Ticker

6/recent/ticker-posts

Mijina Ya Takura Min Mun Sadu A Ramadan

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Malam yau ina cikin damuwa, saboda na kwanta baccin rana, kawai sai naji mijina ya danne ni, na yi ta ƙoƙarin na kwace amma sai yaci ƙarfina ya sadu da ni, alhalin muna Azumi, don Allah Malam a taimaka min da mafita. Allah ya sanyawa zuriyarka albarka.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Ƴar uwa, mutukar yadda kika siffanta haka abin ya faru, to babu kaffara a kanki, saboda takura miki aka yi, kuma ba ki da laifi a wajan Allah, amma shi kuwa ya saɓawa Allah, kuma ya keta alfarmar Ramadan, kuma dole yayi kaffara, ta hanyar ƴanta kuyanga, in bai samu ba sai yayi Azumi sittin a jere, in bai samu dama ba sai ya ciyar da Miskinai sittin, kamar yadda ya zo a Hadisin Bukhari mai lamba ta: (616).

 

Allah ne mafi sani.

 

 Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8ƙu9GT

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsosh

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

************************************** 

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments