Ticker

6/recent/ticker-posts

Na Tsinci Naira ₦500 Ko Zan Iya Amfani Da Ita Ba Tare Da Na Yi Cigiya Ba?

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum malam wani bawan Allah ne ya tsinci Naira 500, kuma baiga wadanda zai yi wa cikiya ba... Yaya kamata ya yi da wannan kudin tsintuwar? Suna ajiye yanzu haka kusan wata daya ke nan.

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN ƘAI.

To ɗan uwa idan mutum ya yi tsintuwa ya wajaba a gareshi ya yi cigiya har tsawon shekara guda, idan bai samu mai ita ba, daga nan zai iya amfani da ita, amma idan mai ita ya zo daga baya zai biya shi. Kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisinsa mai lamba ta: 5761.

Amma idan abin daya tsinta ɗan kaɗan ne bashida yawa, to ya halatta ya yi amfani da shi ko da baiyi cigiya ba. Saboda abin da aka rawaito cewa: Annabi yaga wani dabino a kan hanya, sai ya ce: In banda ına tsoron kona sadaka ne da naci. Muslim ya rawaito a hadith mai lamba ta:2527. Sai hadişin ya nuna dan karamin abu baya bukatar cigiya.

 

Malamai şun yi saɓani wajan iyakance tsintuwar da ba ta bukatar cigiya. Wasu sun ce za a koma al'adar mutane, duk abin da mutane şuke ganinsa ba a bakin komai ba, to idan an tsince shi baya bukatar cigiya, Ibnu Khudama ya hakaito daga Imamu Malik cewa: Bai wajaba mutum ya yi cigiyar abin da bai Kai a yanke hannu saboda shiba, wato daya bisa hudun

dinare. Haka nan sayyadina Aliyu (R.A) ya tsinci dinare daya ya yi amfani da ita batare da ya yi cigiya ba. Abin daya gaba ta yana nuna cewa: mutukar baka sami mai Naira (500) ɗin da ka tsinta ba a kusa da Kai, ya halatta ka yi amfani da ita batare da cigiya ba, tun da ba kuɗi ne mai yawa ba, kuma mai ita ba zai kwallafa rai Akantaba.

 

Domin neman karin bayani aduba: Al-mugni 6/351.

 

Allah shi ne mafi Sani.

 

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/L8l4xHCd7wUG5xZEmvBbzB

 

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

Post a Comment

0 Comments