mace kan ɗauki ciki a tsawon wata tara (9) ko fiye da haka wanda daga bisani za ta haifi abun da ke cikin ta.

Umar (2015) Haihuwa abuce wadda hallitu ke yi sakamakon saduwar jinsi biyu. Ana tunanin haihuwa kan fara ne sakamakon samun ciki wanda yake farawa daga wata ɗaya har zuwa wata tara, haka kuma sukan wuce wannan lokacin. Haihuwa kan za mo abun farin ciki ko abun damuwa a wani lokaci wannan ya ta`allaka ne da yadda haihuwar ta kasance.

Idan muka dubi waɗannan bayanai na malamai zamu iya cewa haihuwa ba sabon abu ba ce ga dukkan abinda yake da rai bisa bayan ƙasa, idan dai za su haɗu jinsi biyu to ana sa ran su samu haihuwa.

2.4 Ire-Iren Haihuwa

Haihuwa takan kasance iri-iri ko kuma nau`o`i daban-daban ta hanyoyi da dama kamar haka:

        i.            Haihuwar Wabi

      ii.            Haihuwar Ƙalau

    iii.            Haihuwar Arziƙi

    iv.            Haihuwar Rurrutsa

      v.            Haihuwar Keke

Ga bayanan waɗannan nau`o`in haihuwar ɗaya bayan ɗaya kamar haka:

1. Haihuwar Wabi: Haihuwa ce wadda wasu mata kan samu jarabawa ta ubangiji mace zata dunga haihuwa amma ɗiyan basa tsayawa sai su dinga mutuwa.

2. Haihuwar Ƙalau: Haihuwa ce da mace za ta haihu idan lokacin haihuwar ta ya yi ba tare da ta sha wata wahala ba ko kiran ma`aikatan lafiya ko zuwa asibiti ko wani tsaiko, To irin wannan haihuwa ita ake ce ma haihuwa ƙalau.

3. Haihuwar Arziƙi: Wannan haihuwa kuwa ita ce mace kanyi kafin lokacin haihuwar yayi,wato shi ne ta yi ɓari ko ta haifi ɗan wata bita ko takwas,ko kuma muce duk haihuwar da aka yi ɗa bai zo da rai ba,to ana danganta ta da haihuwar arziki, yan uwa da abokan arziƙi sukan je su yi ma mace jaje tare da fatar samun lafiya da ɗa rayyaye.

4. Haihuwar Rurrutsa: Wannan haihuwa ce wadda ake samun ɗa ko ɗiya kafin wani lokaci ko kafin a ya ye yaro an sami wani ciki, wata mata ta kan cigaba da ba yaron nono har sai ya kai lokacin da za ta ya ye yaron.

5. Haihuwar Keke: Haihuwa ce wadda Allah yakan ba mutun kamar shi ya tsara ta da kansa, ita wannan haihuwa takan faru ne ga mace bisa ƙaddarawar Ubangiji, za ka ga mace ta haifi ɗa namiji idan za ta kara haihuwa ta biyu sai ta haifi ɗiya mace, haihuwa ta uku ɗa namijita hudu ɗiya mace haka za ta yi ta haihuwa har ta gama haihuwarta. Wannan shi ne bayanin nau`o’in haihuwa a taƙaice.

2.5 Masu Haihuwa

Masu haihuwa su ne jinsin mata waɗanda Allah ya halitta da ɗabi’ar haihuwa. Masu haihuwa kuwa sun haɗa da mutane da dabbobi da tsuntsaye da ƙwari waɗanda ke ɗaukar ciki kuma su haihu.

2.6 Kayan Haihuwa

Kayan haihuwa kaya ne da mai haihuwa ke amfani da su bayan ta haihu, waɗannan kayan sun ta’alaƙa ne daga yanayi al’adar gari ko unguwa ko kuma jinsin mutane. kayan haihuwa ga su kamar haka:

                                i.            Atamfa

                              ii.            Hijabi

                            iii.            Kayan jarirai

                            iv.            Kayan yaji

                              v.            Kayan ƙauri

                            vi.            Akwati

                          vii.            Kayan dauri

                        viii.            Turare

                            ix.            Kayan shafe-shfe

                              x.            Takalmi

                            xi.            Yankune

                          xii.              Sarƙa

                        xiii.            Kayan wanka

                        xiv.            Gyale

                          xv.            Kayan wanki da sauransu.

