Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Wadda Haila Ta Zo Mata Daidai Lokacin Shan Ruwa

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Salamun aleikum malam, Allah gafarta malam da fatan an sha ruwa lafiya, don Allah malam ina da tambaya, tambayata ita ce shin malam ina azumi, na yi sallar azuhur da la'asar, ban yi magariba da isha'i ba sai na ga al'ada ta zo min, shin abin da nake so na sani akwai azumina ko babu shi? Na gode.

Amma fa sai da na sha ruwa sannan na ga al'adar ta zo amma ban yi sallar magariba da isha'i ba.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus salam, ‘yar uwa matuqar al'ada ba ta zo maki ba sai bayan da rana ta faɗa, ko da ba a yi sallar magriba ba, to azuminki na wannan yini ya inganta da ikon Allah, ba wata matsala da ta same shi, kasancewar ba ki yi sallar Magriba da Isha'i ba haila ta zo maki, wannan bai ɓata maki azuminki ba, saboda lokacin azumi yana farawa ne daga ketowar Alfijir zuwa faɗuwar rana, to ke kuma sai bayan da rana ta faɗa sannan hailar ta zo maki, ga shi ma har ruwa kin ce kin sha, saboda haka azuminki ya inganta, in da a ce kafin rana ta faɗa ne haila ta zo, to da sai a ce azumi ya ɓaci.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa  a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BpO6i5KwGBm8IcVtlhBr0j

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments