Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Mata Za Su Iya Bayyana Karatu A Sallah Kamar Maza?

 Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

السلام عليكم ورحمة الله وبركاته

Dan Allah malam tambaya na a kan sallah ne shin mata za su yi karatun su ne a bayyane agurin bayyanawa koko a sirrance za su yi?

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Wa alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuhu

Hadisi ya tabbata daga Annabi ya ce ku yi sallah kamar yanda kukaga inayin sallah sannan ba'ace gata maza gata mataba, Allahumma saidai malamai sun yi ƙarin haske gameda bayyana karatun mace a cikin sallah domin shi Alkur'ani rerashi ake ita mace duk da muryarta ba al'aura ba ce amma daga sautinta zai iya jawo hankalin namiji, sai aka ce idan mace ita kaɗai take sallah za ta yi abayyane ne amma za ta jagoranci 'yan uwanta wajan Limanci za ta shiga gaba tatsaya atsakiyarsu asahun farko ke nan tabayyana musu katatun batareda data daga murya kamar yanda maza sukeyiba

WALLAHU TA'ALA A'ALAM

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/L8l4xHCd7wUG5xZEmvBbzB

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

Post a Comment

0 Comments