Ticker

6/recent/ticker-posts

Mene Ne Khul'i A Musulunci?

Ma'anar Khul'i shi ne mace ta fanshi kanta daga gurin mijinta, ta ba shi sadakinsa da ya biya a lokacin da ya aure ta.

 Kamar yadda hakan ya zo a hadisi wanda hakan ya taɓa faruwa a tsakanin ɗaya daga cikin Sahababan Manzon ALLAH {s.a.w} da matarsa.

 Ya halatta a musulunci mace ta biya mijinta sadakinsa daya ba ta a lokacin daya aureta idan har bazata iya zama da shi ba, ko ba ta sonshi, ko yana mata wasu abubuwa da bataso anyi sulhun anyi sulhu amma bai daina ba, to ya halatta ta yi masa Khul'i kamar yadda ya zo a cikin Suratul Bakarah ayata 229.

 Sannan khul'i yana daukar hukuncin saki ɗaya ne tak, sannan kuma idan anyishi ba'ayin kome sai dai tsohon mijin nata ya sake biyan sabon sadaki sannan sai a ɗaura musu sabon aure.

ALLAH shi ne mafi sani.

ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.

HUKUNCIN KHUL'I

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Malam tambaya ta ita ce ma'aurata biyu da suka yi khul'i, shin za su iya sake yin aure?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumusalam warahmatallahi wabarakatuh.

Khul'i yana nufin rabuwar aure tsakanin ma'aurata, ta yadda matar zata biya Mijinta wani adadin kuɗi ko wani abu mai daraja da nufin fansar kanta daga Mijinta. Wannan yana nufin rushewar auren su kenan.

Shi Khul'i ba kamar saki na Dalaq bane. Shi dalaq idan akayi shi har ya kai 3 toh bazasu sake yin aure ba har sai matar tayi wani aure da wani Miji daban. Amma shi khul'i zasu iya sake yin aure idan matar ta amince ba tareda tirsasawa ba.

Shi Khul'i Ma'anarsa shine ɓata Aure a Kasheshi yazama yanzu wannan Matar da Mijin babu wani ƙulli tsakaninsu, dan haka baze yiwuba a gyara Auren se in anzo da sabon Sadaki an sake ƙulla Sabon Aure. Amma baze yiwuba kawai yace ya maida ita domin ba Saki bane Asali Faskhune shi.

Mai Neman karin bayani yana iya duba Al-Sharhul Mumti, Mujalladi na 12, shafi na 467-470).

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

BAYAN KHUL'I SAI AN AMBACI SAKI?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Salamu alaikum Inaso aimin Karin bayani game da kul'i. mijine aka nemi saki a gunshi sai yace sai ambashi sadakin da yabiya sai aka bashi, shin dole saiya saketa sannan ta zama ba matarsaba ko kuma karɓar kuɗin da yayi ta wadatar?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikis Salaam: Toh malamai sunyi saɓani gameda wannan. Akwai waɗanda sukace bayan ya amshi kuɗin sekuma ya saketa, amma zance mafi inganci shine baseya saketaba domin shi Khul'i yana babin Faskhu ne ba babin saki yake ba.

Wato shi Khul'i lalata aurene da zarar ya saketa toh shikenan auren nasu ya lalace yazama ɓatacce, kuma koda ace sun shirya abayan yin khul'in toh baza'a maida aurenba seya biya sabon sadaki ansake ɗaura sabon aure, saɓanin saki wanda ze iya cewa ya dawo da ita, dan haka Khul'i baseyace ya saketaba matukar ya amshi sadakinsa toh auren nasu ya lalace. Idan kaduba Taudihul Ahkam na Ali Bassam yayi bayani sosai akai.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

IDDAR MATAR DA AKA YIWA KHUL'I:

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Matar da aka saketa ta hanyar Khul'i yaya iddarta zai kasance???

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Toh khul'i shine ɓata aure ta hanyar  amaidawa miji dukiyar aurenda yabada. Toh wannan matar itama idda zatayi ta hanyar jini uku kamar yadda sauran matanda aka sakesu sukeyi. Itama wannan jini ukun zatayi.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments