Ticker

6/recent/ticker-posts

Ban Rama Azumin Bara Ba, Gana Bana Ya Zo, Ya Zan Yi?

 Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

 Question and Answers in Islam

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Malam Akan samu wasu daga cikin mata ana bin su azumin Ramadan ba su rama ba har wani Ramadan ɗin ya riske su. Ina hukuncin wannan?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Abun da yake wajibi akansu shi ne su tuba zuwa ga Allah su daina irin haka, domin ba ya halatta ga wanda ake bin shi azumin Ramadan ya jinkirta shi zuwa wani Ramadan ɗin ba tare da uzuri ba. Domin Nana A'isha, Radhiyallahu anhaa ta ce: "Ya kan kasance ana bi na azumin watan Ramadan, ba na iya rama shi sai a watan Sha'aban".

Wannan yana nuni akan ba ya yiwuwa mutum ya jinkirta ramuwan azumin watan Ramadan har zuwa wani Ramadan ɗin, don haka ya zama wajibi a gare ta, ta tuba kuma ta rama azumin da ake bin ta bayan ta kammala azumin Ramadan na biyu da ya riske ta.

A duba:

فتاوى المرأة المسلمة يجيب عليها أصحاب الفضيلة العلماء.

Shafi na 338

Amsawa:

 Sheikh Muhammad Salih al-Uthaimeen, Rahimahullah

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa  a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/DVpHjgfRdK9IRWvkB23lbE

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

Post a Comment

0 Comments