Muƙalar da aka gabatar a ajin ALH 400 (Seminar), a Sashen Harsuna da Al’adu, Jami’ar Tarayya, Gusau, Jahar Zamfara, Nijeriya, (Disamba 2022 - Janairu, 2023).
Nazari A Kan Wasan Kwaikwayon Duniya Makaranta Na Gidan Rediyon Jihar Zamfara
ZAINAB ABDULƘADIR
08032901257
TSAKURE
Wannan muƙala ta yi nazari ne a kan wasan kwaikwayon “Duniya Makaranta” na gidan rediyon Jihar Zamfara. Kamar yadda masu iya magana ke cewa “Duniya makaranta” ta fara ne tun daga ranar da mutum ya faɗo duniya har zuwa komawarsa ga ubangijinsa, tana ɗauke da dukkan gwagwarmayar da ɗan’Adam kan yi a rayuwarsa ta yau-da-kullum na farin ciki ko baƙin ciki, yakan zamo darasi ga ɗan’Adam don taimaka ma kanshi gobe. Wannan muƙala ta yi nazari ne a kan wasu sigogin wasan da muhimmancinta, matsaloli da kuma hanyoyin warware matsala.
1.0 Gabatarwa
Wasan kwaikwayo na Hausa, fage ne da ya taɓo dukkan harkokin da suka shafi rayuwar ɗan’Adam ta yau da kullum, domin yana bayyana wa mai kallo ko mai sauraro ko karatu, hanyoyin rayuwar jama’a ta fuskar sana’o’insu. Masana adabin Hausa da suka yi nazari akan wasan kwaikwayo sun yi ƙoƙari sun fito da ma’anar wasan kwaikwayo.
Ɗangambo (1984) ya ce “Wasa ne da ake ginashi don kwaikwayon wani labari ko wata matsala ta rayuwar da ake son nusarwa ga jama’a cikin sifar yaƙini ko kuma a rubutashi”.
Yahaya, (1978) ya bayyana wasan kwaikwayo da cewa; “Wasan
kwaikwayon na nuni ne da aikata wani abu musamman a dandali domin yasa nishaɗi ga masu kallo ko
ya raunanar masu da zuciya”.
Rediyo na ɗaya daga cikin hanyoyin sadarwa na zamani da ake amfani dasu domin faɗakarwa da ilmantarwa ga jama’a akan wasu manufofi na gwamnati ko wata sabuwar halayar rayuwar al’umma da ta shigo kuma take wanzuwa a cikin ƙasa. Ta hanyar rediyo ake shirya wasanin kwaikwayo daban-daban domin wayar da kan jama’a, a ciki kuwa har da wasan “Duniya Makaranta” da ake gudanarwa a gidan rediyon Jihar Zamfara.
Umar, (2012), ya ruwaito faɗar Welmeit (2006:1196) da yake cewa: “Rediyo kaface ta isar da saƙonni ga jama’a waɗanda ke zaune wurare daban-daban ba tare da ganin mai ba da saƙon kai tsaye ba”.
Oxford Dictionary (1995), ya bayyana “ma’anar rediyo da
shiraruwa ne na yaɗa labarai, zuwa ga masu sauraro waɗanda suka haɗa da jawo ra’ayin
jama’a da kuma wasanin gida da waje”.
Wasan kwaikwayo shi ne wasan da ake shiryashi domin kwaikwayon halayen mutane ko dabbobi ko aljannu da nufin anunama jama’a su ilmantu ko su wa’azantu ko su gargaɗu ko kuma su samu nishaɗi. Abin nufi shi ne duk wasan da aka yi koyi da halayen kuma aka nunama jama’a to shi ne wasan kwaikwayo.
Chinwieze (1976) ya ce; “Wasan kwaikwayo wani ɓangaren adabi ne da ke samar da aikin shaƙatawa ta yin sojan gona kamar kamanci a aikace ko a magance ko a rubuce kuma a wasance”.
Duniya Makaranta
Idan aka kalli waɗannan kalmomi guda biyu, wato “Duniya” da “Makaranta” za a ga cewa suna ƙunshe da ma’anoni daban-daban kamar haka; Kamar yadda bincike ya nuna cewa; kalmar Duniya tana nufin faɗin ta baki ɗaya, wanda ya ƙunshi doron ƙasa da sararin samaniya da kuma dukkan halittun da ke ciki, waɗanda Allah a cikin ikonsa ya halitta. Makaranta kuma tana nufin wuri ne da ake koyo da koyarwa, wuri ne na ɗaukar ilimin fannona daban-daban domin ƙaruwa ga ɗan’Adam.
Muhallin Bincike
Magaji (2004), Muhalli shi ne wurin da mutum ya kan
tanada domin fakewa da kuma samun kariya daga abubuwan da za su iya cutar da
shi.
Gidan Rediyon Jihar Zamfara shi ne muhallin binciken mu, yana nan kusa ga sabuwar kasuwa da ke Gusau daga yamma, yana da ofisoshi na bene wanda ake gudanar da ayyuka daban-daban na jama’a.
Dabarun Bincike:
Wannan muƙala ta kammala ne ta hanyar hira da masu gudanar da wasar domin jin ta bakinsu game da yadda suke gabatar da wasan, sannan kuma an yi amfani da kallo ko lura. Haka kuma an nazarci littattafai irin littattafan wasan kwaikwayo daban-daban domin zasu taimaka, haka kuma da amfani da kundayen digiri waɗanda za su yi mana jagoranci game da bincikenmu.
Kafurwar Gidan Rediyon Jihar Zamfara:
Gidan Rediyon Jihar Zamfara, asalinsa daga Rima rediyo ne
na Jihar Sakkwato. An ƙirƙiro Jihar Zamfara a shekarar (1996) sai aka samar da
gidan rediyo a Jihar Zamfara. A inda aka naɗa mata manajan
farko Injiniya Mamman Maru, wanda ya mayar da tashar zuwa babban zango da ake
kira (am), sai Alh. Garba Tunau Mafara a (2004), Gidan Rediyon Jihar Zamfara ya
fara shirye-shirye a matsayin tasha mai ƙaramin zango (FM) a
(1996) a shekarar (1997) ya soma aiki daga ƙarfe 5:15 na safiya zuwa 11:00 na dare.
Gidan Rediyon Jihar Zamfara ya fara watsa
shirye-shiryensa a zamanin gwamnatin Kanar Jibril Bala Yakubu, gwamnatin farko
ta soja a Jihar Zamfara. Haka kuma wannan gidan rediyon na da na’urori masu
gajeren zango na 567khz.
Yadda ake Gudanar da Wasan Duniya Makaranta a Taƙaice
Akwai matakai da dama da ake bi wajen gudanar da wasan,
waɗannan matakai ga su kamar haka:
a.
Akan me
za a yi wasan?
Kafin su fara wasan ‘yan wasan su kan zauna ne su tattauna akan me za a gabatar da wasan, idan akan siyasa ne ko lafiya ko tattalin arziki ko zamantakewa ta harkokin yau da kullum, sai aƙirƙira ma wasan suna ta hanyar tattaunawa.
b.
Jigon
Wasa:
Bayan an fito da jigon wasan ne da sunan da za a sakama wasan ne to, sai a fito da jigon wasan watau saƙon da wasan ke isarwa. Daga nan sai mutane da zasu gudanar da wasan. Daga ƙarshe kafin a gudanar da wasan ana buƙatar a yi bitar wasar kafin a gabatar da wasan.
Wasu daga cikin Jigogin Wasan
Ga wasu daga jigogin wasan kamar haka:
1. Wasan zafin Nema: Wannan wasa na nuni ne ga illar jahilci ga rayuwar mutum, da kuma nuni akan illar watsi da sana’a.
A wannan wasa an nuna Mirsisi ya yi jahilci a inda yake ɗaukar cewa keƙƙega ya samu kuɗi don haka shi ma ta kowacehanya sai ya yi kuɗi saboda jahilci, sannan kuma an yi faɗakarwa game da sana’a a inda ake nuna cewa Mirsisi ya yi watsi da sana’arsa saboda raina sana’arsa da ya yi don yana ganin cewa ba ta kawo kuɗi da wuri.
A taƙaice wannan wasa ta
zafin nema tana faɗakarwa ne akan cewa kada mutum ya ce shi sai ya yi kuɗi sannan kuma kada
mutum ya yi watsi da sana’arsa ko kuma ka da ya raina sana’arsa.
2. Wasan Gyara Kayanka – Wannan wasa ta gyara kayanka ta nuna irin yadda direbobi ke tuƙi kan hanya ba bisa ƙa’ida ba, da yadda hakan ke haifar da matsaloli a cikin al’umma har ma da rashe-rashen rayukka. Sannan kuma an nuna yadda ‘yan (Road Safety) masu kula da hanya ke yi wa al’umma matuƙa mota cin zarafi, domin kuma mutanen da ke bin doka yawanci su suke tarewa akan hanya.
A wannan wasa dai an fito da laifin kowanne daga cikinsu
wanda kuma daga ƙarshe kowa ya gyara halinsa.
3. Wasan ƙarya Fure Take: A wannan wasa ta ƙarya fure take, an yi nuni da illar rashin gaskiya da kuma muhimmancin amana. A nan an nuna yadda mirsisi da albasa suka tsaya akan sai sun haɗa tantabara da wanda ba ta so, kuma ba tare da shawarar mai riƙon tantabara ba, wato ƙeƙƙega mijin albasa.
Shi kuma ƙeƙƙega mijin Albasa ya tsaya tsayin daka ya nuna shi abin da Tantabara take so ko kuma wanda take so shi zai aura mata, ya nuna cewa shi ba ya mata auren dole, saboda Tantabara amana ce gare shi. A inda daga ƙarshe Mirsisi da Albasa dai suka yi kunya.
4. Wasan Sallah Mai Yawan Baya: Wannan wasa anyi ta ne bayan shagulgulan sallah da ake yi, inda ake nuni da yadda jama’a ke ƙoƙari wajen ganin cewa sun yi hidindimu kanta. Hakan yana saka wani ko ba ya da shi ya ce lallai sai ya yi ya kai ga shiga cin bashi, hakan ne ya sa aka saka ma wasar suna Sallah mai yawan baya.
Mutanen da suka fara wasan Duniya Makaranta:
1.
Abdullahi
Birnin Magaji
2.
Adamu
Abdullahi Kanoma
3.
Adamu
Abdullahi
4.
Alhaji
Shu’aibu Dangulbi
5.
Garba
Galadima
6.
Hajiya
Halima Bakwai Gulubba
7.
Isah
Galadima Nahuche
8.
Isah Na Banga-Banga
9.
Jamila
Abdullahi Liba
10.
Margayiya
Hajiya Miyatti
11.
Sadiya
Dauda
12.
Sani
Bello
13.
Suwaiba
Dauda
14.
Shehu
Muhammad ‘Yar ƙofa
15.
Shehu
Mai Baƙin-mai
16. Umaru Mai Doki
Tasirin Wasan Ga Al’umma:
Idan aka ce muhimmanci ana nufin amfani, kuma mun san cewa kusan duk wani abu dole ne a ce yana da muhimmanci, musamman ma irin wannan wanda yake amfani da tarin al’ummar da suke sauraron wannan wasan na duniya makaranta.
Don haka, wasan kwaikwayon duniya makaranta yana da
muhimmanci matuƙa musamman ga al’ummar jihar Zamfara
domin suna amfani da hanyoyi da dama wajen isar da saƙonni ga al’ummar kamar haka:
-
Duniya
Makaranta yana da muhimmanci hanya ce mai faɗa da alfasha da
kuma almubazzaranci
-
Hanya
ce ta inganta dangantaka da ƙarfafa zumunci
tsakanin yan wasa da jama’a.
-
Hanya
ce ta wayar da kan al’umma wajen sanar da al’umma abubuwa da suka shige masu
cikin duhu.
-
Hanya
ce ta neman abin rayuwa watau samun aikin yi wanda za a dogara da kai.
-
Hanya
ce ta ƙara haɓaka harshe da ƙara kalmomi da fito
da dabarun sarrafa harshe kamar karin magana, shaguɓe, habaici.
Tasirin Wasan Ga ‘Yan Wasan
1.
Shirin
Duniya Makaranta ya taimaka sosai wajen ƙarfafa zumunci
tsakanin ‘yan wasa da jama’a
2.
Hanyace
ta samar da abin yi da dogara da kai, watau aikin yi ga marasa aikin yi.
3.
Hanya
ce ta ƙara haɓɓaka harshe da ƙara kalmomi
4.
Hanya
ce ta hikimar shirya taɗi da hira da amfanar da mai harshe
5.
Hanya
ce ta samar da kuɗaɗen shiga ga ma’aikatar rediyo ita kanta
6.
Hanya
ce da za ta taimaka wa ɗalibai ƙwarai musamman masu
nazarin Harshe a Jami’o’i da kwalejoji.
Matsaloli da Wasan keFuskanta
Kusan dukkan wani aiki da ake yi akan fuskanci kalubale
gareshi, haka yake a fannin wasan “Duniya Makaranta”.
i.
Rashin
dawowar ɗan wasa
ii.
Matsalar
rashin kayan aiki
iii.
Matsalar
rashin kuɗi
iv.
MatsalarwutarLantarki
Hanyoyin Warware Matsala
Haƙuri kan kuɗi, watau sun yi ƙoƙar wajen sadaukar da karfinsu wajen gudanar da wasan. Saboda ‘yan wasan su na yin ƙoƙari wajen yi ba don a basu kuɗi ba, sannan ko da sunyi zasu saka kuɗin su ne wajen ganin cewa komai ya yi yanda ake so.Sun bayyana cewa wani lokaci idan buƙatar kuɗi ya taso sai dai wani ya yi cikin aljihunsa domin ganin an gabatar da wasan.
Ra’ayoyin Masu Sauraren Wasan
i. Sani Muhammad
ii. Abubakar Maitakara
iii. Sa’adu Umar Bukkuyum
Sani Muhammad; ya ce wannan wasa yana faɗakarwa, ilmantarwa da kuma nishaɗantarwa ga al’umma musamman ta ɓangaren gwamnati suna kariya gareta domin wani lokaci gwamnati ba ta aiwatar da wani abu ba, amma sai su faɗakar akan abin domin gwamnati ta gyara.
Malam Abubakar Maitakara cewa ya yi, “ni dai ina sauraron wannan wasan matuƙa in har ina zaune, don kusan duk lokuttan da ake wannan wasan na sani, a gaskiya yana karantarwa ga jama’a da kuma faɗakarwa ga ita kanta gwamnatin Zamfara. Ina ƙara ba masu aiwatar da wasan goyon baya domin ƙara inganta wasan ga masu sauraro ya yi daidai kamar yadda ya kamata.
Mal. Sa’adu Umar Bukkuyum; ya ce “Ni ke gabatar da wasan,
wannan wasan yana ƙayatarwa da kuma nishaɗantarwa ga al’ummar Jihar Zamfara, har ma da maƙwabtanta, a ko yaushe mutane suna jin daɗin wannan wasan
sosai, wasu daga cikinsu suna ba da shawarwari na cewa ya kamata a ƙara inganta wannan wasan.
Sakamakon
Bincike:
Wannan muƙala ta gano cewa
shirin duniya makaranta ya fi tasiri akan mutanen karkara da kuma matan aure da
gwamnatin jahar Zamfara.
Kasancewar galibin shirin ya fi mai da
hankali ne ga sana’oi da ayyuka na mutanen karkara, kamar noma da kiyo da dai sauransu.
Wannan ya sa mutanen karkara su ka
fi maida hankali sosai wajen sauraron wannan shirin na duniya makaranta a duk ranakkun
da ake yin shirin.
Mafi yawancin mutanen karkara galibi aikinsu noma kuma aikin noma aiki
ne na lokaci da zaran sun gama aikin sai yazamana basu
da wani aiki da ya fi shi, sai dai zaman gida kawai su ke yi. Wannan zaman
da suke yi yana
basu dama ta sauraron rediyo
ta yadda zakatarar mutanen har jiran lokacin shirin su ke yi.
Wannan
ne yasa a lokacin da a ke gudanar da was an masu yawan bugowa mutanen karkara ne, shi yasa masu yin shirin na duniya makaranta suka fi yin shi akan al’amurran da suka danganci mutanen karkara.
Ta fuskar matan aure kuwa, shirin yana
da tasiri ƙwarai
da gaske, domin kasancewarsu masu zaman gida,
don haka zaman gidan
da suke yi ya na basu dama ta sauraren rediyo da kuma bin kadin shirin na kowane lokaci,
ta hanyar sauraron wannan shirin zaka taras da mace
ta daina abin da take yi wanda ba na dai-daiba, ya na faɗakar
da su, kuma ya na nishaɗantar da su, haka kuma ya na wa’azantar
da su.
Shirin duniya makaranta yana faɗakarwa da nishaɗantarwa da wa’azantarwa da ma hanyar samun kuɗi ga masu yin wasan. Shirin yana faɗakarwa sosai
ta fuskar gabatar da shirin kan wani
sabon al’amari da ya shigo duk suna amfani da wannan dammar sai su yi shiri
a kan shi. Shirin kuma yataimaka ta hanyar samar da aikin yi gamarasa aikin yi.
Bugu da ƙari wasan duniya makaranta yana wayarwa al’umma kai game da manufofin gwamnati kan
demokaradiya, haka kuma yana ba da dama ga ‘yansiyasa su ziyarcesu domin
su yi tsokaci game da al’ummuran siyasa ta wannan zamani.
Kammalawa
Wannan muƙala ta yi nazari ne
akan wasan kwaikwayo “Duniya Makaranta” na gidan rediyon Jihar Zamfara” da
ma’anar wasan kwaikwayo, Rediyo da kuma ma’anar Duniya Makaranta, a wannan muƙala munyi bayanai akan kafuwar gidan rediyon Jihar
Zamfara, yadda aka gudanar da wasan a taƙaice. Haka kuma ta
kawo wasu jigogin wasan mutanen da suka fara gabatar da wasan. Wannan muƙala ta kawo muhimmancin wasan ga al’umma, matsaloli da
kuma hanyoyin da ake bi wajen gudanar da wasan da ra’ayoyin wasu masu sauraro.
Manazarta
Bello, (1992): “Wasan Kwaikwayo na Hausa” ZariaPublished by Northern
Nigeria Publishing Company Ltd..
Bunza, A.M
(2004) Waƙaƙƙen ƙa’idojinRubutun
Hausa Lagos Ibrash Islamic Publications Centre Ltd.
Ɗangambo, H. (1984)
“Wasanni Don yara” KanoCentre of Research and Publishing Company.
Yahaya da Wasu, (1992): “Darussan Hausa Littafi na uku. Ibadan University
Press Plc.
Yar Aduwa T.M (2007): Wasan Kwaikwayo na Hausa; Kano Nauoinsa da sigoginsa.
Usman Al-Amin Publishing Company;– Nigeria.
Zagga N.M (1988); Salo da Jigo da Tsarin Al’adun Hausawa a Wasar Idon
Matambayi “Kundin digiri na Farko, Sashen Nazarin Harsunan Nigeria, Jami’a
Usman Ɗanfodiyo Sakkwato.
Zaria, M. (1989) Gudummawar Kafofin Watsa Labarai wajen bunƙasa Harshen Hausa” Muƙalar da aka gabatar a
taron ƙarawa juna sani a Jami’ar Bayero ta Kano.
Waɗanda aka yi hira da su
1.
Lawali Muhammad Unguwar
Yarima
2.
Malam Sama’ila Tudun
Wada Gusau
3.
Malam Bello Abbas
Nasarawa Damba
4.
Mal. Salisu Abarma
5. Malama Jummai Iliyasu, Sabon Gari
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.