Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Azumi Ya Wajaba A Kan Ɗan Shekara Goma Sha-Biyar (15)?

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum, malam barka, malam dan Allah ina son in san actual shekarun da namiji azumi ya wajaba a gare shi, muna da yaro yana cikin shekara ta 15 Amma muryar shi ta yi nauyi kuma gashin hamata ya fito masa amma abun da ba mu sani ba ko ya yi mafarki, to shi ne bai son yin azumi ni kuma ina ganin kamar azumi ya wajaba a gare shi amma babansa yana yi masa daukar karamin yaro.

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Wa'alaikumus Salam, Duk yaron da waɗannan abubuwa guda uku suka tabbata a tare da shi, to babu shakka ya kai haddin balaga:

1. Tsurowar gashin mara, ko na Hammata.

2. Kai wa shekara goma sha biyar (15).

3. Yin mafarki.

Matuƙar ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa uku ya sami yaro namiji, to ya balaga, kuma azumi da sauran ibadoji kamar sallah da sauransu, sun hau kansa. Idan kuma mace ce sai a ƙara mata da:

4. Al'ada ko Haila.

Dazarar ɗaya daga cikin huɗun nan ya tabbata ga ya mace, to ita ma azumi da sauran ibadoji sun wajaba a kanta. Saboda haka, kuskure ne a bar yaron da ya kai shekara goma sha biyar (15), ko ya taɓa yin mafarkin saduwa, ko gashin mara da hamata suka fito masa ya ƙi yin azumi.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GEahmrOpR4pA5TmW0ZW0cU

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

************************************** 

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments