Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum Malam A bani shawara: Na kamu da wata
cuta ta zubar da yawu wanda bana iya kai azumi yau shekara uku kenan, nasha
azumi 23 da farko, shekara ta zagayo ban samu sauki ba na kuma shan 20 kuma ina
tsoron kada wata shekaran ta riskeni shine na auno masara mudan nabi 43 akan
akwai makwabtanmu yaran marayu ne, shin idan na basu na biya azumi na ko ko? Na
gode
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikum assalam In har akwai tabbacin ciwon ba zai
warke ba ka rama azumin, kana iya ciyarwa. Amma in har akwai tunanin za ka
warke to ba za ka ciyar ba, saboda wajibi akan mara lafiyan da ya sha azumi
saboda lalura ya rama a wasu kwanakin na daban kamar yadda Allah yake cewa: "Kuma wanda ya kasance
mara lafiya bai azumci Ramdan ba, to ya rama abin da ya sha a kwanaki na daban"
Suratu Al-bakarah aya ta:(185).
Aya ta (184) a cikin surar ta nuna wanda ya sha azumi saboda rashin lafiya ko tsufa
kuma babu tunanin ya samu damar ramawa nan gaba zai iya ciyarwa.
A bisa abin da ya gabata In har likita ya tabbatar za
ka samu damar ramawa nan gaba to azumin yana nan akanka, ciyarwa ba za ta
wadatar maka ba.
Sannan in har ciyarwa ce ta halatta a kanka ai ba mudun-nabi ake
bayarwa ba !!!
Allah ne mafi sani
DR JAMILU YUSUF
ZAREWA
Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa
Tare Da Fadakarwa a Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/DVpHjgfRdK9IRWvkB23lbE
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.