Hukuncin Tsintuwa

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi. 

    Question and Answers in Islam

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Idan mutum ya samu kuɗi a hanya a ƙasa shin ya Halatta ya ɗauka?

    𝐀𝐌𝐒𝐀👇

    Tsintuwa ya rabu kashi uku.

    Na farko: Tsintuwan abin da bashi da ƙima mai yawa, kamar tsintuwar Sanda, ko wani abin sha kaman lemu misali, ko Biredi misali. Ko irin tsintuwar naira ashirin. Dai duk abin da a al’adance an san mai ita ba zai damu da ita ba idan ta ɓace. To idan mutum ya tsinci irin wannan abu to zai yi amfani da shi babu laifi. Saboda Hadisin da Abu dawud ya rawaito

    Annabi ya yi rangwame game da tsintuwar sanda, ko igiya ko makamancin su. Wanda ya samu ya yi amfani dasu

    Abu Dawud: 1717. (Sheikh Nasirud-din Albani ya raunata Hadisin.).

    Na biyu: abin da idan aka barshi ba zai salwanta ba har mai shi ya zo ya same shi. Kaman raƙumi, ko kujera, da makamantansu. Shi wannan baya halatta a ɗauka. Domin an tambayi Annabi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi game da tsintuwar Raƙumi sai ya ce: Ina ruwanka da ita? Tana tare da ruwan shanta da abin da zai tsare mata ƙafafun ta, tana zuwa wurin ruwa tasha, sannan tana cin bishiya har ta kai ga mai ita

    Sahihul Bukhari: 2372

     

    Wannan Hadisi yana nuna cewa ba a tsintuwar raƙumi ko wata dabba da za ta iya komawa zuwa ga mai ita.

     

    Ya shiga ƙarƙashin wannan hadisi duk wani abu da idan aka barshi mai shi zai iya zuwa ya ɗauki kayansa ba tare da wani matsala ba kamar yadda mukayi bayani a baya.

     

    Na Uku: dukiya da za ta iya salwanta idan aka barta, kaman Rago ko akuya da makamantansu. Ko kuma sauran dukiyoyi kaman kuɗi na takarda, ko zinari ko azurfa.

    Idan abin da aka tsinta dabba ne kaman rago ko akuya to wanda ya same ta zai yi ɗayan abubuwa uku:

    1. Ko ya yanka yaci naman. Amma idan mai ita ya dawo zai biya shi kuɗin dabbar

    2. Ko ya siyar da dabbar ya ajiye kuɗin duk randa aka samu mai ita sai ya bashi.

    3. Ko ya ajiye ya cigaba da kiwon dabbar har randa Allah zai kawo mai shi. Idan ya ɗauki lokaci mai yawa yaga ba zai iya cigaba da ajiya ba to sai ya yi amfani da ɗayan hanyoyi biyun farko.

    Idan kuma dukiyar da ya samu kuɗi ne to zai ajiye. Yasan yawan kuɗin da yanayin kuɗin sannan ya yi shela wa mutane. Zai yi ta sanar wa har na shekara guda. Idan aka yi shekara guda ba a samu mai shi ba to sai ya yi amfani da shi ko ya bada sadaƙar sa. Amma idan mai dukiyar ya dawo yana nemanta to zai biya shi.

     

    An rawaito daga Annabi an tambaye shi game da tsintuwa sai ya umarci wanda ya yi tsintuwa da ya san siffar abin da ya tsinta idan kuɗine misali to yasan yawan kuɗin sannan yasan yanayin kuɗin ta yadda idan mai shi ya zo ya yi bayani da ya gamsu cewa nashi ne sai ya bashi. Sannan sai ya nemi mai ita har tsawon shekara guda. Idan bai samu mai ita ba to sai ya yi amfani da dukiyar ko ya bada sadaƙa. Wannan Hadisi Bukhari ya rawaito shi a hadisi na 2372.

     

    Ya kamata mu lura da abubuwa kaman haka:

    1. Kafin mutum ya ɗauki tsintuwa dole sai ya aminta da kansa cewa zai nemi mai dukiyar, sannan kuma zai kiyaye dukiyar har a samu mai ita. Idan yasan ba zai iya haka ba to haramun ne ya ɗauki wannan tsintuwa.

     

    2. Dole yasan adadin kuɗin ko nau’in Dukiyar kamar yadda hadisin da muka kawo a sama ya yi bayani.

     

    3. Dole idan ya ɗauki dukiyar ya yi shela ya nemi mai ita. zai yi shelan ne kuma da yanayi da ya dace da zamanin sa. Misali ko ta gidan rediyo ko ta waya da makamantansu.

     

    4. Idan mai dukiyar ya zo kuma ya siffanta dukiyar daidai to dole a miƙa masa dukiyar sa.

    Idan ba a samu mai dukiyar ba to wanda ya samu ta zama tashi. Ko ya yi sadaƙa da ita ladan ya kai ga mai dukiyar ko kuma ya yi amfani da ita. Amma idan mai dukiyar ya dawo zai mayar masa da dukiyar sa.

    Wannan shi ne taƙaitaccen hukuncin Tsintuwa.

     

    Allah ya sa mu dace.

     

    Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/L8l4xHCd7wUG5xZEmvBbzB

     

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.