Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Magidancin Da Ya Bar Iyalinsa Suna Yawo Da Gyale

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum wa rahmatullah ina ma mallam fatan alheri, mallam Tambaya kamar aka, ya dace magidanci ya bar matansa da ya'yansa suna yawo da gyele. Mallam shin bashi da laifi idan ya kasance shi ya ƙoƙarin bin sunnah aman su bai hana su saka gyale ba sobada ba a ko da yaushe suke fita da gyale ba shin hakan ya dace? jazakumullahu khair

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillah wa ala alihi wa sahbihi ajma'in.

Gaskiya bai dace ga magidanci ya zamo kan shiriya, sunnah, amma iyalinsa da yaransa a kan bidi'a da saɓon Allah, domin amana ne Allah ya damƙa a hannunsa kuma ya ce ya kula da su ya tseratar da su daga wuta. Ba an ce ya yi ta kansa ba ne shi kaɗai, bar saura ko oho.

(یَـٰۤأَیُّهَا ٱلَّذِینَ ءَامَنُوا۟ قُوۤا۟ أَنفُسَكُمۡ وَأَهۡلِیكُمۡ نَارࣰا وَقُودُهَا ٱلنَّاسُ وَٱلۡحِجَارَةُ عَلَیۡهَا مَلَـٰۤىِٕكَةٌ غِلَاظࣱ شِدَادࣱ لَّا یَعۡصُونَ ٱللَّهَ مَاۤ أَمَرَهُمۡ وَیَفۡعَلُونَ مَا یُؤۡمَرُونَ)

[Surah At-Tahrim 6]

 

Ya sani cewa gobe ƙiyamah ba zai kuɓuta a gaban Allah ba, sai ya yi bayani kan amanar da aka bashi. Allah ya ce mu umarce iyalan mu da su yi sallah, Annabi ya ce a duke su idan ba su yi sallah ba a shekara goma. Allah ya ce

(وَأۡمُرۡ أَهۡلَكَ بِٱلصَّلَوٰةِ وَٱصۡطَبِرۡ عَلَیۡهَاۖ لَا نَسۡـَٔلُكَ رِزۡقࣰاۖ نَّحۡنُ نَرۡزُقُكَۗ وَٱلۡعَـٰقِبَةُ لِلتَّقۡوَىٰ)

[Surah Ta-Ha 132]

Annabi sallallahu alaihi wa sallama Ya ce

5866 - «مروا أبا بكر فليصل بالناس».

(صحيح) [حم ق ت هـ] عن عائشة... [ق] عن أبي موسى... [خ] عن ابن عمر... [هـ] عن ابن عباس وسالم بن عبيد. فقه السيرة 499، الإرواء 541.

Bayan haka, Annabi ya ce mai rashin kishin iyali, yara mata, ko yan'uwa mata, ba zai shiga aljanna ba, Annabi ya ce mutane uku ba su shiga aljanna, mai saɓa ma iyaye, daiyus da macen da ke kama da maza

3063 - «ثلاثة لا يدخلون الجنة: العاق لوالديه والديوث ورجلة النساء».

(صحيح)... [ك هب] عن ابن عمر. حجاب المرأة المسلمة ص 67: حم، الضياء.

 

A nan nake so na jawo hankalin mata musulmi, su gane cewa, hijabi, addini ne, ibadah ce, Allah ne ya umarce su da shi. Allah ya fara da Annabi ne sannan aka zo ga sauran muminai, Allah Ya ce

(یَـٰۤأَیُّهَا ٱلنَّبِیُّ قُل لِّأَزۡوَ ٰ⁠جِكَ وَبَنَاتِكَ وَنِسَاۤءِ ٱلۡمُؤۡمِنِینَ یُدۡنِینَ عَلَیۡهِنَّ مِن جَلَـٰبِیبِهِنَّۚ ذَ ٰ⁠لِكَ أَدۡنَىٰۤ أَن یُعۡرَفۡنَ فَلَا یُؤۡذَیۡنَۗ وَكَانَ ٱللَّهُ غَفُورࣰا رَّحِیمࣰا)

[Surah Al-Ahzab 59]

Daga ƙarshe saka gyale ba laifi ba ne idan zai rufe dukkan jiki, yana da kauri, babu ado, bai kama da na kafirai ba, ba mai ɗaukar ido ba, ma'ana dai idan ya cika sharuɗɗan hijabi.

Wallahu ta'aala a'alam.

Amsawa:

Malam Aliyu Abubakar Masanawa

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Eub2uLrV18T4vHJcƙRDkPZ

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments