Ticker

6/recent/ticker-posts

Canja Abinci Da Miji Ya Kawo

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Malam mene ne matsayin canjen abinci da mata ke yi kamar mijinta ya ajiye mata semonbita ita kuma ta fi son masara sai ta canza?

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Wa alakum assalam, ya kamata ya zama da iznin miji saboda hakan zai iya kawo rikici a tsakaninsu, tun da zai iya fahimtar rainawa da rashin wadatar zuci.

Rayuwar aure tana tsayuwa a kan girmama miji da nuna ba ki da sama da shi, da kimanta shi, Annabi yana cewa inda zan umarci wani ya yiwa wani sujjada, da na umarci mace ta yiwa MUJINTA sujjada kamar yarda Ibnu Hibban ya rawaito a Sahihinsa a hadisi mai lamba ta: 4162 kuma shuaibu Al’arna’ud ya inganta .

Wannan yake nuna girman da muhimmanncin rashin Saɓa masa.

WALLAHU A'ALAM

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/J1hm5Tw12uYBƙfaiPwf28l

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments