Ticker

6/recent/ticker-posts

Yaushe Ake Azumin Ramadan

 Yin Azumin Ramadan yana wajaba da ɗayan abubuwa guda biyu:

1• Ganin watan Ramadan

 ALLAH TA'ALAH ya ce:

Duk wanda ya tabbatar da tsayuwar watan to ya azumce shi.

 Al-Baƙara ayata:185.

Idan mutum ya ga watan Ramadan shi kaɗai, kuma shi mutumin adali ne, wanda aka aminta da adalcinsa, to za'ayi aiki da maganarsa ta ganin wata a wajen mafi yawancin ma’abota ilimi.

Abdullahi ibn Umar (R.A) ya ce:

Mutane sun ga wata, kuma ni ma na gan shi, don haka, sai na je na bawa Manzon ALLAH {s.a.w} labari, sai Annabi {s.a.w} ya yi Azumi, kuma ya umarci mutane su ma su azumta.

 [Abu Dawud ne ya rawaito].

2• Cikar Watan Sha’aban Kwana Talatin.

Idan sama ta yi duhu gajimare ya rufeta a ranar ashirin da tara, ba a ga wata ba, har aka wayi gari ranar talatin ga wata, to wajibi ne a ranar talatin kowa ya ɗauki Azumi.

 Abdullahi Ɗan Umar (R.A) ya ce:

 Manzon ALLAH {s.a.w} ya ce:

Wata dare ashirin da tara ne, don haka kar ku yi Azumi har sai kun ga wata, idan kuwa sama ta yi girgije, to saiku lissafa kwana talatin.

 [Bukhari ne ya rawaito]. 

************************************** 

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments