Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
MAZA DA YAWA ZA SU YI DANA SANI A GABAN ALLAH
Da yawan maza a wannan zamanin sukan yi aure ne ba dan
ibadah ba sai kawai domin biyan buƙatar kansu, hakan ya sa mata
suke fuskanta matsaloli iri-iri a cikin zaman aurensu a wannan zamanin.
Zaizo ya yita
lallaɓaki kafin ya aureki amma da zarar kin zama matarsa ya samu ya
kusanceki, tofa shi ke nan saiya fara canja miki, ya fara watsi da duk wata
soyayya da yake nuna miki a lokacin baya kafin aure,
kuma bazaga
gane auren biyan buƙata ba ne sai lokacin da
suka gama jima'i yana samun biyan buƙatarsa saiya juya mata baya,
babu ruwan da ita, bai damu ba ta sami gamsuwa ko ba ta samuba, inda za ta yi
masa magana a kan cewa itafa ba ta sami gamsuwa ba a wannan lokacin da sai ya
gaya mata magana mara daɗi lallai maza ku ji tsoron
ALLAH ku sani ALLAH ba zai bar wannan hakki ba dole za a tambayeku akansa.
Wani kuma daga
lokacin daya santa a mace, to shi ke nan batada wata daraja a gurinsa saiya
fara tunanin ƙaro aure, ko da kuwa baida
halin ƙaro auren, kuma ita kanta
matarsa ta gida ba ta samun cikakkar kulawa daga gareshi amma a haka yake
hangen ya auro wata a waje kuma fa baya iya gamsar da ita a kwance kuma baya
wadatar da ita da duk wani da take buƙata na hidimomin gida.
Amma a haka
zakaga ita wacce zai ƙaro saboda rashin tunani
bazata yi bincike ba akansa tasan yaya yake rayuwa data gidan, amma a haka za
ta aureshi babu bincike saboda kwaɗayin abin duniya ko kuma ya
zo ya banka mata ƙarya, sai bayan ta shigo
kuma a fara yawo gurin Bokaye ana nemi sihiri.
Sannan daga
ranar daya ƙaro aure to ita wannan uwar
gidan ta zama mara amfani zai maida ita kamar shara, domin ita shara duk dattin
da aka kwaso ita ake kaiwa, to ita ma idan aka ɓata masa rai akanta zaizo ya
sauke ba zai iya zuwa wajen amaryasa ba ya yi mata haka ba.
To ita ma amaryar
data kwana biyu zai fara hangen wata saiya fara wulaƙantata itama, wannan shi ne auren biyan buƙata, irin wannan auren ALLAH yana cire albarka a cikinsa.
Sannan wasu
mazan kuwa da zarar uwar gida ta nemi hakkinta sai ya yi ƙoƙarin zaginta wanima harda
duka wani kuma saiya sake ta to ku sani ALLAH yana kallon duk abin da kuke
aikatawa ALLAH ya ce na haramta zalunci a kan kaina kuma na haramtashi a
tsakaninku.
Sannan kuma
babu wani miji ko maca da wani zai zalunci wani a tsakaninsu face sai sun tsaya
a gaban ALLAH a ranar alƙiyama an karɓawa mai hakki hakkinsa kuma
a wannan rana ana biyan hakkokine da ayyukan ƙwarai, kuma sai a kwashi
salloli da azumi da wasu ayyuka na mutum na shekara ɗaya basu gama biyan hakkin
matarka daka tauye na kwana ɗaya ba.
Lallai mazan wannan
zamanin mun rasa wasu abubuwa wanda duk wanda bai kiyayesu ba zai iya samun
kansa a cikin azabar ALLAH wato su ne kamar haka:
• Hakkin ciyarwa gwargwadon iko.
• Tufatarwa gwargwadon iko.
• Baiwa matarka lokacinka domin ɗebe kewa.
• Maganganu masu daɗi da rarrashi.
• Gamsar da ita a ya yin kwanciyar aure.
• Girmama iyayenta da ƴan uwanta.
• Nisantar kule-kulen mata a waje.
• Son kanka da nuna isa da iko ga matarka.
Wato abubuwan
nada yawa lallai mu sani a kan rashin kiyaye waɗannan abubuwa da muka
lissafo a sama da yawan maza za su iya faɗawa cikin azabar ALLAH a
dalilin rashin kiyayesu.
Da yawan mata
suna afkawa zina ne a dalilin mazansu ba sa iya gamsar dasu a ya yin jima'i.
Da yawan mata
suna fara yiwa mazansu sata ne a dalilin mazan ba sa iya basu abin da zai
wadatar dasu na harkokin gida kuma bawai babu ba ne akwai dukiyar kaeai mugunta
ce.
Sai kaga
abincin da za a dafa kowa yaci da shi da 'ƴa'ƴansa amma yana baƙin cikin ya bada kuɗin cefanen dazai wadatar a
yi komai ya yi kyau, idan kuwa ta yi iya ƙokarinta da abin da ya bata,
sai ya zo yana faɗa yana masifa, ya manta shi ne ya bai bada abin da zai
wadatarba.
Don haka lallai
maza muji tsoron ALLAH mu gyara tsakaninmu da matanmu sai tsakaninmu da ALLAH
ya yi kyau.
ALLAH ka bamu ikon yin adalci a tsakaninmu da matanmu.
ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.