Abdullahi, Hannatu da Jamila (2021) duk sun amince da haka a cikin kundin binciken da suka gabatar a (F.E.T) Gusau.

2.7 Kayan Karɓar Haihuwa Jiya Da Yau

Kayan karɓar haihuwa na da sun sha bamban da na yanzu, domin kuwa akwai bambance-bambance a tsakanin na da da na yanzu. Gasu kamar haka:

1. Kayan Karɓar Haihuwa A Jiya

Gasu kamar haka:

a) Tukunyar ƙasa ta dafa ruwan zafi   

b) Toka wato (sabulun salo)

c) Alkajiya      

d) Fallen zane

e) Tukunyar dauri wadda ake dafa magani

f) Kwatarni

g) Kujera wadda mai jego ke yin wankan sabara

2. Kayan Karbar Haihuwa A Ayu.

Gasu kamar haka:

a) Reza ko Almakashi 

b) Sabulun wanka

c) Robar wanka

d) Lalle

e) Sabili detol

f) Manzaitun

g) Rigar yaro

i) Tukunyar da fa ruwa

j) Safar hannu

k) Omo

 l) Tawul

 m) Ruwan wanke yaro (Baby oil)

 n) Ruwan kasha kwayoyin cuta (detol)

i) Auduga da filista

3.0 Ma’anar Biki

Biki wani taro ne na mutane da suke shiryawa, su gudanar don nuna farin cikin su a kan wata baiwa da Allah ya yi ma wani daga cikin su ko ya yi wa wasu. Ga al’adar Bahaushe ya na yin biki ne don ya nuna farin cikin sa tare da murna da annanshuwa a kan wata baiwa da Allah muhallicin sarki ya yi masa.

Bukukuwa suna daga cikin fitattun al’adun Hausawa, waɗanda suka sami asali tun kaka da kakanni. Biki ana yin sa don nuna farin ciki da ake da shi ga wani abin farin ciki da ya faru, ko don tunawa da wani abu muhimmin ko don zagayowar wata.

Ire-iren bukukuwa

  Kamar yadda zamu gani bukukuwa sun kasu kashi-kashi kamar haka:

a)      Bikin Aure

b)      Bikin Haihuwa

c)      Bikin suna

d)      Bikin kalankuwa

e)      Bikin nadin sarauta

f)       Bikin sallah babba

g)      Bikin sallah ƙarama da sauran su.

3.2 Ma’anar Bikin Suna

 Hausawa kan ce, suna linzami ne sai mai shi ke amsawa.

    Bikin suna: Biki ne wanda ake gudanar da shi ga abinda aka Haifa, bayan mako ɗaya da haihuwarsa.

  3.3   Yadda Ake Yin Bikin Suna

    Bikin suna dai kamar yadda bayani ya gabata ana yin sa bayan kwana bakwai da haihuwa. Akan bawa yaro ko yarinyar da aka haifa suna kwana bakwai da haihuwa, kafin ranar bukin kamar yadda maudaci da wasu (1998) suka ce, baban jariri ko jaririya zai sayi goro ko dabino, zai raba goron ko dabinon a matsayin gayyata ga ‘yan uwa da abokan arziki zuwa wajen bukin suna amma a wasu wurare za a raba goron ko dabinon ne kawai ranar bukin suna.

    

3.4 Bikin Suna A Addinance

     Bikin suna shi ne, taron jama’a da aka yi shi bisa sunnar manzon Allah Annabi muhammadu (SAW), ta hanyar shirya walima ga jama’a kamar yadda shari’a ta amince batare da anyi wata bidi’a ko sanya ra’ayi a wajen gudanar da bikin suna a addinancen ba.

3.5 Bikin Suna A Gargajiyance

   Bikin suna a gargajiyace shi ne, taron jama’a wanda aka shirya, kuma aka kira Makaɗa da mawaƙa su cashe, a nuna izza da isa da al’ada ƙarara, to shi ake kira da bikin suna a gargajiyance.

4.0 Tasirin Zamananci A Kan Sauye-Sauyen Da Aka Samu Wajen Bikin Sunan Hausawa A Garin Dutsin-Ma.

   Hausawa kan ce zamani riga ce, inji masu iya Magana.shi zamani lokaci ne wanda ke yiwa kowa dai-dai, sai dai wanda ba sanya ba. A wannan aiki zamu dubi tasiri ko sauye- sauyen da zamani ya kawo a cikin bukukuwan sunan Hausawa musamman a cikin garin Dutsin-ma. Kasancewar zamani ya kawo sauye-sauye masu tarin yawa a cikin bukukuwan sunan Bahaushe inda har waɗannan sauye-sauyen suke ƙoƙarin kore al’adunsa na gargajiya da ya gada tun kaka da kakanni.

 Waɗansu daga cikin baƙin al’adun da zamani ya kawo a cikin bukukuwan sunan gargajiya na Bahaushe sun hada da:

a)      Ɗakin Taro(Hall): A da taron bikin suna taro ne da ake gudanar da shi a gidan mai jego. Amma yanzu sakamakon zuwan zamani ya sanya taron bikin suna ana gudanar da shi a ɗakunan taro domin haɗuwa don gudanar da taron inda ya haɗa da dangin miji da na maijego da ‘yan uwa da abokan arziƙi a ci a sha don taya murna a kan abin da ka haifa da kuma mai jego.

 b) Walima: Wannan ma wata sabuwar al’ada ce, wadda ake gudanar da ita wajen bikin suna wadda ake tara mata da ƙananan yara a kira malamai mata don gudanar da nasihohi da wa’azoji domin nuna farin ciki a kan ƙaruwar da aka samu da ta ya iyayen jariri ko jaririya murna.

c) Anko: Anko ma wata sabuwar al’ada ce, ga al’ummar Hausawa a wajen bikin suna, wanda wannan al’adar ta wasu ƙabilu ce amma bahaushe ya ɗauka ya yi uwa makarɓiya ya sanya ta a cikin al’adunsa na yau da kullun, wanda harma ya sanya yanzu mafi a kasari duk inda ake gudanar da bikin suna zaka tarar ana yin anko, maijego ita ce take zaɓen irin kalar atamfar ko kuma zanen da za a gudanar da anko da shi inda miji da mssata tare da ‘ya’yansu da kuma abokan arziƙi duk zasu gudanar da ankon.

d) D.J: Al’ada kaɗe-kaɗe da raye-raye da waƙe-waƙe, a bikin suna ba baƙuwar  al’ada ce, tun iyaye da kakanni ake aiwatar da ita. Amma sakamakon zuwan zamani ya  sanya an samu wata baƙuwar al’ada ta D. J wanda yanzu mafi a kasari duk inda ake gudanar da bikin suna zaka tarar maijego ta ɗauko mai D. J domin a saka waƙa a na rawa don taya murna akan ƙaruwar da aka samu wajen bikin suna.

e) Majalisi: kamar yadda muka sani majalisi wata sabuwar al’ada ce wadda da  ba a sanda ita ba a cikin al’adun bahaushe amma sakamakon zuwan larabawa ta samu. Sannan kuma wannan al’ada ta majalisi wasu mutane ne masu gudanar da bege ko ƙasida ko kuma ‘yanmandiri sune suke gudanar da majalisi. Anan ma wannan al’ada ana gudanar da ita ne waje bikin suna inda za a tara mata da ƙananan yara domin a kira masu bege ko ƙasidu ko kuma ‘yanmandiri domin nuna farin cikin su a kan abin da aka samu.

f) Shan shayi: Al’adar shan shayi al’ada ce, sabuwa a garin Dutsin-ma wadda wannan al’adar ana gudanar da ita ne daren suna a gidan da aka samu ƙaruwa domin yin hira kuma ana shan shayi inda za a tattara kuɗi ga wanda Allah ya horemawa sai a je a haɗo kayan shayi, manya maza da ƙananan yara maza da mata duk suna gudanar da ita.

g) Fati na zanen suna (Namming party): fati na zanen suna wannan wani biki ne da yannan jariri ko jaririya ke shiryawa tare da gudummuwar uwaye za’a rarraba minti da biskit ga kawaye da abokannai na gayyata wajen bikin da zarar ranar da aka ayyana ta zo.

Kuma wani lokaci wasu ma’aurata sukanyi anko, wato sutura iri ɗaya, wannan wani nau’in sutura ne ko yadi da zamani ya zo dashi wanda masu bikin ke shiryawa domin yin amfani da shi a lokacin bikin aure ko suna. Galibi mai jego ita ce ke shirya wannan irin suturar da za’a yi amfani da ita lokacin bikin aure ko suna, saboda nuna murnar su ga abinda aka Haifa, domin yin godiya ga Ubangiji Allah. kuma takan umarci dukkan ‘ya’yanta da ‘yan uwa da abokan arziki da su ɗinka irin wannan atamfar, domin fita iri ɗaya a ranar bikin sunan sai ka ga duk mutanen da suka halarci wannan taron bikin sunan su zama iri daya.

 h. Fati na cikar shekara (Birth Day party): Tabbas, shigowar addinin musulunci a ƙasar Hausa shi ne mabuɗin samuwar ilimin karatu da rubutu ga Bahaushe. Duk da samuwar karatu da rubutu ga Bahaushe bai sa ya fara rubutawa da adana sunayen ‘ya’yansa da ya haifa ba.

 Amma bayan shigowar wani zamani na Turawa mulkin mallaka, Bahaushe ya fara rubuta wa da adana duk wani abu da ya rubuta kamar sunansa da na ‘ya’yansa. Ganin yadda Turawa suke fatin cika shekara ya ba Bahaushe damar shi ma ya kwaikwaya a wajen Bahaushe da tunaninsa na lissafin shekarunsa na haihuwa ko na wani abu, ya ta’allaka ne a lokacin faruwar wani abu.misali:

       Idan ka tambayi Bahaushe lokacin da aka haife shi to, amsar da zai bayar ita ce zamanin sarki wane ko kuma ya ce lokacin muda (wata irin yunwa ce da aka taɓa yi a ƙasar Hausa), ko kuma yace a lokacin shugaba wane, amma yanzu zamani ya kawo sauyi a inda ake rubutawa a cikin litattafai ko a katin asibiti, ko a wuni wuri ba tare da an manta ba.

     Wasu daga cikin Hausawa yanzu suna yin wannan biki, don tunawa da irin waɗannan ranaku.A yi shagali sosai, a sheke aya, a yi kallace-kallace na finafinain Hausa da na Turawa a wajen irin wannan bikin ne ake yin abubuwa da dama na nishaɗi da nishaɗantarwa. Galibi kuma mai jegoce ta ke shirya irin wannan biki domin taya ta murnar cikar sheka ga abin da ta Haifa.

i.Naɗar Hotunan Suna (Naming Pictures): Wannan ma wata baƙuwar al’ada ce wadda bahaushe ke gudanar da ita sakamakon zuwan turawa ƙasar hausa wannan al’ada ta ɗaukar hoto wajen bikin suna tana da ɗa yaɗuwa a cikin hausawa. Da bahaushe baisan wata al’ada ta daukar hoto ba sai da turawa suka shigo ƙasar wanda ya sanya yanzu duk inda ake bikin suna zaka tarar ana ɗaukar hotuna ta wayar salula ko kuma a yi ammafani na’urar ɗaukar hoto (camera). Ba dan wani abu ba  sai dan  tarihi.

4.1 Muhimmancin Biki Ga Rayuwar Al’umma

Kowace al’umma tana da al’adunta da take alfahari da su, kuma takan so a yi magana a kansu. Al’ummar Hausawa mutane ne masu ƙaunar juna da mutunta juna da kuma gayyatar juna, domin a taru waje ɗaya a yi wa juna murna da nuna farin ciki a kan abin alheri ko na baƙin ciki da ya samu.

  Ga kaɗan da ga cikin muhimmancin biki ga rayuwar al’umma.

                                i.            Yana haɗa aure tsakanin saurayi da budurwa.

                              ii.            Yana sa a sabunta tufafi da yin tsafta, da kuma wadatuwa da abinci.

                            iii.            Yana sanya jindaɗin rayuwa da ɗebe kewa.

                            iv.            Yana sanya raha da annashuwa, da kuma watsuwar harshe da cigaban al’ada.

                              v.            Yana sanya alheri ga ‘yan gida da kuma baƙi.

                            vi.            Yana haɗa kan jama’a da ƙaunar juna, da sanya zumunci.

                          vii.             

             4.2 Sakamakon Bincike

  Sakamakon wannan bincike ya gano cewa akwai baƙin al’adu masu tarin yawa da zamani ya kawo a cikin bukukuwan sunan Hausawa na gargajiya kamar yadda suka gabata a sama waɗannan baƙin al’adu sun haɗa da:

a) Kama ɗakunan taro don gudanar da taron bikin suna koma bayan da ana gudanar da shi a gidan maijego.

b) Haka nan kuma Sakamakon wannan bincike an gano wata sabuwar al’ada ta shan shayi wadda ake gudanar da ita gidan da aka haihu, ita wannan al’ada daren suna ake aiwatar da ita.Wasu suna yin ta don yin hira na ɗan lokaci wasu kuma har kwana suke yi daga cikin masu gudanar da wannan al’ada sun haɗa da yara maza da mata da kuma maza manya.

c) Sannan kuma a sakamakon binciken an samu wata baƙuwar al’ada ta D J wadda a da makaɗa da mawaƙa ne ake kira domin kaɗe-kaɗe da raye-raye amma sakamakon zuwan wannan al’ada ta sanya yanzu mafi a kasari duk inda aka haihu waje bikin suna ana aiwatar da wannan al’ada ta D J.

d) Daga cikin sakamakon wannan bincike an gano wata sabuwar al’ada ta bikin zagayowar ranar haihuwa (Birth day) ita wannan al’ada turawa aka sani da ita amma yanzu Bahaushe ya yi uwa makarɓiya ya rike ta kacokam abun yi.

               5.0 Kammalawa

Al’amarin haihuwa, al’amari ne mai matuƙar muhimmanci a wurin al’ummar Hausawa. Hasali ma, haihuwa ita ce ƙashin bayan yawaitar ko wacce al’umma a duniya. Shi kuwa lamarin haihuwa yana samuwa ne sanadiyyar yin aure a tsakanin namiji da mace. Buƙatar wannan haihuwa ya sa al’ummar Hausawa ta ba wa aure muhimmanci domin samun haihuwa.

A wannan muƙala an yi ƙoƙarin nazarin ma’anar al’ada da kuma ma’anar haihuwa da ire-iren haihuwa da bikin suna da ma’anar bikin suna da taƙaitaccen tarihi garin dutsin-ma da sauransu.

Manazarta

Ahmad, A. (2016), Jiya Ba Yau Ba, Sauye-Sauye A Cikin Bukukuwan Hausawa:                       

Bikin Aure A garin katsina,Argungun Jounal of Language Studies       (AJOLAS), Adamu Augie College of Education, Argugu Nigeria.

 

                Bunza, A.M. (2014), “In Baka san Gari Ba Saurari Daka:

                          Muryar Nazari Cikin Tafashen Gambo’’ Elkods printing Hause, Cairo

                

                Bunza, A.M. (2006) Gadon Feɗe Al’ada.Lagas:Tiwal Nigeria ltd, 16, Akinbaruwa

                           street,off Atunrase stteet surulere.

                  

               Hauwa’u, M.A.B,(2012), Goyon Ciki Jiya Da Yau, B.A.

                          Hausa, Dissatation, Ahmadu Bello University, Zaria.

 

               Maudaci I. da Wasu (1968), Hausa Custom Zaria: Northern Publishing Company.

 

 

             Tattaunawa da Malama Zainab Ranar 19/12/2022, a Garin Dutsin-ma.

             Ƙaramar hukumar Dutsin-ma Jahar Katsina.

             Tattaunawa da Baba yaha mai ɗanwake Ranar 22/12/2022, a Ɗarawa, Dutsin-ma Jahar 

 Katsina.

Post a Comment

0 Comments