Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Yin Aswaki Ga Mai Azumi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Shin Mai Azumi Zai Iya Yin Asuwaki, Idan Har Zai Iya Yi Da Danyen Ice Ko Busasshe Zai Yi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Na'am, zai iya yi kuma da kowane ice zai iya yi, domin hadisi ya tabbta a Bukhari cewa "Ana ambaton Manzon Allah (S.A.W) yana Asuwaki alhali yana azumi.  Wannan ya sanya Bukhari ya yi babi a kan mai asuwaki da danye ko busasshen itace.     

Kuma ibn sirina ya ce, babu laifi ga mai azumi yayi asuwaki da danye ko busasshe sai akace dashi ai danye yana da ɗanɗano,  sai ya ce shin ruwa baya da ɗanɗano,  kuke kuskure baki dashi.

(1) Duba sharhin Bukhari ibn Biddal

        (Al Malikiy), Juz'I na 4 shafi na 56.

 

Wannan kuma shi ne mafi rinjayen Magana.  Domin Manzon Allah (S.A.W) da ya ambaci asuwaki bai bambance ko danye ko busasshe ba, mai azumi, ko mara azumi ba.(1).  Don haka mutun zai iya yin brush idan yana azumi, domin yadda danyen asuwaki yake da ɗanɗano haka brush yake dashi.  Kuma hadisi ya tabbatar da yin asuwakin.  To kuma me zai sa a hana?

_

(1)  Duba Bukhari (babi na 25, Kitabus siyam)

:

Allah ta'ala yasa mudace

:

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa  a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8ƙu9GT

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

************************************** 

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments