Ticker

6/recent/ticker-posts

Jinin Haila Yana Zuwa Min A Yayyanke, Ya Zan Yi?

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Idan mutum yana jinin haila yana mashi kwana shidda. Amma sai ya yi kwana biyu ya dauke, bai ganshi a kwana na ukku ba. Sai kwana na huɗu ya ganshi. Toh wannan yana cikin kwanukan hailar shi na asali. Kuma zai yi lissafin kwanan da bai zo ba a cikin kwanakin hailar tashi ko yaya zai yi?

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Wa’alaikum assalam. Yayyankewar jinin haila, ta yadda yau mace za ta ga jini, gobe kuma taga tsarki ko makamancin haka, ya kasu kashi biyu:

1. Idan kodayaushe haka take gani, to wannan hukuncinta hukuncin mai jinin istihala ne, ta yadda hakan ba zai hana ta ibada ba.

2. Idan ya zama wasu lokutan take ganin hakan, yawancin lokutan kuma tana samun tsarki, to wannan malamai sun yi saɓani a kan wannan tsarkin, shin tsarki ne ko kuma yana ɗaukar hukunce- hukuncen jinin haila ne?

A mazhabar malikiyya duk sanda ta ga jini to yana daukar hukuncin jinin haila, haka ma tsarki yana daukar hukunce-hukuncen tsarki, ta yadda za ta yi wanka duk yinin da ta gan shi, saidai idan an hada su sun wuce mafi yawancin haila, to sai jinin da ya wuce ya zama istihala.

Sai dai idan yana yayyankewa kusa kusa, to tana iya jinkirta wankan, sai ta hada sallolin da ba taga jini ba a lokutansu, saboda yin wanka a kowanne lokaci akwai wahala a ciki, kuma Allah yana cewa: “Bai sanya muku kunci a cikin addini ba”

 

Don neman karin bayani duba Hukunce-hukuncen jinanen al’ada shafi:15.

 

Allah ne mafi sani.

 

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfƙds

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

Post a Comment

0 Comments