Ticker

6/recent/ticker-posts

Game Da Rubutun Novels, Shin Halal Ne Ko Haramun?

 Rubutun Novels ya kasu gida uku:

1• Akwai wanda yake haram ne gaba ɗayansa, saboda irin saƙonnin da ke cikinsa sun saɓawa Alƙur'ani da sunnah.

 Kamar littafin da yake ƙunshe da kalmomi na shirka da kuma da suke raba kan musulmi dama al'ummar baki ɗaya.

 Kuma suna kimsa rasahin zaman lafiya a tsakanin ma'aurata ko suke raba kishiyoyi suna kuma raba iyaye da yaransu, harma wasu suna nuni da yadda ake bin malaman tsubbu da bokaye da sauransu, to irin wannan littafin kwata-kwata haramun ne.

2• Akwai wanda yake ɗauke wani sashinsa akwai ɓarna wani sashin kuma yana amfanarwa, kamar litattafan da ke ƙunshe da bayanai a kan mene ne aure da kuma zaman aure da kuma wasu hanyoyi da za abi domin kyautata zamantakewa a tsakanin miji da matarsa harma da abokiyar zamanta.

 Amma kuma wani sashin nasa yana ɗauke da kalmomi na batsa wanda hakan yana jefa mai karatu a cikin damuwa musamman idan waɗanda basuda aure suna karantawa sai su sami kansu cikin motsawar sha'awa wanda hakan yana kai ga wasu su fara istimina'i wasu kuma su afkawa zina ko maɗigo.

 To irin wannan littafin akwai buƙatar ya zama antaceshi aya yin rubutu, kuma mai rubutun ya kiyaye Haƙƙoƙin ALLAH a cikin rubutunsa, kada ya rubuta abin da zai jawo masa zunubi a gaban ALLAH.

 

3• Akwai littafin da yake dukkansa halal ne, kamar irin wanda ke ƙunshe da bayanai wanda wasunsu an cirosu ne daga Alƙur'ani da Hadisai ingantattu.

 Wasu bayanan kuma suna ƙunshe da hikima da nasiha da kuma labarai na magaba ta na ƙwarai domin a koyi darussa daga irin rayuwarsu kuma a koyar da masu zuwa a bayan-baya.

 Sannan kuma suna koyar da yadda mutum zai rayu cikin aminci suna nuni da illolin ha'intar miji ko ƙawa ko aboki ko wanin haka.

 Suna kuma nuni da sakamakon mai aikata wani aiki mara kyau da yadda ƙarshensa ke ƙarewa, wanda kuma ya yi haƙuri ya bi ALLAH da Manzon ALLAH {s.a.w} yakan sami sakamakonsa mai kyau dadai sauransu.

 Saboda haka ire-iren waɗannan littattafan suna da kyau, domin ta hanyarsu ana samun al'umma na gyaruwa, sannan kuma akwaisu a cikin yare iri-iri, kamar Larabci ko ingilishi ko Faransanci ko Hausa.

 Mafi kyawun littafi mai ɗauke da gaskiyar zance shi ne Alkur'ani da Hadisan Manzon ALLAH {s.a.w} sai dai muna wani zamani wanda ba kowa ke iya buɗe Alkur'ani ko Hadisi ya bibiyi hukuncin ALLAH a cikinsu ba,

 Amma kuma mutane na iyabxaman karanta Novels, shi ya sa idan aka ciro bayanan aka saka a cikin littattafan Novels aka faɗaɗa bayanai, kuma aka yisu cikin harshen da mai karatu zai fahimci saƙon da ke cikinsu, to mai karatu zai zauna ya yita bibiyar abin da ke cikin wannan littafi ba tare da gajiya ba, kuma maribucinsa zai sami lada, mace ko namiji.

ALLAH TA'ALAH ka sa mu dace, ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments