Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
GAME DA ADDU'A BAYAN SALLAME SALLAH
Idan muka duba da nassin hadisi da bayanai da suka zo
a cikin litattafn fiqhu, babu inda aka samu cewa Manzon ALLAH {s.a.w} yana yin
addu'a a bayan sallar farillah wacce har zai ɗaga hannu sama ko kuma yana
karanta wata addu'a shabbai su ma karantawa bayan ya faɗa babu wannan kwata-kwata,
sai dai iya azhkar daya koyar, shi kuma wannan kowane mutum zai yi nasane shi
kaɗai.
Amma hakan ya samo asaline daga gurin malaman gargajiya wanda yin haka bidi'ah ne ba koyarwar Manzon ALLAH {s.a.w} bace.
Manzon ALLAH
{s.a.w} ya kasance yana shigar da duk wata addu'arsa ne cikin sujjadarsa ta
farillah a ya yin sallar farillah ko a ƙarshen tahiya bayan kammala
salati da addu'o'i na sunnah sai kuma mutum ya roƙi duk wata buƙata tasa da yakeso ya roƙa.
Amma da zarar
anyi sallama ba a shigo da wata buƙata sai iya abinda aka samu
a nassi Annabi {s.a.w} yanayi kuma ya sunnantawa sahabbansa (R.A) yin hakan.
An sunnanta a
kowacce sallar farillah idan mai sallah zai shigo da buƙatarsa to ya roƙa a cikin sujjadarsa ta
sallah, a sujjadar farko ko a ta ƙarshe ko kuma a cikin ko
wacce sujjadah a cikin sallar farillah sai ya faɗawa ALLAH buƙatarsa.
Manzon ALLAH
{s.a.w} ya ce:
Babu gurin da bawa ya fi kusanci da UBANGIJINsa kamar
a cikin sujjada don haka ku yawaita addu'a a cikinta.
Sannan kuma ana
roƙon ALLAH a ƙarshen tahiyar sallah kafin
ayi sallama, ananma za ka iya shigo da duk wata buƙatarka, kuma ita addu'a ana iyayinta a cikin ko wanne nau'in
yare.
Amma bayan anyi
sallama ba a ɗaga hannu a roƙi ALLAH babu hadisi a kan wannan,
hasalima ita addu'arq da aka yita a cikin sallah tafi domin za a ɗauki sallarka tare da
addu'arka akaita ga UBANGIJINka a tare ba a rarrabe su.
Kawai dai
anayin azhkar da aka sunnata a bayan sallar farillah ne wanda Annabi {s.a.w} ya
karantar kuma sunanan damƙam a cikin hadisai
ingantattu.
Musammam idan
mutum yanaso ya sami cikakken bayani ya nemi littafi mai suna Siffatus-salatun
Nabiyyi {s.a.w} musamman na Muhammad Nasiruddin Albani (R.h) zai sami
ingantattun hadisai tareda maganganun malaman fiqhu a cikinsa.
Amma a sallar
Nafila ana iyayin addu'a a cikin sujjadah haka kuma ana iyayin addu'a a ƙarshen tahiya kafin sallama, ana kuma iya ɗaga hannu sama a roƙi ALLAH duk wata buƙata bayan an sallame sallar
nafila.
Idan mai sallah
ya yi sallar Nafila yana iya ɗaga hannunsa sama ya roƙi ALLAH dukkan damuwarsa bayan ya gama saiya sauke hannunsa
ba a shafawa a fuska ko a wani guri, babu hadisi ingantacce da ya zo da cewa
Annabi {s.a.w} yana shafe fuskarsa bayan ya gama addu'a.
Wannan bayanai muna kawo su ne domin dukkan al'ummar musulmi susan sallar Manzon ALLAH {s.a.w} da kuma yadda za su bi wajen kiyaye koyi da shi a cikin sallarsu, domin ALLAH baya karɓan ibadar da ba a koyo ta daga Manzon ALLAH {s.a.w} ba.
ALLAH shi ne mafi sani.
Duk mai neman ƙarin bayani ya tuntuɓe mu ta private.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.