Jerin keɓaɓɓun kalmomi a ɓangaren ilimin kimiyyar harshe tare da fassarorinsu cikin Turancin Ingilishi.
Wasu Keɓaɓɓun Kalmomin Nazarin Harshe Da Ma’anarsu Ta Hausa
Daga
ALMUSTAPHA
WALI SAMBO
Mail:
mustaphaoldman@gmail.com
Phone:
+2347061305340
A
abstract noun - sunan ɓoye
accent - karin lafazi
acceptability - karɓuwa
accusative case - sigar karɓau
active voice - kalami nufatau
acute accent - tsanantaccen lafazi
Adam’s apple - zakaran wuya
adjectival complex - sarƙaƙiyar
sifa
adjective phrase - yankin sifa
adjective stem - tushen sifa/sifatau
adjective - sifa/sifatau
adjunct - ƙawatau
adjunction - ƙawatawa
adverb of degree - bayanau ƙimau
adverb of manner - bayanau na yanayi
adverb of place - bayanau na wuri
adverb of time - bayanau na lokaci
adverb phrase - yankin bayanau
adverb - bayanau
adverbial cluster - cunkoson bayanau
adverbial complex - sarƙaƙƙen
bayanau
adverbial compound - harɗaɗɗen
bayanau
adverbial noun - bayanau na suna
affirmation - tabbatarwa
affirmative sentence - tabbatacciyar jumla
affirmative - tabbatau
affix - ɗafi
agential adjective - sifa mai ‘ma’
agreement suffix - manunin yarjejeniya
agreement/auxiliary phrase - yankin
yarjejeniya
agreement/concord - jituwa/yarjejeniya
alphabet - abajadi
ambiguity - harshen damo
ambiguous - mai harshen damo
anaphor - inuwar wakilin suna
anaphora - nanatau
animism - maguzanci
anomalous - shirɓatacce
anomaly - shirɓace
antonym - kishiyar kalma
aspect - taƙi
B
basic - tushe
basic/simple sentence - sassauƙar jumla
bilingual - mai magana da harsuna biyu
bilingualism - magana da harsuna biyu
bisemy - ma’ana biyu
branch - rassa
branching - rabuwar rassa
C
case grammar - nahawun zumunta
chapter - babi
circumflex accent - faɗaɗɗen karin lafazi
class - aji
classical language - harshen gwaninta
classification - rarrabewa
clause - ganga
close syllable - rufaffiyar gaɓa
closed class - rufaffen aji
code-mixing - hargitsa-balle
code-switching - surki
collective noun - suna tattarau
colloquial - gargaliya
combination - gamin-gambiza
common language - harshe gama-gari
common noun - suna gama-gari
comparative grammar - nahawun kwatance
comparative linguistics - ilimin kimiyyar
bambance harsuna
competence - basira a harshe
complement - cike
complementary distribution - zaman surukai
complex sentence - sassarƙiyar jumla
complex - sarƙaƙƙe
compound noun - harɗaɗɗen suna
compound sentence - harɗaɗɗiyar
jumla
compound - harɗaɗɗe
compound-complex sentence - harɗa-sarƙiyar jumla
concept - tunani
concrete noun - sunan fai
condition - sharaɗi
conditional - sharɗaɗɗe
conditional clause - sharɗaɗɗiyar
ganga
conjunction - kalmar haɗi/ɗori
consonant - baƙi
constituent - tubali
constraints - tarnaƙi
construction - gini
contradiction - saɓani
contrastive analysis - nazarin bambancin
harsuna
contrastive distribution - zaman bamban
copular/stablizer - dirka
countable noun - suna ƙirgau
creole - gargaliyanci
critical analysis - ƙalailaicewa
culture - al’adu
D
declarative/statement sentence - jumla mai
sigar jawabi
declension - rikiɗewar kalma
deep structure - ƙirar ɓoye
deletion - shafewa
demonstrative proper - manuniya
demonstrative specifier/determiner - nunau
denotation - ma’anar fili
dependent/subordinate clause - ƙaramar
ganga/ganga dogarau
descriptive grammar - nahawun bayani
descriptive level of adequacy - mataki na
bayyanawa
dialect - karin harshe
dialectology - ilimin nazarin karin harshe
diglossia - hawa biyu
diminutive - tsigalau
diphthong - tagwan wasali
direct object noun - karɓau na
kai-tsaye na suna
direct object pronoun - karɓau na
kai-tsaye na wakilin suna
direct object - karɓau na kai-tsaye
disjunction - rabau
disjunctive pronoun - wakilin suna rabau
disyllabic verb - aikatau
mai gaɓa biyu
dynamic noun - sunan-aiki
E
embedded sentence - goyayyiyar jumla
embedding - goyon jumla
emphasis - ƙarafafawa
entailment - goyon ma’ana
exclamatory sentence - jumla mai
sigar motsin rai
explanatory level of adequacy - mataki na ƙalailaicewa
F
falling tone - karin sauti faɗau
feminine gender - jinsi ta mata
finite clause - ganga sanau
first future tense - lokaci mai zuwa na I
first language acquisition - naƙaltar
harshen farko
first language - harshen farko
first person - mutum na ɗaya
fluency - iya harshe
fluent - gwanin harshe
foreign language learning - koyon baƙon
harshe
foreign language teaching - koyar da baƙon
harshe
foreign language - baƙon harshe
formal grammar - nahawun ƙa’idance
formalism - bi-ƙa’ida
formation - sigantawa/ginawa/zubawa/tsarawa
functional categories - rukunin kalmomi
masu aikin nahawu
future - mai zuwa
G
geminate adjective - tagwan sifa
geminate - tagwaitawa/shaddantawa
gender - jinsi
general continuous tense - lokaci mai ci
yanke
general past tense - shuɗaɗɗen lokaci yanke
generalization - jam’u
generative grammar - nahawun tsirau
generative linguist - masani/manazarci
nahawun tsirau
generosity - karimci
genetival complex - sarƙaƙiyar nasaba
genetival link - mahaɗin nasaba
genitive - nasaba
grade - giredi
grammar - nahawu
grammatical analysis - bayanin nahawu
grammatical category - rabe-raben
nahawu/kalmomi
grammatical models - ra’o’in nahawu
grammatical sentence - karɓaɓɓiyar jumla
grammatical - karɓaɓɓe
grammaticality - karɓuwa
grave accent - sassautacciyar alama
H
habitual tense - sababben lokaci
habitual tense-aspect - sababben lokataƙ
Hausa Verbal Grade System - Tsarin Giredin
Aikatan Hausa
head/nominal - jagora
heavy syllable - gava nannauya
high tone - karin sautin sama
high vowel - wasalin sama
hyponym - ‘yar dangi
I
ideograph - zanen tunani
ideology - aqida
ideophone - amsa-kama
ill-formed sentence - yasasshiyar jumla
imperative/command sentence - jumla mai
sigar umarni
imperative/subjunctive - umartau
imperfective tense-aspect - ragaggen lokataƙ
indefinite pronoun - wakilin sunan da ba a
fayyace ba
indefinite specifier/determiner - lamirin
da ba a fayyace ba
independent pronoun - wakilin suna mai
zaman kansa
independent/main/matrix clause - ganga
tsayayyiya/babbar ganga
indirect object - karɓau na kai-kai-ce
infix - ɗafa-ciki
influence - tasiri
interjection - motsin rai
interlanguage - harshe ƙirƙirau
interrogative pronoun - wakilin suna
tambayau
interrogative specifier/determiner- lamirin
tambaya
interrogative/question sentence - jumlar
tambaya
intransitive preposition - harafi ƙi-karɓau
intransitive verb - aiktau ƙi-karɓau
intuition - ilhami
irregular verb - aikatau ƙi-tsarin-giredi
isolated - warau
K
keyword - fitacciyar kalma
kinship term - sunan dangi
L
labeled bracketing - tsarin baka-biyu
Language Acquisition Devices (LAD)- hanyoyin
laƙantar harshe
language acquisition - laƙantar
harshe
language diversity - bambanci/saɓanin
harshe
language learning - koyon harshe
language planning - tsarin amfani da harshe
language policy - shirin amfani da harshe
language variations - bambance-bambancen
harshe
language - harshe
levels of grammatical adequacy - matakan
auna nahawu
lexicography - shirya ƙamus
lexicon - rumbun kalmomin harshe
lexis - kalmomin harshe
light syllable - gaɓa sassauƙa
lingua franca - harshen hulɗa/zamantakewa
linguist - masani/manazarci kimiyyar harshe
linguistic deviation - saɓa ƙa’idar
harshe
linguistic mapping - zanen taswirar
kimiyyar harshe
linguistics - ilimin nazarin kimiyyar
harshe
link element/linker - mahaɗi
literature - adabi
loan word - kalmar aro
location marker - manunin bagire
long consonant/gemination - shadda/tagwaitaccen
baƙi
long demonstrative - nunau ta nesa
long possessive - doguwar mallaka
long syllable - doguwar gaɓa
long vowel - dogon wasali
low tone - karin sautin ƙasa
M
masculine gender - jinsi namiji
mass/uncountable noun - suna ƙaƙara-ƙirga
metalanguage - keɓaɓɓen harshe
metathesis - sauyin gurbi/rawar ‘yan mata
mid-vowel - wasalin tsakiya
minimal pair - ‘yan biyu
modern linguistics - kimiyyar harshe na
zamani
modifier - fayyatau
monophthong - gwauron wasali
monosyllabic verb - aiktau
mai gaɓa ɗaya
morpheme - ƙwayar ma’ana
morphology - ilimin nazarin ƙirar
kalma/tasrifi
morphophonology - ilimin nazarin sauti da
tasrifi
morphosyntax - ilimin nazarin ƙirar
kalma da ginin jimla
mother tongue - harshen uwa
movement - gushi/gusawa
multilingual - mai magana da harsuna uku
multilingualism - magana da harsuna uku
mutual intelligibility - fahimtar juna
N
native language - harshen asali/tushe/uwa