Ticker

6/recent/ticker-posts

Yaya Matsayin Sallar Mai Juna Biyun?

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum. Malam ina maka fatan alkairi dan Allah a amsa min wannan tambayar. Malam mace mai juna biyu tana fama da yawu, to ko da yaushe sai in da abin taunawa a bakinta, ko sallah za ta yi, in kuma ba ta sa abu a bakinta ba to za ta yi amai tana cikin yin sallar. To malam mene ne matsayin sallarta? Na gode.

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Wa'alaikumus Salamu, Lallai cin abinci a cikin sallah yana ɓata sallah, kamar yadda duk malaman Fiƙhu suka tabbatar, to amma shi ko amai ba ya ɓata sallah, saboda amai ba najasa ba ne, don haka bai halasta ta yi sallah tana tauna komai a bakinta ba, kawai ta yi sallarta a haka, ta sami kyallaye ko tsumma yalwatacce kuma mai tsafta da idan amai ɗin ya zo mata za ta yi a ciki, ta share bakinta, ta kuma cigaba da yin sallarta, kuma sallarta ta inganta a hakan.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.🏻

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/J1hm5Tw12uYBƙfaiPwf28l

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments