Tsayuwar Sallar Mace, Za Ta Ware Kafa Ko Za Ta Tsuke Ta?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalam alaikum Malam naga wasu na yawo da wani post na cewa ba a kabar sallah mace da ta yi sallah alhalin kafafunta na wace inda wasu mallamai suka ce ba hakan ba ne mallam miye tabbacin hakan?

    𝐀𝐌𝐒𝐀👇

    Waalaikumussalam, A Iya Abin da Nasani Wanda Kuma Dayawa Daga Cikin Malamai Na ji Sun tafi a kan Hakan shi ne Annabi Ya ce, SALLU KAMA RA-AITU MUNI USALLI (Kuyi Sallah Kamar Yadda Kukaga Ina yin Sallah) A Sallah Be Ware Cewa Ga Kalar Ta Mata ba Ga Kuma Ta Maza, Kawai Dai Su Mata Kamar Yanda Kowa Ya Sani shi ne za su Rufe Jikinsu Dukane Saboda Ko Ina Al'aurane A Jikinsu, za su Rufe Tin Daga Kai Har Kafafun Karsu Bayyana Da Abu Me Kauri Kuma Bame Nuna Shape Ba, Wannan Shi Ake Kirada Hijabi, Wadda Take Saka Saɓanin Wannan Kuma Sai dai Muce Allah Ya Shirya.

    Malamai Da Dama Sun yi Magana a kan Tsuke Kafa Da Wasu Matan Suke Wannan Ba Karamin Kuskure ba ne, Sai dai Sun yi Bayanin Cewa Su Mata Yanda za su Ware Kafar Tasu Za su yine Bada Fadiba Kamar Yanda Maza Suke Nasu. Sannan Musani Cewa Duk Wadannan Abubuwan Ana Yin su ne Domin Sallar Tasamu Cikakkiyar Karbuwa, Rashin Cika Wannan Ka'idoji Baya Daga Cikin Dole Na Sallah Sai dai Mutum Yana Barin Falala Me Girma, Kamar Su Samun Rahamar Allah Ga Masallata Sannan Cika Wadannan Sharudan Yana Daga Cikin Nuna Soyayyarka Ga Annabi Muhammad Wanda Hakan Zesa Ku Tashi da shi Ranar Gobe Alkiyama, Shi ya sa Ake so Dakaji Ance Wannan Abu Sunnah ne To Kayi shi Ba Kakkautawa.

    WALLAHU A'ALAM.

    🏼 Abu_Zhahrah.

    Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/Eub2uLrV18T4vHJcƙRDkPZ

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.