Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Mene ne hukuncin yaɗa irin wannan saƙonnin???
👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
SALAMU ALAIKUM
Yana daga sunna Na ma'aiki kanemi gafarar kowa kafin
shigar watan RAMADAN, dan Allah idan nataba bata maka/miki asane ko arashin
sani, ina neman Yafiyarka/ki, ki/ka
yafemin
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Toh wannan akwai nau'ine na ganganci babu shakka
acikinsa. Domin nidai ban taɓa jin inda akace Annabi
Muhammad (s.a.w) ko sahabbansa suna neman afuwar junaba saboda kusantowar
ramadana kokuma saboda shigowarsa. Toh amma ita wannan tace wai sunnar
Annabinema mutum yanemi afuwar mutane toh kaga wannan inhar babu jahilci acikin
lamarin toh akwai ganganci domin kuwa a ƙa'ida baka kiran abu sunnah
se wanda ya tabbata. Idan abu ya tabbata cewa tabbas Annabi (s.a.w) yafaɗa kokuma ya aikata toh shine
se ace sunnah amma idan akwai shakku akwai ko be ingantaba toh sedai acemai
hadisi amma badai ace sunnah ba.
Toh amma ita wannan kaga saboda ganganci da taƙama kai tsayema tace wai yin hakan sunnah ne. Amma ƙila batada labarin cewa Annabi (s.a.w) yace duk wanda ya yi
masa ƙarya da gangan toh ya tanadi wajanda ze zauna a wutar
jahannama. A wata ruwayar kuma yace duk wanda yace nafaɗi abu alhali kuma ban faɗa ba toh haƙiƙa ya girmma ƙarya ga Allah seya tattali wajanda ze zauna a wuta. Toh
kaduba irin wannan bala'i da Annabi ﷺ ya ajjiye akan wanda ya yi
masa ƙarya toh tayaya zakizo kina yiwa Annabi ﷺ ƙarya da sunan kina neman afuwar mutane? Shin wacce riba
zakici idan mutanen suka yafe miki Annabi ﷺ kuma shi da kikaiwa ƙarya be yafe mikiba??? Na'am babu shakka neman afuwa abune
mekyau amma ware wani lokaci ace se a wannan lokacin shine za'a nemi yafiya toh
wannan kodai bakacema abun bidi'a ba toh be kamataba acemai sunnah domin sunnah
tanada ƙa'idoji awajan malamanta.
Allah Ya sa mu dace
Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa
Tare Da Fadakarwa a Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/BJikpGm7VXV1vEVVGcNH5J
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.