Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin ya hallata mace ta fito tsakar gida babu hijabi?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum munayima mlm fatan alkhairi mlm tambayata ita ce ya halatta mace tafito tsakar gida babu hijabi ajikinta kuma gidan na hayane akwai maza sosai ko Kuma abokan mijinta su zo ta fito ba hijabi.

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Ya Kamata Mata Su Sani Cewar. A Cikin Addinin Musulunci, Akwai Abin da Ake Cewa Al'aura. Wanda wannan Au'aura ɗin, Haramun ne Mutum ya Bayyana ta ga Wasu Waɗanda ba Mazajensu Ba. Allah da kansa yana Kishi a kan Mace Ko Namiji Ya Bayyana Al'aurarsa ko Al'aurarta.

Ma'ana dai. Namiji Al'aurarsa ta fara daga Cinyoyin sa zuwa Cibiyarsa. Haka Malamai Suka Ce. Ma'ana baya Halatta Wani wanda ba Matarsa ba. Ya ga Abin da yake daga Cibiyarsa Zuwa Cinyoyin sa. In ban da Matarsa ta Aure.

Al'aurar Mace Kuma ko'inanta Al'aura Ne, in ban da Fuskarta da Hannayenta. Sabida haka ke nan. Bai Halatta mace ta Bayyana Wani Sashe Na Jikinta ba ga Wani wanda ba Mijinta ba. Harma Ya ga Ko da Wuyanta ko Kwabrinta ko Dantsen hannayenta in ban da Mijinta. Sai 'yan'wanta na jini. Wanda suke Uwa ɗaya ko Uba ɗaya ko Uwa ɗaya Uba ɗaya ko kanenta ko yayanta ko Iyayenta ko kwannen Iyayenta ko Ka kanta Ko Mijin Mahaifiyarta. Waɗannan su ne bai Halatta ku Aureta ba har Abada. Ko soyayya ga ɗaya daga Cikin waɗannan Mutanen da na Zayyano su Haramun Ne.

Sannan Su ɗin Ma bai Halatta Suga Abin da yake Daga Cinyoyinta ko Kirjinta ko wani sashe na Jikinta ba. In ban da Mijinta ba. Sai idan ko Larurar hakan ta kama. Kamar idan Likita ne da zai yi Mata Tiyata ko wani Abu daban.

 

Miji yana da ikon da zai Iya ganin ko Ina Na Jikin Matarsa, har Farjin ta ya Halatta ya gani, sai dai ba zai Kwarai Masa Ido Ba Kamar yadda Turawa Suke yi. Musulunci bai Koya Mana Haka ba. Sabida Nana Aisha Tace, Tana Yin Wanka tare da Manzon Allah a Maka yi Guda ɗaya.

 

Kuma in ban da ma zaman Larura. Ta yaya Mutum zai Zauna a gida tare da wani Mutum. shi ma da ta sa matar a gida ɗaya? Larura ce ta ke sa hakan. Ina Nufin Zaman haya.

 

Sabida haka ke nan. Baya Halatta mace ta zauna a tsakar gidan haya. Tana mai Nuna Tsiraicinta. shi ma Kuma Namiji bai kamata ya fito tsakar gidan haya wanda ba shi kaɗai ne a gidan ba. Alhalin kuma yana mai Nuna tsiraicinsa. Kai ko ba Tsiraicinsa ba. Sabida Gujewa Fitina.

 

Idan mace tana Fitar da Tsiraicinta a gidan haya. Abu na farko da zai Faru shi ne, ZINA a Tsakanin Matar wane da mijin wance. Wata Matar za ta iya Sha'awar Mijin wata. Haka shi ma Mijin wata, zai iya Sha'awar matar wani. Kuma ta dalilin Fitar da Tsiraici. Domin Shaiɗan yana Cewa. MASHIN DA IDAN YA HARBA BAYA KUSKUREWA, SAI YA KAFA MUTUM shi ne MACE. Ba Kowanne Namiji ba ne za a jarrabeshi da Mace ba ya Tsallake. Sai wanda Allah ya Tsallakar da Shi. kin ga ke nan, idan har mace za ta Fitar da Al'aurar ta ga wani Namiji, Sha'awa za ta taso. Idan Sha'awa ta Taso sai dai kuma Addu'a.

 

A irin wannan Zamanin da Ake wayar Gari. Mijin wata ya yi Bulaguro na Wasu Kwanaki, ya bar Matarsa a Gidan da yake da Matar wani. Haka matar wani ma za ta Iya yin Bulaguro na wani Kwanaki, Alhalin Mijinta Kuma Yana Wannan Gidan. ke nan Wancan Mijinta baya nan, ya yi Tafiya, wannan mata matarsa ba ta nan. Kuma matar wane tana fidda Tsiraicin ta a Wannan Gidan. Ta yadda za ta Iya Tayar da Sha'awar Wancan da Matarsa ta yi Bulaguro. Lalle Kam sai dai Addu'a.

 

Haka zalika idan an sami sharing na ban ɗaki Na Bayan Gida. Ma'ana idan banɗaki ɗaya ne a wannan gidan na haya. Tabbas wani Namijin idan har Fitinanne ne, da gangan zai shiga Wannan banɗakin. musamman ma idan ya tabbatar da wance tana Ciki.

Sannan yana Iya Faruwa idan wanda kuke tare da shi baya Shigowa gida da wuri. kin ga ke nan wannan gidan Bashi da Security. Sabida ba za ku Rufe Masa Gida ba. Sa bisa Ba Naku ba ne. Kuma yadda Kuke Biya shi ma Haka yake Biya. Sannan zaman gidan haya. Ko Mene ne ya haɗa Mutum da matarsa na ba Daidai ba. Sai kowa ya ji. Ma'ana Asirinsa baya Rufuwa.

 

Haka Zalika a irin wannan gidan za ka samu Ana Gulmace-gulmace. a nan ne za ka ji ance wance Maiya Ce, Wance Barauniya ce, Wance Mazinaciya Ce, Wance ta Rena Mijinta, Wance ta fiya son Miji, wance ta cika Jaraba, wance Masifaffiya Ce, wance Kaza, Wance Kaza.

 

Daga ƙarshe Dai. Maganar gaskiya Idan har Allah ya Kaddara Mijinki Bashi da Ikon Mallakar Gidan da za ku Zauna. Wanda haka ne ma ya sa yake Zaune a gidan Haya. Wanda Hakan ne Ma ya sa kuke Zaune da Wasu matan da Mazajensu kuma Kike Fitar da Tsiraicinki. Wannan ba Daidai ba ne. Ba Karamin Kuskure ba ne. Kuma wajibi ne Kowanne Namiji ya Tabbatar da Cewar matarsa tana Kiyayewa Daidai gwargwado.

 

Muna Rokon Allah ya Wadata duk wanda Bashi da gidan kansa. Allah ka wadata shi ya Mallaki Gida Nasa Na Kansa.👏

 

Manzon Allah Ya ce, ARZIKIN DUNIYA ABU UKKU NE. GIDA YALWATACCE. MACE TA GARI. ABIN HAWA LAFIYAYYE.

 

Gida Yalwatacce shi ne, wanda yake da dakin Maigida daban, Dakin Matansa da ban, Dakin yara daban, dakunan Baki daban. Sannan Akwai wajen Hutawa daban, da Tsakar gida Yalwatacciya.

 

Ta bangaren Abokan Miji Kuma. In ban da Ma Wani Rashin Tsari Na Mutum. Ta yaya za ka ke kai Abokanan ka Gidanka. Wajen matarka. Wadda Wannan Matar Taka Ita ce Suturar ka. Harma matarka ta fito babu hijabi a Jikinta? Gaskiya Wannan Ba Daidai ba ne ga Rayuwar Kowanne Musulmi. Kuma hakan yana Sabbaba Fitina Tsakanin Matar Aure da Abokanan Mijinta. Ko wani daga Abokanan Mijinta. Maganar Gaskiya, Ba kai ba Zuwa gidan Abokin ka in baya nan. Babu ke babu Sauraron Abokin Mijinki idan Mijinki baya nan. Sannan Kuma Abin Haushi ma sai ka ga Wai matar Musulmi tana da Number waya na Abokin Mijinta. Me ya yi Zafi Haka. Wai tana Kiransa Lokaci bayan Lokaci. Wani Lokacin ma a gaban Mijinta za ta kira Abokinsa. Shi kuma yana Ji yana Gani. Wai suna Gaisawa. Harma tana Tambayar sa Abin da ya sa na Kira ka na ga kwana biyu ka Guje mu ko ka manta da mu. Shi ya sa na kira ki!!!!. Allah ya Sawwake Mana. Maganar Gaskiya Wannan Ba Musulunci ba ne. Babu wata Alaka Tsakanin Ki da Abokanan Mijinki. Babu lefi za ki iya yin Zumunci da Matar Abokin Mijinki. Amma ba da Abokin Miji ba. Zumunci da Abokin Miji. Wannan Fitina Ne.

 

Manzon Allah Ya ce ban bar wata Fitina a baya na ba, da take Cutar da Maza in ban da Mata. Sabida Haka Mu ma Maza Sai Mun zama masu Kishin Matan mu. Manzon Allah Ya ce, WANDA BAYA KISHIN MATARSA, BA ZAI SHIGA ALJANNAH BA. Ko Waye kai idan ba ka kishin Matarka. Ba za ka shiga Aljannah ba. Manzon Allah Ya ce NA GA WATA A TSAKIYAR WANI GIDA DA YAKE CIKIN ALJANNAH. SAI na ce WANNAN GIDAN NA WANENE. SAI AKA CE NA UMAR NE. DA HAR ZAN LEKA WANNAN GIDAN DA aka ce NA UMAR NE, DA NA TUNA KISHIN UMAR, SAI NA FASA LEKAWA. Sannan Manzon Allah Ya ce ALLAH YANA KISHI, KISHIN UBANGIJI shi ne YA GA BAWA YA JEWA ABIN DA YA HARAMTA MASA. Sannan Wani Lokaci Sa'ad dan Abi Waƙƙas Allah ya kara masa yarda Ya ce. Idan na ga Mutum a gida na tare da mata ta. Zan sa takobi Ne in kashe shi ya Manzon Allah Sai Sahabbai Suka yi Mamaki dan irin wannan Kishin Na Sa'ad. Sai manzon Allah Ya ce, KUNA MAMAKI NE a kan KISHIN SA'AD? WALLAHI NI NA FI SA'AD KISHI, NIMA KUMA ALLAH YA FI NI KISHI. Sabida haka kishi na namiji ga matarsa. Wannan Wajibi ne yan Uwa.

 

Allah shi ne Masani.

 

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Eub2uLrV18T4vHJcƙRDkPZ

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments