Girman Larurar Da Za A Iya Ajiye Azumi Dominta

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum. malam ina da tambaya nice ina shayarwa yarinyar kwana 50 take yanzu amma tsakani da Allah yarinyar bata rasa nonon sha, shin zan iya ajiye azumi saboda ana rana kuma akwai wani ciwo da na yi Wanda yake bukatar arunka shan ruwa sosai gudun kar ya tashi?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

    Kafin ki ajiye azumi dole sai kin tuntubi kwararrun likitoci musulmai, kuma sun tabbatar miki da cewar idan har baki sha ruwa bayan adadin lokuta kaza da kaza ba, tabbas wannan ciwon zai iya motsawa.

    Idan sun tabbatar miki da haka, to shikenan sai ki ajiye azumin. Idan kin samu lafiya kuma ki rama adadin abinda kika sha. Idan kuma sun tabbatar miki cewar ciwon ba irin wanda ake tsammanin warkewarsa bane, To sai ki rika ciyar da miskinai bisa adadin azumin da kika sha.

     

    Amma idan likitocin sun tabbatar miki da cewar zaki iya yin azuminki ba tare da barazanar motsawar wannan jinyar ba, to shikenan sai kiyi azuminki. Tunda Allah Ya faɗa acikin Alƙur'ani cewa : "KUYI AZUMIN SHI YAFI ALKHAIRI GAREKU IDAN HAR KUN SANI".

    Amma kasancewar ana yin zafin rana, wannan kaɗai bazai zama hujjar ajiye azumi ba.

    WALLAHU A'ALAM.

    Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa a Sunnah.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8ƙu9GT

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

     ************************************** 

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.