Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin idan al'adar mace ya ɗauke sai ta yi wanka bayan fitowar alfijir, sai ta yi sallah ta yi azumi, shin za ta rama azumin wannan ranan?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Shin idan al'adar mace ya ɗauke sai ta yi wanka bayan fitowar alfijir, sai ta yi sallah ta yi azumi, shin za ta rama azumin wannan ranan?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Idan al'ada ya ɗaukewa mace kafin fitowar alfijir koda da minti ɗaya ne kuma hakan a ramadan ne to ya wajaba akanta ta yi azumin wannan ranan, domin ta yi azumi tana cikin tsarki, koda kuwa batayi wanka ba sai bayan fitowar alfijir, kamar namiji ne da ya tashi da janaba ajikinsa sawa'un na saduwa ne ko kuma na mafarki, baiyi wanka ba har sai bayan fitowar alfijir azuminsa yana nan babu abinda ya sameshi.

  Aƙarƙashin wannan zanso in faɗakar da mata a kan wani abu, idan al'ada ta zowa mace bayan faɗuwar rana kafin ta yi sallan magriba, azuminta na nan bai ɓaci ba, koda kuwa ya zo matane bayan faɗuwar rana da minti ɗaya, azuminta ya cika"

 

📝 المصدر :

[ ٦٠ سؤالا في أحكام الحيض والنفاس/لفضيلة الشيخ محمد بن صالح العثيمين رحمه الله ص٨].

 

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8ƙu9GT

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

************************************** 

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments