Zina Da Ƙanin Miji

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Aslm Mallam na samu matsala ne a rayuwata ina zaune da mijina shekaranmu 7 da aure akwai kaninsa da yake bibiyata malam tun bana kulashi har ya kai yanzu muna wasa dashi. na yi na yi ya bari yaki bari. mai ya kamata inyi? Har ya saba inya shigo ya danneni har sai ya biya buƙatansa akaina kuma bana iya ce masa komai. Malam a taimaka mun da addu’oi da shawarwari.

    𝐀𝐌𝐒𝐀👇

    Wa alaikis salam. Hakika kin aikata kuskure babba. Domin kuwa bayan shirka babu wani zunubi mafi girma awajen Allah kamar zina. 

    Manzon Allah ya ce: “MAZINATA ANA HURA MUSU WUTA NE BISA FUSKOKINSU (RANAR ALKIYAMAH ke nan). 

    (Imam Tabaraniy ne ya ruwaito). Sannan a cikin hadisai da dama Manzon Allah ya bayyana cewar Akwai wani ruwa mai bala’in doyi wanda ke fita ta farjojin Mazinata a cikin Wuta. Wannan ruwan da shi ake yi wa sauran ‘yan Wuta Azaba. Sannan a cikin wani Sahihin hadisi wanda Imamul Mundhiriy ya ruwaito a cikin Targheeb wat-Tarheeb, Manzon Allah ya ce: “ALLAH YANA KUSANTOWA GA BAYIN SA, SAI ya yi GAFARA GA DUK MAI NEMAN GAFARA. AMMA BAN DA MATAR da ke ZINA DA FARJINTA…. “.

     

    Ya zama wajibi ki ji tsoron Allah ki dena domin kuwa wannan laifin zai iya janyo miki bala’i da tozarta da wula kanta da ke da danginki da iyayenki tun daga nan duniya. Aranar lahira kuma Farjin naki da kike zinar dashi, da kuma sauran gabobin jikinki su ne za su tona asirinki a gaban Zatin Allah, ga dukkan halittu suna kallonki. 

     

    Zata yiwu ki samu ciki ta dalilin wannan Zinar, kuma ki shigo ma mijinki da wannan cikin (Ma’ana ba zai gane cewa cikin ba nasa ba ne). Alhali Manzon Allah (saww) ya ce: “DUK MATAR DA TA SHIGO MA WASU MUTANE DA WANI WANDA BA CIKINSU YAKE BA, TO ITA BA KOMAI BACE AWAJEN ALLAH. KUMA (ALLAH) BA ZAI SHIGAR DA ITA ALJANNARSA BA… “ (Nisa’iy hadisi na 3481, Abu Dawud Hadisi na 2263).

     

    Shi kuwa wannan Ƙanin Mijin naki ya ci amanar Allah da Manzonsa Kuma ya ci amanar Ɗan'uwansa (wato mijinki). Kuma yana daga cikin mutanen da Allah yake yin tsinuwa agaresu. Manzon Allah ya gaya ma Sahabbansa cewa “WALLAHI MUTUM ya yi ZINA DA MATAYE GUDA GOMA, SHI ya fi SAUKI AGARESHI (WATO SAUKIN AZABA AKANSA) FIYE DA ya yi ZINA DA MATAR MAKOBCINSA”. (Imamu Ahmad da Tabaraniy ne suka ruwaitoshi). a cikin riwayar Ibnu Abid dunya kuma daga Sayyiduna Abdullahi ‘dan Umar (ra): “WANDA ya yi ZINA DA HALAL ƊIN MAKOBCINSA (WATO MATAR MAKOBCIN KO KUYANGARSA) ALLAH BA ZAI DUBESHI NA ARANAR ALƘIYAMAH (WATO BA ZAI MASA KALLON RAHAMA BA) KUMA BA ZAI TSARKAKESHI BA. KUMA ZAI CE MASA SHIGA WUTA TARE DA MASU SHIGARTA).

     

    To in dai haka lamarin yake a kan matar Makobci, to yaya kuma matar Ɗan'uwa? Saboda guje ma faruwar irin wannan Fasadin shi ya sa Manzon Allah ya ce: “KADA WANI MUTUM YA KEƁANCE TARE DA WATA MACE, FACHE SAI TARE DA MUHARRAMINTA. Sai wani ya ce Ya Rasulallahi shin Makusancin Miji fa?” Sai Manzo Ya ce “MAKUSANCI AI shi ne MUTUWA” (Wato shi ne ya fi ɓarna ke nan). 

    ABIN DA ZA KI YI shi ne:

    👉Da farko ki tuba zuwa ga Allah ki janye jiki daga wannan kwarton fasikin da ke zuwa miki. 

    👉Ki hanashi shigowa amma idan bai hanu ba, Ki sanar ma mijinki cewa lallai ya hana wannan Ƙanin nasa shigowa inda kike. 

    👉Ki rika tuna lahirarki da kuma tsayuwarki a gaban zatin Allah. Da kuma kusancin Allah gareki ako yaushe. 

    👉Ki sani cewa Biyan buƙatar Sha’awar Minti biyar za ta iya janyo miki Wula kantar duniya da lahira. 

    👉Ki tuna rayuwar yaranki da kuma tarbiyyarsu. Kuma ki dubi amanar Mijinki da kike ci. 

    👉Ki Yawaita Istighfari da Azumin nafilah domin samun tsarkaka daga wannan alfashar. 

    👉Idan Mijinki ba mazauni ba ne, gara ki matsa ki bishi wajen da yake aiki ku zauna achan domin samun tsira da Imaninki da mutuncinki. 

    👉Ki rika yin wannan addu’ar domin nisanta kanki daga alfasha “ALLAHUMMA JANNIBNEE MUNKARATIL AKHLAƘI WAL AF’ALI WAL AHWA’I”

    Allah ya sawwake ya gafarta miki ya shirye ki ya tsamoki daga kowanne laifi, tare damu bakiɗaya. 

    WALLAHU A’ALAM. 

    Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/F1YV6JhrD89EfJddPLvƘ32

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.